Ticker

Na Gama Zama Da Ke Har Abada

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum,_ Allaah ya taimaki malam. Tambayata a nan ita ce: Idan miji ya ce ma matar shi: Ban son ki! Ban ƙaunar ki! Kuma na gama zama da ke har abada!! Shin malam, wannan saki ne? Idan saki ne, to saki nawa wannan kalmar ke nufi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Allaah ya taimake mu gaba-ɗaya.

Da farko: Malamai sun kasa sakin aure ta fuskar lafazinsa gida biyu ne: Akwai Saki Sareeh , akwai kuma Saki na Kinaaya .

Saki Sareeh shi ne wanda mijin ya yi amfani da wata kalma ko kalmomin da ba su iya ɗaukar wata fassara ko ma’ana sai dai sakin kawai. Kamar ya ce: Ya sake ta , ko ya ce: Ke sakakka ce, ko: Sakakkiya ce .

A nan ana zartar masa da abin da lafazinsa ya nuna a fili, ba tare da neman wani bayani game da manufarsa a wurin furta wannan kalmar ba.

Saki na Kinaaya kuwa shi ne wanda a cikinsa mijin ya yi amfani da wata kalma mai harshen-damo, wadda tana iya ɗaukar ma’anar saki, kuma tana iya ɗaukar ma’anar wani abin da ba sakin ba. Kamar ya ce mata: Tafi gidanku!

A nan ba a cewa ya saki matar har sai bayan an tambaye shi, an ji manufarsa. Domin kalmar tana iya ɗaukar ma’anar: Tafi gidanku sai na zo…! Ko: Tafi gidanku a yi miki faɗa…! Ko kuma: Tafi gidanku sai bayan kwana biyu…! Da sauran makamantan haka.

Galibi namijin da ke amfani da irin wannan sakin na Kinaaya ba sakin matarsa yake nufi ba. Yawanci gargaɗi ko razanarwa ko jan-kunnenta kawai yake son yi, don ta aikata wani aiki ko ta nisanci aikata wani aiki. Domin in ba haka ba, me ya hana shi furta kalmar sakin na Sareeh kawai, a wuce wurin?!

Amma duk da haka, idan bayanansa daga baya suka nuna manufarsa game da furucinsa shikenan.

Kamar haka, wanda ya ce wa matarsa: Shi ya gama zama da ita har abada! Wannan ba saki ne sareeh ba, domin bai ambaci kalmar saki a fili ƙarara ba.

Sannan kuma kalmar tana iya ɗaukar fassara ko ma’anar cewa: Ya gama zama da ita har abada a kan tattauna wannan matsalar…!

Ko: Ya gama zama da ita har abada a wannan gidan sai dai a sabon gidansa da ya gina…!

Ko kuma: Ya gama zama da ita har abada sai in iyayenta sun shiga maganar…!!

Da sauran makamantan haka.

Don haka, da irin wannan kalmar ba za a ce ya saki matar ba, sai bayan an zaunar da shi an ji musabbabin abin da ya kai shi ga furta wannan maganar, kuma sai an tambaye shi abin da yake nufi da hakan.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaahi Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/DSdbBS8RZVoIKYG5exOuZE

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments