Ticker

    Loading......

Sarkin Rafin Kuryad Dambo Alhaji Mamuda

Sarkin Rafin Kuryad Dambo Alhaji Mamuda
"Hawo da shirin yaƙi Na Dambo marinjayi,
Sarkin Rwahi mai ƙasak Kurya,
Ya kwan da shirin gaba" 

Inji Makaɗa Alhaji (Dr.) Ibrahim Buhari Abdulƙadir Mai Dangwale Narambaɗa Tubali a faifansa na Marigayi Dagacin Kuryad Dambo Ibrahim. Wannan shi ne Halifan wanda aka yiwa wannan Waƙar, watau Sarkin Rafin Kuryad Dambo na yanzu, Alhaji Mamuda. Na ɗauki wannan hoton Ranar Talata, 29/8/2017 a Fadar Mai Martaba Sarkin Gabas na Shinkafi, Alhaji Muhammadu Makwashi Isah dake garin Shinkafi, Jihar Zamfara. Allah ya jiƙan magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.
Daga Taskar:
Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments