𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum, Mlm so nake ai
min bayani saurayi ne yakai kudi, da sa rana har kayansa ya kai na lefe, to sai
aka ja lokacin da yawa, to mlm ya kasance saurayin in dai ya xo xance sai ya yi
ta kokarin taɓa ni
ko taɓa wani waje
daga jikina, ni kuma ba na son haka, mlm har faɗa
muke yi da shi wai a kan ba na ba shi jikina, wai sai ya ce min ai na riga na
xama matarsa, kawai ai rana ake jira, ni kuma mlm abun yana damu na, to shi ne
nake son na tsaya akan tafarki guda 1, na yi masa nasihar cewa babu kyau ya ki
ya gane, yana cewa ai ni na xama mallakinsa, dan Allah mlm ka fahimtar da ni
hakan da ya fada gaskiya ne ko na ki shi koda kuwa xai fasa aurena? Wannan ita
ce tambayata, kuma ina rokon malamina ya taimaka ya amsa min, na gode.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salamu, Subhánallah!
Allah ya qara tsare mana imaninmu, ƴar uwa lallai abin da wannan saurayi naki
ya faɗa maki ba
gaskiya ba ne, har yanzu ke ba matarsa ba ce, saboda addinin Musulunci ya
tabbatar cewa babu aure har sai an sami abubuwa guda huɗu kamar haka
1.Waliyyi.
2.Sadaqi.
3. Shahidai biyu adilai.
4. Siga.
Babu aure sai da waɗannan abubuwa guda huɗu kamar yadda malaman
Fiqhu suka tabbatar. Waliyyi shi ne mai aurar da mace, sadaqi kuma shi ne
haqqin da Allah ya ce namiji ya ba macen da zai aura, shahidai biyu adilai su
ne za su shaida cewa waliyyin wance ya aurar da ita ga wane, ɗan gidan Alhaji wane ko
malam wane, siga kuma ita ce maganar da waliyyinki zai faɗa cewa ni waliyyin wance
na aurar da ita ga wane bisa sadaqi kaza, sai wakilin ango ya ce na karɓa masa zan kai masa, in
kuma angon ne da kansa sai ya ce na karɓa.
To ƴar uwa malaman fiqhu sun ce babu aure sai
da waɗannan abubuwa,
wasu malaman kuma sun taqaita ne ga waliyyi da sadaqi da shaidu adilai guda
biyu. Don haka ƴar uwa wannan saurayi naki bai gama cika sharaɗin mallakarki ba har sai
an ɗaura maku aure,
saboda haka kada ki yarda ki amince masa ya taɓa
jikinki kwata-kwata, yin haka haramun ne, har yanzu ke ba matarsa ba ce, sa
rana ba ɗaurin aure
ba ne.
Idan kuma ya qi dainawa ki yi
masa barazanar cewa za ki faɗa
wa magabatanki, in Allah ya so zai ji tsoro ya kiyaye. Kuma duk masu yin haka
su tuba wa Allah su daina, in dai an yi tuba ingantacciya wadda babu tunanin
komawa ga saɓo, tare
da yin nadama ga abin da wuce, to tabbas
Allah yana karɓar
irin wannan tuba kamar yadda ayoyin Alqur'ani da dama suka tabbatar. Allah ya
shiryar da mu.
Kuma al''adu masu wahalarwa da
ake shigowa da su cikin harkar aure duk su suke qara haifar da waɗannan matsaloli, saboda
al'adun nan na kashe kuɗi
su suke sa a ja lokaci mai tsawo kafin aure har ta kai ga hakan ya sa shaiɗan ya shiga saqanin
saurayi da budurwa, don haka sai mu ji tsoron Allah, duk wani abin da bai zama
dole ba a harkar aure mu daina matsa wa kanmu da su, yin hakan zai taimaka
wajen yin aure cikin qanqanin lokaci kafin a kai ga fara zakkewa saɓon Allah.
Allah ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.✍🏻
Ga Masu Buqatar Shiga Wannan
Group Zaku iya bi ta Links ɗin
mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.