Tarihin Tashar Labin-Labin dake Tudun Wada, Gusau Babban Birnin Jihar Zamfara

    Tashar Labin-Labin dake Tudun Wada, Gusau Babban Birnin Jihar Zamfara ta samo asalinta daga wani Dattijo Direba mai Motar Haya ƙirar Fijo Siteshi Wagunu /Siteshiwagun mai lamba GS 1111 da ake kira Alhaji Garba.

    Saboda lambar Motarshi tana 1111/Eleven Eleven haka abokan sana'arshi ke kiran shi da suna Garba 1111/Garba Eleven Eleven, amma ga masu tu'ammali dashi wajen shiga mota da ba yan boko ba sai suna kiran shi Garba Labin-Labin. Sannu a hankali aka tciri/tsiri wurin tsayawa domin a ɗauki mutane a cikin Motoci zuwa garuruwa musamman dake gabasci/arewa maso gabascin Gusau anan Tudun Wada, Gusau. Zaman shi cikin mutanen farko - farko da ke wannan sana'ar kuma ga shi Dattijo sai mutane suna cewa "Zamu je Tashar Labin - Labin mu shiga Mota" wanda daga wannan ɗin ne  aka samu wannan sunan.

    A shekarar 1981, ya taɓa saka ni Motar wani Direba kyauta daga wannan Tashar(Tashar Labin - Labin, Tudun Wada, Gusau) zuwa Ƙaura Namoda ya kuma ce idan muka isa Ƙaura Namoda Direban Motar ya bani abun riƙewa in saka a aljihuna domin nayi mashi ƙorafi ne cewa bani da kuɗin Mota.

    Ya zuwa yanzu akwai zuriyarshi anan Tudun Wada, Gusau, Jihar Zamfara. Allah ya jaddada mashi rahama shi da sauran magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.
    www.amsoshi.com
    Daga Taskar:
    Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
    Ɗanmadamin Birnin Magaji
    Imel: birninbagaji4040@gmail.com
    Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.