𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul
Laah. Mutum ne ya auro mace mai fama da wani rashin lafiyar da ba a gaya masa
ba, sai a bayan auren ne ya gano. To dole ne ya nema mata maganin wannan
matsalar?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul
Laah Wa Barakaatuh.
Haƙƙi ne a kan ma’aurata tun kafin a ƙulla aurensu su sanar da junansu duk wani
aibu ko rashin lafiyar da zai iya zama tarnaƙi ko matsala a wurin jin daɗin zamantakewarsu a bayan
aure, bai halatta su ɓoye
shi sai a bayan auren a gano ba. Idan kuma suka yi sakacin haka, to ya halatta
ga wanda aka yi masa wannan rufa-rufar ya warware auren a lokacin da ya gano
hakan.
Sai dai kuma ba kowane irin
rashin lafiya ne ake warware aure saboda shi ba. Malamai sun yi bayanin cewa
hakan na tabbata ne kawai a kan cututtukan da samuwarsu ke hana jin daɗin zaman auren, kamar
rashin ƙarfin
ikon saduwa a wurin namiji, ko toshewar gaba a wurin mace, ko kuma kuturta a
wurin ɗayansu.
A asali miji ya nema wa matarsa
magani a kan duk wani rashin lafiyar da take fama da shi yana daga cikin haƙƙoƙinta
a kansa, kamar yadda Allaah (Subhaanahu Wa Ta’aala) ya ce
وَعَاشِرُوهُنَّ بِٱلۡمَعۡرُوف
Kuma ku rayu da su a cikin
alheri. (Surah An-Nisaa’: 19).
Kuma ba rayuwa a cikin alheri ba
ce miji ya bar matarsa haka nan a cikin zogi da raɗaɗin
ciwo ko rashin lafiya, ya nuna halin ko-a-jikinsa! In kuwa haka ya kasance, to
ina ƙauna
da tausayin juna da Allaah ke sanyawa a tsakaninsu kenan?!
Amma idan ya zama wani abu ne da
aka ɓoye masa, aka
yi masa rufa-rufa ba a sanar da shi tun kafin ƙullin auren ba, to yana da ’yancin ya mayar da ita ga
waliyyanta don su yi mata maganin matsalar sannan ta dawo, kamar dai yadda yake
da ikon warware auren, ya ce ya fasa, muddin dai wannan matsala ce da take hana
jin daɗin zaman
auren a tsakaninsu, kamar yadda ya gabata.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah
Assalafiy
08164363661
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.