Ticker

Tsayuwa A Bayan Malami

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Wace magana ce ta fi a kan: Tsayuwa a bayan malami a lokacin da yake gabatar da wa’azi ko karatu?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Malaman da suka yarda da a riƙa yin hakan gare su ko ga waɗansu malaman da ba su ba, me yiwuwa suna da dalilan da suka gamsu da su a kan hakan. Amma dai abin da Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce shi ne

« إِنْ كِدْتُمْ آنِفِاً لَتَفْعَلُونَ فِعْلَ فَارِسَ وَالرُّومِ يَقُومُونَ عَلَى مُلُوكِهِمْ وَهُمْ قُعُودٌ فَلاَ تَفْعَلُوا »

Ɗazun nan kun kusa yin irin aikin Farisawa da Rumawa: Suna tsayuwa a kan sarakunansu a lokacin da su ke zazzaune! Kar ku ƙara yin irin hakan. (Sahih Muslim: 955).

Ya faɗi wannan ne a cikin hadisin Jaabir Bn Abdillaah bayan ya ga yadda Jaabir ɗin tare da waɗansu Sahabbai (Radiyal Laahu Anhum) sun yi sallah a tsaitsaye a bayansa, alhali kuma shi a zaune ya yi sallar saboda larurar rashin lafiya da ta same shi a lokacin (Sallal Laahu Alaihi Wa Alaa Alihi Wa Sahbihi Wa Sallam).

A wurin fassara wannan maganar Al-Imaam An-Nawawiy (Rahimahul Laah) ya ce

فِيهِ النَّهْيُ عَنْ قِيَامِ الْغِلْمَانِ وَالْأَتْبَاعِ عَلَى رَأْسِ مَتْبُوعِهِمْ الْجَالِسِ لِغَيْرِ حَاجَةٍ

Wannan hadisin ya hana masu hidima da mabiya su miƙe tsaye a kan wanda suke girmamawa alhali shi yana zaune, ba da wata larura ba. (Sharh An-Nawawiy Alaa Muslim: 4/135).

A fahimtar malamanmu:

(i) Babu wata larura ko buƙata da za ta sa ɗan agaji ya tsaya a baya ko a gefe ko kuma a gaban mai wa’azi ko mai karantarwa, irin yadda ake yi wa waɗansu malamai a yau.

(ii) Kamar yadda hadisin ya nuna a fili, wannan koyi ne kawai ake yi da kafirai (Farisawa da Rumawa) a cikin ɗabi’unsu na rayuwarsu.

(iii) Koyi da kafirai a cikin duk wata keɓantacciyar ɗabi’a da ta shafi rayuwarsu abin hanawa ne a shari’ar musulunci, sai dai abin da ya zama dole ba makawa a gare mu.

(iv) A yau dai tsayuwar ɗan agaji a gaba ko baya ko a gefen malami ba za ta iya kare malamin daga ta’addancin ’yan ta’adda ba gare shi ko ga sauran masu sauraron wa’azinsa ko karatunsa.

(v) Tsayuwar waɗannan jami’an tsaron a bakin gate ko ƙofofin shiga inda ake gabatar da darussan, suna binciken masu shiga da fita ba tare da bambantawa ba shi zai fi amfani, kuma ya fi samar da natsuwa ta zuciya da gaɓoɓi ga masu sauraro da bin karatun, in shaa’al Laah.

Allaah ya ƙara mana kariya gaba-ɗaya daga sharrin dukkan masharranta.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

Ga Masu Buqatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi Waɗannan Links...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments