Tatsuniyar 'Yar Ashana

    Wani mutum ne da matarsa suka d'au hanya da dukuduku don yin tafiya zuwa wani k'auye sada zumunta. Shi yana gaba ita na biye suna sauri. Burinsu su isa inda suka nufa tun kan rana ta fito. Can sai suka gamu da wata Hawainiya ta saje da ganye ta yi koriya shar. Ba sallama ba gaisuwa ta ce da su "Ina za ku kuke sauri da sanyi safiya nan?"

    Mijin ya juya cike da mamaki ya kalli matarsa ca yake ita ce ta yi maganar. Matarsa ta yi nuni da baki inda zancen ya fito ya kyalla ido ya ga hawainiyar tsaye in mutum ba lura ya yi da kyau ba ba zai ce da ita a wajen ba. Da jin maganarta ya kyautata zato ba bil Adama ba ce. Ya ce da ita "To kan in baki amsa ya sunanki?"

    Ta ce "Hawuya nake ko ka ce da ni Hauwa." Matarsa ta kau da kai ta ce "Ko dai ya ce dake Aljana" Maigidanta ya kalle abokiyar tafiyarsa ya ce "Ko kuma in ce da ita 'Yar Ashana ba." Hauwa ta yi murmishi ta ce da su "To ku yi hakuri Babana. Da alkhairi na nufe ku amma tunda kun ji zafi kar ku damu bari in ce da ku a sauka lafiya."

    Matar mutumin ta harare ta har za ta ce da ita wani abu mutumin ya yi sauri ya kwa6e ta ya ce da iyalinsa "Wuce." Bacin ta shige ya juya zai yiwa hawainiyar nan magana ya neme ta ya rasa ta yi masa dabo. Ya ce "Yar kwal uba. Har da wani kasa kanya ta na sayarwa. Da kin yabawa aya zak'i." Ya dinga juye-juye yana nemanta.

    Wannan kad'an ne daga wata tatsuniya mai suna 'Yar Ashana. Duk mai son ya ji yadda ta kaya tsakanin matafiyin nan da hawainiya MU GAMU A HIBAF23 ranar 14-16 Disamba, 2023 a Ado Bayero Mall dake Filin Baje Koli a titin Zoo Road, Kano.

    Tatsuniyar 'Yar Ashana

     Daga Taskar

    Malam Muhammad Tajajjini Tijjani
    Imel: mmtijjani@gmail.com
    Lambar Waya: +234 806 706 2960

    A Kiyayi Haƙƙin Mallaka

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.