𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum. Mutun ne Ylya
saki matarsa a cikin dare, kafin gari ya waye kuma sai ya sadu da ita. To shi
ne ake tambaya: Wai menene hukuncin wannan saduwar?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul
Laah.
Malamai sun saɓa wa juna a kan hakan
Al-Imaam Al-Qurtubiy ya ce
وَإِذَا جَامَعَ أَوْ قَبَّلَ أَوْ بَاشَرَ يُرِيدُ بِذَلِكَ الرَّجْعَةَ، وَتَكَلَّمَ بِالرَّجْعَةِ يُرِيدُ بِهِ الرَّجْعَةَ فَهُوَ مُرَاجِعٌ عِنْدَ مَالِكٍ، وَإِنْ لَمْ يُرِدْ بِذَلِكَ الرَّجْعَةَ فَلَيْسَ بِمُرَاجِعٍ. وَقَالَ أَبُو حَنِيفَةَ وَأَصْحَابُهُ: إِذَا قَبَّلَ أَوْ بَاشَرَ أَوْ لَامَسَ بِشَهْوَةٍ فَهُوَ رَجْعَةٌ. وَقَالُوا: وَالنَّظَرُ إِلَى الْفَرْجِ رَجْعَةٌ. وَقَالَ الشَّافِعِيُّ وَأَبُو ثَوْرٍ: إِذَا تَكَلَّمَ بِالرَّجْعَةِ فَهُوَ رَجْعَةٌ. وَقَدْ قِيلَ: وَطْؤُهُ مُرَاجَعَةٌ عَلَى كُلِّ حَالٍ، نَوَاهَا أَوْ لَمْ يَنْوِهَا. وَرُوِيَ ذَلِكَ عَنْ طَائِفَةٍ مِنْ أَصْحَابِ مَالِكٍ. وَإِلَيْهِ ذهب الليث. وكان ما لك يَقُولُ:
إِذَا وَطِئَ وَلَمْ يَنْوِ الرَّجْعَةَ فَهُوَ وطئ فَاسِدٌ، وَلَا يَعُودُ لِوَطْئِهَا حَتَّى يَسْتَبْرِئَهَا مِنْ مَائِهِ الْفَاسِدِ، وَلَهُ الرَّجْعَةُ فِي بَقِيَّةِ الْعِدَّةِ الْأُولَى، وَلَيْسَ لَهُ رَجْعَةٌ فِي هَذَا الِاسْتِبْرَاءِ.
Idan miji ya yi saduwa ko ya yi
sumba ko ya yi runguma da matar da ya saka yana nufin mayar da ita, ko ya furta
batun komen kuma yana nufin kome da hakan, to komensa ya yi a wurin Al-Imaam
Maalik. Idan kuwa ba nufinsa kome ba ne, to abin da ya yi ba kome ba ne.
Al-Imaam Abu-Haneefah da Sahabbansa kuma cewa suka yi: Idan miji ya yi sumba ko
ya yi runguma ko ya yi shafa da sha’awa to kome wannan ne ya yi. Suka ce: Kallo
ga farjinta ma kome ne! Al-Imaam As-Shaafi’iy da Abu-Thaur kuma suka ce: Idan
ya furta batun kome, to abin da ya yi (na saduwa a bayan saki) ya zama kome ne.
A wata magana kuma sun faɗi
cewa: Saduwarsa gare ta kome ce ta kowane irin hali, ko ya yi niyyar hakan ko
bai yi niyya ba. Hakan aka riwaito daga waɗansu
sahabban Al-Imaam Maalik, kuma hakan ita ce mazhabar Laith. Kuma Al-Imaam
Maalik ya kasance yana cewa: Idan ya sadu da ita ba tare da niyyar kome ba, to
wannan saduwa ce ɓatacciya
ta ɓarna kawai, ba
zai sake komawa ga saduwa da ita ba har sai ta yi istibra’i (ya tabbatar babu
komai a cikin mahaifarta) daga wannan maniyyinsa ɓatacce
da ya zuba mata. Kuma yana da ikon yin kome a cikin sauran kwanankin iddar ta
farko, amma ba a cikin wannan istibra’in ba. (Tafsir Al-Qurtubiy: 18/158).
Wato dai
(i) Waɗansu malamai suna ganin saduwa ko magabatan
saduwar a bayan saki kome ne idan ya ɗaura
niyyar hakan.
(ii) Waɗansu kuma suna ganin hakan kome ne kawai ko
ya yi niyyar hakan ko bai ɗaura
niyyar ba.
(iii) Waɗansu kuma suna ganin saduwar da niyya ba za
ta zama kome ba sai in ya furta hakan da bakinsa.
Akwai irin waɗannan maganganun a cikin
Nailul Awtaar: 7/25, da Majmuu’ul Fataawa: 20/381, da As-Sharhul Mumti’u:
13/189, da sauransu.
Har zuwa yau akwai wannan saɓanin a tsakanin malamai.
Al-Imaam Al-Uthaimeen (Rahimahul Laah) ya ce
الصَّوَابُ أنَّ الرَّجْعَةَ لَا تَحْصِلُ بِمُجَرَّدِ الْوَطْءِ، إلَّا إنْ كَانَ مِنْ نِيَّتِهِ أنَّهُ رَدَّهَا، وَأنَّهُ اسْتَبَاحَهَا عَلَى أنَّهَا زَوْجَةٌ، فَإذَا كَانَ كَذَلِكَ فَهَذِهِ مُرَاجَعَةٌ
Abin da ya ke daidai dai shi ne:
Kome ba ya tabbata da saduwa kaɗai,
sai idan ya kasance a cikin niyyarsa akwai cewa ya mayar da ita, wato ya sadu
da ita a kan cewa ita matarsa ce. Idan aka samu hakan to wannan ɗin kome ne. (As-Sharhul
Mumti’u: 13/190).
Shi kuwa Al-Imaam Al-Albaaniy
(Rahimahul Laah) cewa ya yi
إذَا جَامَعَهَا فَهَذَا يَعْنِي إرْجَاعَهَا
Idan dai har ya sadu da ita, to
wannan yana nufin kome ne ya yi gare ta. (Haka Al-Awaayishah ya Ambato daga
gare shi a cikin Al-Mausuu’atul Fiqhiyyah: 5/318).
Amma ga wanda bai yarda cewa
wannan saduwar kome ba ne, to yaya matsayinta?
(i) Ba za a tsai da masa da
hukuncin zina ba saboda saduwar ta shubuha ce, domin kuma matar da take cikin
idda tana nan a hukuncin matarsa ce har sai lokacin da ya mayar da ita ko kuma
ta ƙare
iddar.
(ii) Kodayake ba za a yanke masa
hukuncin zina ba amma dai alƙali zai yi masa ta’azeer, wato horo na gargaɗi
domin a hana shi maimatawa kuma a hana waninsa yin hakan da wadda ya sake ta.
(iii) Idan kuma aka samu ciki
daga wannan saduwar, to wannan cikinsa ne kuma abin da ta haifa ɗansa ne, domin saduwa ce
ta shubuha kamar yadda ya gabata. (Wannan duk a cikin As-Sharhul Mumti’u:
13/190).
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah
Assalafiy
Ga masu tambaya sai su turo ta
WhatsApp number: 08021117734
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.