Cite this article: Bunza, U.A., Yusuf, J., Aliyu, A. & Mujaheed, A. (2023). Wasu Darussan La’akari a Zaɓaɓɓun Matanonin Adabin Baka Na Hausa. Zamfara International Journal of Humanities, (2)3, 39-49. www.doi.org/10.36349/zamijoh.2023.v02i03.005.
Wasu Darussan La’akari a Zaɓaɓɓun Matanonin Adabin Baka Na Hausa
Na
Dr. Umar Aliyu Bunza
Sashen Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto
Email: aliyu.bunza@udusok.edu.ng
Phone No: +2347063532532
Da
Jibril Yusuf
Sashen Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harsuna
Jami’ar Jihar Kaduna
Email: yusuf.jibril@kasu.edu.ng
Phone No: +2347030399995
Da
Abdulrahman Aliyu
Sashen Harsunan Nijeriya
Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, Katsina
Email: ksarauta@gmail.com
Phone No: +2348036954354
Abstract
This paper focused on the study of Hausa Orature as a
tool for emparting knowledge to contemporary society. Hausa Orature as
component of Hausa literature constitutes an indepth knowledge which can serve
as reference points in building a better society yet, researchers in this
century gives little considerations in analysing such angle. The medology used
in the analysis includes consultation of books and online sources, and citing
examples from the folktales, epics, stories and other related literature with
oral sources. The study shows how How Hausa Orature constitutes knowledge for
the betterment of the society today and in the future generation.
Tsakure
Manufar wannan
takarda ita ce nazarin labarun bakan Hausawa a matsayin
taskar ilimi ga al’ummar yau. Nazarin yana da muhimmanci ne ganin labaran baka
kamar sauran nau’o’in adabin bakan Bahaushe, ɗamfare suke da ilimin da zai iya zama
madogara ga al’umma, amma duk da haka manazarta ba su faye ba su muhimmanci ba
a wannan ƙarnin. Hanyyoyin da aka yi amfani da su
wajen gudanar da binciken sun haɗa: karance-karance a littattafai da
kuma yanar gizo tare da zaƙulo labaran da kuma yin nazarinsu. A ƙarshe, takardar ta gano cewa, labarun
bakan Bahaushe suna da matuƙar muhimmanci, musamman wajen bayyana
tunani da dabarun rayuwar al’ummar da ta gabata domin kasancewa madubi ga
al’ummar yau.
Fitilun Kalmomi: Darussa, La’akari, Zaɓaɓɓu, Matanoni,
Adabin Baka
1.0
Gabatarwa
Labarun baka nau’i ne na adabin baka na Hausawa.
Labaru ne da ake ƙirƙirar su a ka, a wanzar da su da fatar baki, kuma a adana su
a ka. Da yake adabi tamkar madubi
ne da ke nuna yadda rayuwa ke gudana, mai taimaka wa mutum ya ƙaru da ilmin jiya domin gyaran yau tare da daidaita
makomar gobe. A wannan takarda an mayar da hankali
kan labaran baka, domin rarabe aya da tsakuwa a kan abin da ya shafi
muhimmancin labaran na baka wajen taskace ilimi ga al’ummar yau. Nazarin, ya
shafi tsokaci ne kan yadda labarun baka suka
kasance a matsayin taskar ilimi ga al’ummar yau. An yi nazarin
ne ta
hanyar fito da batutuwan da suka shafi tarihi da sana’o’i da fasaha da
kimiyya a cikin labarun. Sannan aka fayyace yadda labaran za su
iya kasancewa hanyar gina rayuwar gobe, musamman ta fuskokin sadaukar da kai da
taimakon juna da aikin gayya da makamantansu. Daga ƙarshe an kawo jawabin kammalawa da
manazarta.
2.0 Ma’anar Labaran Baka
Masana irin su Ɗangambo, (2008) da Yahaya, da wasu, (1992); da sauransu, sun nuna cewa labaran
baka , su ne labaran da Hausawa suka gada daga kaka da
kakanni. Wato
sun kalli labaran baka a
matsayin nau’in adabi wanda ke ɗauke
da zantuttuka gajeru ko dogaye na hikima waɗanda ke koyar da wasu darrusa. Ke
nan, labaran baka, zance ne na hikima da ake shiryawa cikin azanci da yake zuwa
kara zube, kuma yake wanzuwa ta hanyar magana; zance ne mai ɗan tsawo wanda kuma yake ɗauke da dabarun zaman duniya ta
hanyoyi da matakai daban-daban. Babbar
hanyar isar da su
ita ce kunne-ya-girmi-kaka.
Haka kuma, labaran baka sun kasance ayyuka ne na fasaha da suka shafi
sarrafa harshe da kaifafa tunani daga cikin rayuwar al'umma ta yau da kullum. Labaru ne da aka fara samar
da su tun zamanin gargajiya, wato zamanin da Bahaushe ba shi da wata takamammiyar hanyar
rubutu. Ke nan, a ka, ake adana su. Kuma da fatar baki ake bayar
da su.
2.1
Ire-iren Labaran Baka
Labaran baka zance ne na hikima da ake
shiryawa cikin azanci da yake zuwa a kara zube, kuma mai ɗan tsawo, mai kuma
ban sha`awa da koyar da dabarun zaman duniya ta hanyoyi da matakai daban-daban.
Labarun baka sun haɗa da tatsuniya da almara da ƙissa da hikaya da tarihi da tarihihi. Haka kuma akwai
guntattakin maganganu na hikima kamar kirari, da karin magana, da
kacici-kacici, da zaurance, da salon magana da dai sauransu. Bari mu kawo bayanin wasu daga
cikinsu:
2.1.1
Tatsuniya
Masana da dama sun daɗe suna kallon tatsuniya ta fuskoki daban-daban, (Gusau,
2006) cewa ya yi “tatsunniya wani tsararren labari ne wanda magabata (musamman
tsofaffin mata) suke shiryawa cikin hikima da nuna ƙwarewa da naƙaltar harshe da ya ƙunshi wata shiryarwa da nuni zuwa ga halaye da ilmin zaman
duniya, sannan da saka nishaɗi da raha ga rayuwa da kuma cinye dare”.
Tatsuniya makaranta ce ta Hausawa wadda ta nan ne suke ilimantar da `ya`yansu tare da koya masu dabarun zaman duniya tun kafin su sadu da baƙin al’umma. Ta amfani da tatsuniya, Hausawa kan kaifafa tunanin `ya`yansu. Har ila yau, tsofaffi
ne kan shirya tatsuniya, domin ilmantarwa ga yara. Ana buɗe tatsuniya ne da ‘Ga ta nan ga ta nan ku’ a
rufe kuma da ‘Ƙurungus’. Galibi an fi yin tatsuniya da dare, in kuwa za a
yi da rana to sai an ɗaure
gizo.
2.1.2
Almara
Almara ita ce hanyar gabatar da wasu
matsaloli kara-zube ko kuma ta hanyar labari, sannan a buƙaci mai sauraro ya bayar da amsa ko kuma ya zaɓa tsakanin
abubuwan da aka ambata. Gusau, (1995), yana ganin almara wani shiryayyen labari
ne na jawo hankali da ake bayarwa don kaifafa tunanin masu sauraro ko nishaɗi. Saboda haka
almara ba ta fiye tsawo sosai ba, sai dai takan ƙunshi wani abu na ban dariya ko ƙalubalen da za a nemi mai sauraro ya warware. A taƙaice, almara labari ne ƙirƙirarre wanda ba lalle ne ya auku ba.
Tun kafin Hausawa su haɗu da Larabawa suna
da ire-iren waɗannan labaru na ban dariya da sa nishaɗi. Misalin almara
ta kaifafa tunani ko wasa ƙwaƙwalwa ko auna fahimta, wato mai buƙatar sai an yi tunani kafin a bayar da amsa, ita ce;
Wasu adadin tsuntsaye ne a sama, da kuma
wasu a ƙasa. Sai na sama suka ce wa na ƙasa da ɗaya daga cikinku zai hawo sama da
adadinmu ya zama daidai. Su kuma na ƙasa suka ce wa na sama da ɗaya daga cikinku
zai sauko ya haɗu da mu, da adadinmu ya ninka naku.
Shin tsuntsaye nawa ne a sama kuma nawa ne a ƙasa ?
Akwai kuma almara ta dabara mai buƙatar ka amsa tambayar in kai ne yaya za ka yi ? Wato mai ɗauke da ɗaurin gwarmai da
ake buƙatar ka kwance. Misali:
Mutum ne yake tafiya tare da akuya da kura da dawa.
Sai ya zo tsallake ruwa, kuma kana da damar
tsallakawa tare da abu ɗaya ne kawai cikin ukun da kake tafe da
su sannan ka dawo ka ɗauki sauran biyun, ɗaya bayan ɗaya ba tare da ka
bar wani ya cutar da ɗaya ba. Ga shi kuma kura tana iya cutar
da akuya, akuya kuma tana iya cutar da dawa. In kai ne ya za ka yi ka tsallaka
da su?
Akwai kuma almara ta barkwanci wadda
takan ƙunshi wasannin tsakanin ƙabilu ko garuruwa ko sana’o’i ko dangantaka da sauransu.
Ta haka ne ake ƙirƙirar labaru iri-iri da suke nuna rashin wayo ko gidadancin abokin wasan, lamarin ba
ya kai wa ga faɗa sai dai raha kawai. Misali, tsakanin Fulani da Barebari ko tsakanin Kanawa da Zazzagawa, da
sauransu. Misalin irin wannan almara ta barkwanci ta ƙunshi waɗannan:
i.
Wai Bafulatani ya ga biri ya ƙura masa ido, aka tambaye shi ko me ya sa yake kallon
birin, sai ya ce ; “Baffa sak !”.
ii.
Bayerabe
yana cin sabulu yana yamutsa baki ba daɗi, shi ya ɗauka abin ci ne. Da aka tambaye shi ya aka yi? Sai ya ce;
“kudina ina ci.”
2.1.3
Hikaya
Hikaya labari ne da ake bayarwa da ya faru dangane da mala`iku, ko
aljannu ko mutane ko rauhanai ko dabbobi ko tsuntsaye ko kuma ƙwari. Wani lokaci kuma takan ɗauki yanayin ƙago wasu labaran don ƙarin bayani kan wani abu ko kwaikwayon sa. Hikaya labari ne na manyan
mutane, ba annabawa ba, da abin da ya faru gare su. Misali, hikayar wani halifa
ko sahabi ko wani babban sarki. Hikaya kuma, takan ƙunshi wani abin mamaki da ya auku ko kuma dai wani labari mai koya darasi
ga zaman duniya (ko ma amfanin lahira). Hikaya kuma tana iya zama ta wani
attajiri ko kuma dai wani labari mai koya zaman duniya dangane da yadda mutum
zai iya bakinsa, (Ɗangambo, 2008). Misali hikayar kunkuru da gauraki da
sauransu.
2.1.4
Ƙissa
Ita dai wannan kalma tana ɗauke da ma’anoni biyu a cikin harshen
Larabci. Wato ma’ana ta lugga da kuma ta zahiri. A luggance, ƙissa na nufin
bibiya ko ƙididdigewa. Wato mutum ya bi diddigin wani abu har zuwa ƙarshensa (Sabe,
2011:43).
A ma’ana ta zahiri kuwa, kalmar ƙissa na nufin ba da labari dangane da
mutanen da suka shuɗe,
ko kuma ba da labarai a kan waɗansu abubuwa da suka auku a da. Watau wani labari da yake
kara zube wanda ya danganci rayuwar wasu magabata wanda ake cirowa daga cikin
Alƙur’ani mai girma. Wato bayanai a kan rayuwar Annabawa da
Sahabbai da wasu Waliyyai waɗanda Allah (SWT)
ya kawo labarinsu cikin Alƙur’ani.
Ana kuma samun ƙissa ta akasin
mutane na gari kamar su Fir’ana da Ƙaruna da sauransu. A taƙaice ƙissa wata hanya ce ta cusa wata manufa
cikin zukatan masu saurare (Sabe, 2011:43).
A ɓangare ɗaya kuma akwai ƙissar Bahaushe. Ita wannan ita ce ƙissar da aka gina ne bisa
tunanin Bahaushe, wato ga yadda labarin yake a zahiri, amma a ƙara masa wani abu
ko dai don daɗin labarin ko kuma domin a ƙara ƙayatar da mai
sauraro. Bisa ga wannan sai aka raba ƙissar Bahaushe zuwa gida biyu, wato issar
cinye dare wadda ta ƙunshi labarai da zantuttukan da mutane
suke yi don cinye darensu kawai. Akwai kuma ƙissar addini
wadda ta ƙunshi labarai ne
da ake tsarawa a kan wani abu da ya auku na addini a lokacin Annabawa da
Sahabbai da waliyyai da shaihunnai da sauransu (Sabe, 2011:44).
2.1.5
Tarihi/Tarihihi
Shi dai tarihi dai yana nufin wani labari ne na haƙiƙa da ya taɓa faruwa a cikin al’umma. To, amma shi tarihihi za a iya
cewa, wani labari ne na wasu abubuwa da suka taɓa
wakana na haƙiƙa a cikin al’umma, sai dai irin wannan labarin yana cakuɗe da wasu abubuwan da ba a tabbatar da
faruwarsu ba. Don haka idan aka ce tarihihi, a taƙaice ana nufin gurɓataccen tarihi, wanda aka cakuɗa shi, a tsakanin abin da ya faru na haƙiƙa da wanda bai
faru ba (Sabe, 2011:45).
Ana ƙirƙirar tarihihi a matsayin labari a ka, kuma a adana shi a ka,
akan sami sauye-sauye saboda tsawon zamani wajen wanzar da shi daga al`umma
zuwa ga wata al`ummar. Wannan dalili ne ya sa mutane ke ganin ba abin mamaki ba
ne don an sami ƙarya a cikin tarihihi. Tarihihi, ya ƙunshi labarai ne na kunne-ya-girmi-kaka,
waɗanda ba a iya tabbatar da haƙiƙanin aukuwarsu ba.
Kuma labarai ne da suka ƙunshi abubuwan da
suka danganci rayuwar Hausawa, musamman a jiya, akwai tarihihi kala-kala a ƙasar Hausa sai dai
waɗanda suka yi tashe sun haɗa da taririhin Bayajidda da tarihihin
Sarkin Katsina Korau da tarihihin Wali Ɗanmarina da Wali Ɗan Masani ko wani ɓangare na tarihin Usman Ɗanfodiyo ko Ɗanwaire da
makamantan su (Sabe, 2011:45).
Duk wanda ya duba ɗaya daga misalin da aka bayar zai fahimci labarai ne masu ƙunshe da gaskiya
da ƙarya duk a cikinsu, wato wani ɓangare na labarin ƙarya ce wani kuma akwai alamun gaskiya.
3.0 Labaran Baka a Matsayin Taskar Ilimi ga Al’ummar Yau
Tabbas! Labarun bakan Bahaushe wata
makaranta ce mai zaman kanta, ko kuwa ana iya bayyana su a matsayin taskar
ilimi ga al’ummar wannan
zamanin musamman idan aka nazarce su don ganin irin ƙunshiyar da suke ɗauke da ita, domin kuwa cike suke da hikima da basira da kuma tunani irin na ɗan’Adam wanda ya ƙirƙira kan wani abu, ya kuma
aiwatar da shi ta fatar baki, domin yaɗa wata manufa don koyarwa ko kuma hannunka-mai-sanda ko kuma don samun nishaɗi a tsakanin al’umma musamman ƙananan yara. Haka
kuma labaran bakan Bahaushe ba su tsaya kan nishaɗi kaɗai ba, akan yi amfani da su don koyar wa yara da nusar da su ko zaburar da su ko kuma yin amfani
da labaran dom kaifafa tunani ga yaran. Wataƙila
wannan shi ne dalilin da ya sa labaran suka ƙunshi
kusan kowane fanni na rayuwa da zamantakewar al’umma.
Ta la’akari da waɗannan bayanai da
aka kawo a sama, an a dubi waɗansu batutuwa don ganin yadda tasirinsu
ya fito a cikin labaran bakan Bahaushe. Batutuwan sun haɗa da: kimiyya da
fasaha da tarihi da sana’o’in Bahaushe da ma wasu waɗanda a cikin su ne
za a kafa hujjojin da za su tabbatar da kasancewar labaran a matsayin taskar
ilimi ga Bahaushen jiya, har ma da na yau idan lokaci ya ba da dama. Mu je
zuwa!
3.1
Tarihi
Tarihi wani labari ne na haƙiƙa da ya taɓa faruwa a cikin al’umma (Sabe, 2011:45). Ke nan, tarihi
taska ce mai ƙunshe da rayuwar da ta gabata, inda ake fasalta yau da kuma
hasashen yadda gobe za ta kasance. Wasu daga cikin labarun bakan Bahaushe sun
kasance ƙunshe da tarihin al’ummar ƙasar Hausa da wasu maƙwaftansu, ko kuma wasu al’adu nasu waɗanda sun shuɗe. Labarin Gardamar Wali Ɗanmasani da Wali Ɗanmarina ya baje
mana wannan fasali a faifai:
Gardamar Wali Ɗanmasani
da Wali Ɗanmarina
Wata rana gardama ta kaure tsakanin wani mutum da matarsa
kan ganin watan Azumi. Mijin ya ce yau ne watan zai tsaya, matar kuma ta ce sai
gobe. Suka tashi suka iske Wali Ɗanmasani domin neman fatawa, suka tarar
yana zaune tare da sauran almajiran Wali Ɗanmasani.
Wali Ɗanmasani ya ce yau ne wata zai tsaya.
Shi kuwa Wali Ɗanmarina wanda yake almajirin Malamin ne, cikin ladabi da
girmamawa ya ce gobe wata zai tsaya. Daga nan sai gardama ta koma tsakanin
malami da ɗalibinsa.
Da yamma ta yi lokacin duban wata, jama’a suka taru a
unguwar malamai domin ganin yadda al’amarin ganin watan zai kaya. Kowa ya ɗaga kai sama yana duban ko wata zai
tsaya.
Da aka ɗauki lokaci, sai Wali Ɗanmasani ya shiga
gida ya sami sakaina ya feƙe ta daidai tsayuwar wata. Ya jefa ta sama, sai ta manne.
Mutane suka ɗauki kuwwa malam ya yi kaye.
Shi kuma Wali Ɗanmarina da ganin haka ya gane sakaina
ce, sai ya tashi tsaye, ya miƙa hannunsa ya ce sakaina ta faɗo. Kafin ka ce kwabo, sai ga sakaina a
tafin hannunsa. Sai kuwa kuwwa ta sake ɓarkewa.
Wali Ɗanmasani ya ji sabuwar kuwwa, sai ya
fito ya ga dalilinta, ya iske sakaina a hannun almajirinsa. Da ganin haka sai
ya ce wa almajirin nasa, ‘‘Bayan mutuwarka babu mai sanin ɗaya daga cikin danginka.’’ Shi kuma
Wali Ɗanmarina ya ce masa, ‘‘Kai kuma babu mai sanin kabarinka, ko
waɗanda suka rufe
ka.’’ Haka kuwa lamarin ya kasance, babu wanda ya san ɗaya daga cikin dangin Wali Ɗanmarina bayan
mutuwarsa, haka kuma babu wanda ya san inda kabarin Wali Ɗanmasani
yake bayan mutuwarsa, (Bunza, 2012:9-10).
Ko ba komai wannan labari ya nuna wani ɓangare na tarihin waɗannan mashahuran malamai da aka yi a ƙasar Katsina.
Wannan ya sake jaddada yadda labarin baka ke ɗamfare da tarihin al’umma. Haka kuma
labarin Wali Ɗanmasani da Wali Ɗanmarina sun nuna irin baiwar da Allah
Ta’ala ya yi cikin ƙasar Katsina, ya raya wasu bayinsa da tarihinsu bai ɓacewa har abada (Bunza, 2012:13.
3.2
Sana’o’i
Dangane da ma’anar sana’a, a cikin Ƙamusun Hausa na CNHN (2006:186) an bayyana sana’a ko
sana’o’i da cewa: Aikin da mutum yake yi don samun abinci, misali manomi
sana’arsa noma, wanzami kuwa sana’arsa aski ne. Saboda haka, sana’a hanya ce ta neman abinci ga
mutum. Kowace al’umma tana da sana’o’in da take yi don samar da abinci da
sauran kayan buƙata (Bunza,
2015:130). Daga cikin labarun bakan Hausawa akwai waɗanda suka fito da
irin sana’o’in da Bahaushe yake da su tun can azal, waɗanda suke ƙunshe da bayani kan waɗannan sana’o’in, wanda hakan ke nuna cewa tun can da
Bahaushe ba ci-ma-zaune ne ba. Shi ya sa wasu labarun baka suna ƙunshe da bayani kan wasu sana’o’i na wasu al’ummomi da
kuma nuna muhimmancin sana’ar ga rayuwa. Misali,
a labarin:
Basha Jagora
An nuna cewa akwai wasu mutane da suke zaune a dajin
tsakanin Bidda da Kwantagora waɗanda
ba su da wata sana’a sai farauta da neman zuma. Ta wannan sana’a tasu ta neman
zuma suka waye da tsutsuwa ‘Basha’ wadda take jan su zuwa wurin da ke da zuma.
A hankali har ta fara kai su mahallaka. Ta kai mutum ɗaya ga zakanya mai ɗiya ta kashe shi. Ta ja na biyu, ta kai, Allah ya kare shi,
ya kashe zakanyar. Daga wannan lokaci mutane suka nemi layar zana, suka kuma riƙa shiga daji da kwari da baka (Bunza, 2015: 130).
Wannan labarin ya nuna yadda wasu mutanen da ke maƙwaftaka da ƙasar
Hausa suke gudanar da sana’arsu. A ɗaya ɓangaren kuma an nuna muhimmancin shiri a duk al’amarin da za
a sa gaba na fita nema, musamman dabarun kare kai daga hare-haren mugayen
halittu.
Bugu da ƙari,
idan aka yi la’akari da labarin Bakatsine Mai Kan ƙwarya, ko da yake akwai ɓurɓushin wauta-wauta a cikinsa, amma ya fito da irin zaman
mutanen Katsina mazajen tsaye ga riƙon sana’a domin kore wa bakinsu ƙuda da hana wa kansu zama ci-ma-kwance, ‘yan ku-ci-ku-ba-mu.
Wannan ya sa ɗan alewa ya jajirce da ɗaukar
masakin alewarsa yana yawo gari-gari yana tallatawa (Bunza, 2012:12), har dai
‘tsautsayi’ ko ‘wauta’ ta sa bayan ya sha fura ya kwanta bacci a inuwa garin
magagin bacci kansa ya shige ƙwaryar
alewa ya maƙale saboda danƙo. Ƙarshe dai sai da aka yi jidali kafin aka cire masa bayan ya
farka daga bacci, (Bunza, 2012:4-5).
3.3
Falsafar Bahaushe
Falsafa hanya ce ta tunani da ƙoƙarin samun bayanin
dukkan al’amurra da suka shafi duniya da ɗan’Adam
da inda suka sa gaba (Dunfawa, 2013). Ke nan, falsafa wani tsarin ilmi ne mai
alaƙa da imani, da tataccen tunani
mai zurfi a kan al’amarin rayuwa da halita, da duniya, da kuma nazarin halayyar
wani. Labarun baka na Bahaushe suna haska mana irin falsafar Bahaushe, wato
tunaninsa game da duniya, da yadda yake kallon duniyar da halittun da suke
cikinta. Misali, Bahaushe yana alaƙanta wasu tsuntsaye da wayo, musamman tsuntsaye irin su
hankaka da makwarwa da yautai da kurciya da tsadda da sauransu. Bari mu ɗauki labarin hankaka mai hikima domin nuna misalin yadda
Bahaushe ke tunani game da tsuntsaye musamman hankaka:
Labarin Hankaka Mai Hikima
Wani hankaka ne
yana jin ƙishirwa, yana
cikin fafutukar neman inda zai sha ruwa, sai ya hangi wani tulu. Ya yi ƙasa-ƙasa ya sauka a bakin tulun, ya leƙa ya ga akwai ruwa a ciki sai dai kash!
Yawan ruwan rabin tulu ne, bakinsa ba zai kai yadda zai sha ba. Yana nan bakin
tulu, yana tunani. Ga ƙishirwa yana ji ,
ga ruwa yana gani, amma ba hali ya sha, yaya ke nan? Kawai sai ya je yana
tsinto duwatsu yana jefawa cikin tulun, da haka ruwa ya riƙa yiwo sama har ya kai yadda bakin
hankaka zai kai, ya sha iyakar yadda ya ishe shi ya tashi (Muhammad, (2014).
Abin lura a wannan labarin shi ne, Bahaushe yana danganta
wayo ga hankaka, bisa wannan dalili ne ya sanya hankaka bai fid da tsammani ga
shan ruwan tulu ba, duk da bakinsa ba zai kai ba. Don haka sai ya ci moriyar
wayonsa ya riƙa ɗebo dutse yana jefawa cikin tulun, ruwa na fallatsowa yana
sha, har ya sha ya ishe shi. Ke nan, in da wani tsuntsun ne wanda Bahaushe ba
ya kallon sa a matsayin mai wayo, to da sai dai ya haƙura da shan ruwan, tun da bakinsa ba zai kai ba.
3.4
Kimiyyar Gargajiya
A nan, idana aka yi batun kimiyyar
Bahaushe a gargajiyance ana nufin hikimar da yakan yi amfani da iya wajen
sarrafa wani abu ko samar da wani daga wani. Saboda haka, Bahaushe yana da
kimiyyarsa ta gargajiya wadda yake sarrafa duniyarsa da ita domin samun abin
masarufi musamman ta sana’o’insa na gargajiya. Shi
ya sa wasu labarun bakan Bahaushe kan zo da bayanin irin kimiyyar da Bahaushe
ke da ita a gargajiyance. Misali, labarain Bakatsine Mai Kan Ƙwarya ya nuna mana
yadda kimiyyar sarrafa alewa take da kuma yadda ake sarrafa wuta a kimiyyance
domin narkar da abin da ya daskare.
Bakatsine Mai Kan Ƙwarya
Wani ɗan alewa a ƙasar Katsina ya ɗauki ƙatuwar ƙwaryarsa danƙare da alewa, ya nufi Caranci cin kasuwa. Hantsi na yi,
ban ruwan dawaki, ɗan alewa ya isa kasuwa, ya raɓa gindin inuwar wata ‘yar rumfa, ya sauke ƙwaryarsa ta alewa. Ya sa baki ya kira
wata mai tallar fura da wata mai nono. Ya sayi furar kwabo biyu, nonon taro, ya
yi damun ƙyale moɗa. Da ya gama, ya ɗebe hularsa ya
ajiye gefe guda, ya sa ludayi ya yi wa furan nan kaf. Ya sa ruwa ya ɗauraye ƙwaryar. Ya zauna
yana hutawa.
Can ta gero ta
fara kama shi, sai ya riƙa lumshe ido yana
gyangyaɗi. Sai ya yi nan lau, ya buɗe ido, ya sake yin lau, ya buɗe ido.
Jim kaɗan sai ya kishingiɗa gyangyaɗi na ta ɗaukarsa. Can barci
ya rufe masa ido, bai san abin da yake yi ba, sai ya jawo ƙwaryarsa ta alewa, ya aza kansa bisa
alewar. Ka san takan daskare ne kamar dutse, sai an narka in za a ja a sayar.
Gogan naka, ko da
ya samu abin tayar da kai, sai ya duƙa barci, har da saleɓa. Can rana ta
take tsaka, inuwar rumfa kuwa ta janye, alewa ta ce me za ta yi ko ba narkewa
ba. Ashe sa’ad da alewa ke narkewa, kan gogan naka sai lumewa yake ciki, bai
sani ba. Ga shi ko da suma cike da kai.
Can bayan azahar,
da rana ta yi sanyi, sai alewa ta sake daskarewa, da kan ɗan alewa nutse ciki. Zuwa can kasuwa ta cika maƙil, sai hayaniyar mutane ta tayar da
goganmu. Ya buɗe ido, ya yi miƙa, ya yi hamma, ya yunƙura zai tashi, sai ya ji kansa
gingirim. Ya yi, ya yi ya tashi, ya kasa. Sai ya fasa kuka. Nan da nan kasuwa
ta yi caa, aka taru wajensa.
Dattijai suka kama
ƙwaryar alewa, suna
ƙoƙari wai su cire ta. In sun ɗan ja, sai ɗan alewa ya ce,
‘‘Wayyo! Wayyo! Ku tsaya, ku tsaya!’’
Yara suka kewaye
suna ta dariya, suna cewa, ‘‘Ihu! Ihu! Ga mai kan ƙwarya!’’
Mutane suka rasa
yadda za su yi da shi. Sai wani ɗan alewa kuma ya
ba da wata dabara, ya ce, ‘‘A kawo shi nan wajen masu tsire, a narka alewar.’’
Nan da nan aka kinkime shi da ƙwarya riƙe, aka je aka narka alewa. In an dakata
wajen wuta, ɗan alewa ya ce,
‘‘Ku juya ni, ku juya ni, zan ƙone!.’’ Haka dai
aka yi ta yi sannu sannu, har aka samu aka cire masa ƙwaryan nan daga kansa (Bunza, 2012:5).
A wannan labarin an nuna kimiyyar
Hausawa ta hanyar amfani da wuta don sarrafa wasu buƙatun rayuwarsu. Sannan kuma, sana’ar alewa da yadda ake sarrafa ta sun
tabbatar da yadda Bahaushe yake da kimiyyarsa a gargajiyance tun kafin ya haɗu da wata baƙuwar al’umma. haka kuma dabara da suka yi wajen amfani da wuta domin cire ƙwaryar da ta maƙale a kan ɗan alewa, kimiyya
ce ta gargajiya kamar yadda ta fito a cikin labarin. Bugu da ƙari, ko a labarin Ƙunar Baƙinwake mun ga yadda kimiyyar gargajiya take, musamman
abin da ya shafi sarrafawa da samar da tukwane da toya su a wuta da
makamantansu.
3.5
Fasahar Al’umma
Al’ummar Hausawa suna amfani da
adabinsu wajen kimshe fasaharsu. Shi ya sa ta hanyar labarun baka za a iya naƙaltar fasahar al’ummar Hausawa. Misali, a labarin Wani
Maciji da Zakara a Zariya, za a ga yadda labarin yake ƙunshe da fasahar al’ummar Hausawa wajen magance matsalar da
aka hango tun kafin faruwarta:
Labarin Wani Maciji da Zakara a Zariya
A cikin Birnin Zariya an yi wani
shahararren malamin addinin Musulunci, mai suna Malam Shehu na Malam Na'iya.
“Wata rana yana cikin bayar da karatu a zawiyya, sai yara suka fito daga cikin
gida da mushen zakara a hannunsu. A ɗaya
hannun kuma da mushen maciji, sai Malam ya tambaye su ina za ku? Me ya faru?
Yara suka ce ai wannan macijin ne ya sari zakara ya kashe shi, sai su kuma suka
kashe macijin. Abin mamaki, sai Malam ya ce su ajiye mushen zakaran su tafi su
jefar da mushen macijin. Bayan ɗan
lokaci ana cikin karatu, sai ga wani maciji yana janye da mushen macijin da aka
jefar ya shigo cikin zaure. Nan take, sai malamin nan ya sa aka ɗauko mushen zakara, ya karɓa ya ajiye a gaban macijin. Sai ya ce: “Ga ɓarnar da ya yi mana. Ya kashe zakara ne, mu kuma muka kashe
shi.” Sai kawai aka ga macijin nan ya ɗauki mushen macijin nan ya juya ya tafi abinsa (Muhammad,
2014).
A wannan
labarin, fasahar Bahaushe ta fito ƙarara inda
aka nuna yadda malamin cikin hikima ya kauce wa abin da zai iya faruwa,
sakamakon kashe macijin da yara suka yi. A matsayinsa na babba ya san cewa
akwai yiwuwar macijin aljani ne (ko kuma aljani ya shiga jikinsa), tun da an
san idan maciji ya riƙa, ya gawurta aljani kan shige
shi. Saboda haka sai ya ce yaran su ajiye mushen zakaran domin ko da
‘yan’uwansa sun biyo baya, to za su gane wa idonsa ɓarnar da ɗan’uwansu ya
yi har aka ɗauki fansa. Wannan ya tabbatar da fasahar al’ummar Hausawa cikin
labaransu na baka. Haƙiƙa, za a iya
cewa in da za a yi amfani da irin wannan fasahar, to da an yi maganin matsalar
tsaro da ta addabi ƙasar nan, domin kuwa za a haƙe tutsiya tun daga tsittsigen.
4.0
Labaran Baka a Matsayin Hanyar Gina
Rayuwar Gobe
A wannan gaɓar an zaɓi wasu batutuwa da suka shafi gina rayuwar gobe aka yi
bayanin yadda suke fitowa cikin labaran bakan Bahaushe. An kawo misalan labaran
da suke nuna sadaukar da kai da aikin gayya da taimakon juna da kuma nuna illar
ƙarya da mutunta ɗan’Adam.
4.1 Sadaukar Da Kai Wurin Neman
‘Yanci
Babu wata al’umma da ba ta son ta rayu
a matsayin ‘yantacciya. Kasancewa cikin ƙangin bauta yakan
sa waɗansu su yi tunanin mafita ko da kuwa za ta zamo ajalinsu, matuƙar dai na baya za su rayu cikin ‘yanci. A wasu lokutan,
labaran baka sukan nuna darasi na sadaukar da kai domin ceto al’umma daga wani
hali da suka shiga. Ire-iren waɗannan labaran
sukan kasance na ƙundumbala da
tauraron labarin ya yi domin kuɓutar da al’umma
daga cikin wani halin ƙunci da suke ciki,
don gobensu ta yi kyau. Irin wannan sadaukarwa ta fito ƙarara a labarin:
Ƙunar
Baƙinwake
A zamanin da, an yi wani mutum marini mai ƙarfi wai shi Baƙinwake a Katsina. A daidai wannan lokaci kuwa akwai wani ɗan sarki da ya ƙasaita, ana jin tsoron sa a dukkan faɗin ƙasar, saboda zalunci da rashin tausayinsa. Su kuma mutanen
fada a duk lokacin da ya fito sai kirari kawai suke masa, shi kuma sai girman
kai, ba ya ko magana da talaka, sai dai ya sa a buge shi a ɗaure.
Shi ɗan
sarkin nan yakan fita kilisa lokaci-lokaci. Ranar nan zai fita kilisa sai ɗan sarkin nan ya ce wai shi ya gaji da hawan doki. Nan da
nan wani bawansa ya ce a je a kawo raƙumi. Ɗan sarki ya ce ya gaji da hawan raƙumin ma. Daga nan sai wani bawansa ya ce, ‘‘Ranka ya daɗe, yanzu ba abin da ba ka hau ba, sai mutum.’’
Da yake an sosa wa ɗan sarki abin da yake so, sai ya ce, ‘‘Haka ne. A je cikin
birni a kamo ƙato
guda, a yi mini sirdi bisansa.’’
Daga wannan lokaci sai ɗan sarki ya daina hawan dabba sai dai mutum. Idan zai hau
sai a ɗaura masa sirdi a baya, a rataya masa igiya a wuya, ya dafa
wani mutum, sa’annan ya hau a yi ta gudu da shi kamar dai ya hau doki. Kullum
haka yake yi. Yau a kamo ƙato daga wannan unguwa, gobe wata unguwa.
A kwana a tashi, sai hawa ya kawo kan Baƙinwake. Mai unguwarsu ya zo ya gaya masa gobe shi za a hau,
kada ya je ko’ina.
Baƙinwake
ya yi shiru, ya ce, ‘‘To, ta faru ta ƙare!.’’Bayan da mai unguwarsu ya wuce, sai Baƙinwake ya tafi marinarsu ya sami tarin ciyawa ya sa masa
wuta, ya koma gida ya jira wayewar gari. Kafin gobe wuta ta kama ciyawa
rigirigi.
Gari ya waye, ɗan
sarki ya aiko ga mai unguwa a kai masa ƙaton da zai hau ya je kilisa. Mai unguwa ya kira Baƙinwake ya ce ya hanzarta ya je ɗan sarki na jiran sa. Baƙinwake ya shiga gida ya yi ban kwana da iyalansa. Mutane
suka nemi su ji ko lafiya, ya ƙi faɗin
aniyarsa.
Da isar Baƙinwake fada aka yi masa sirdi, ɗan sarki ya hau, yana gaba sauran jama’a na biye. Bayan da
suka ƙare
kilisa, za a dawo gida sai aka bi ta hanyar marina. Suna nan zuwa har suka kai
marinar su Baƙinwake,
suka iske wuri ya cika da mutanen gidan su Baƙinwake. Idan Baƙinwake ya yi sanyi, sai ɗan sarki ya yi masa ƙaimi ya tsala masa bulala. Da Baƙinwake ya zo daidai ciyawar da ya sa wa wuta jiya, sai ya
fara sakin hanya, ɗan sarki na karkata linzami, Baƙinwake na ƙiyawa. Dogarai na ‘‘Hattara dai, zaki! Linzami!’’ Shi kuwa ɗan sarki ya ruɗe
sai bulala yake tsala wa Baƙinwake, yana masa ƙaimi. Da mutane suka gane nufin Baƙinwake sai suka fara ‘‘Kai, kai, kai! Shi kuwa ɗan sarki sai ihu yake yi, yana ƙoƙari ya kubce. Kafin dogarawa su cece shi, Baƙinwake ya kai ga wuta, ya yunƙura ya ce; ‘‘Tun nan duniya zan fara jefa ka wuta, daga yau kowa ya huta.’’ Sai ya yi tsalle ya faɗa tsakiyar wuta tare da ɗan sarki (Bunza, 2012:6-8).
An ce tun daga wannan lokaci ba a sake samun wani ɗan sarki a Katsina ko ma a kowane ɓangare na ƙasar
Hausa, ya sake hawan mutum ya yi kilisa ba. Ke nan, wannan sadaukar da kai da
Baƙinwake ya yi, ya kuɓutar da al’ummar ƙasar Katsina da ma sauran ƙasashe daga wani nau’in zalunci daga masu mulkinsu na gargajiya. Tun daga wannan
lokaci aka sami karin maganar nan ta ‘Ƙunar Baƙinwake’. Wannan yana nuna mana ko a yanzu idan
ana buƙatar kawo gyara
daga wata matsalar da ta yi wa al’umma katutu, sai wasu sun sadaukar da rayukansu don goben
wasu ta yi kyau. Domin kuwa labarin Ƙunar Baƙinwake
ƙarara ya nuna irin sadaukar da kan
mutanen Katsina wajen ceto ‘yan’
uwansu daga halin ƙunci da baƙin ciki na baƙin zaluncin da wani ke yi masu. Ba tsoro, ba mugun mutuwa.
Wannan shi ya sa Baƙinwake ya sadaukar
da ransa, ya yi ƙunar mu je mu mutu
tare da ɗan sarkin da ya addabi talakawa a nasa lokaci (Bunza,
2012:12).
4.2
Ayyukan Gayya
Aikin gayya wani aiki ne da ake taimaka wa juna ta hanyar haɗuwa a yi aikin taimakon kai da kai, ko kuma idan wani ba shi
da lafiya ya kasa gyara gonarsa sai a yi gayyar ‘yan’uwa da abokan arziƙi a tafi a nome masa kyauta (Muhammad, 2014). An lura za a
iya amfani da darussan cikin labarun baka domin gina rayuwar gobe, musamman ta
la’akari
da yadda wasu labaran ke ɗamfare da darussan da ke nuna muhimmancin ayyukan gayya a
cikin al’umma. Misali, tatsuniyar:
Barewa ta Auri Mutum
A cikin tatsuniyar, an nuna wata barewa ce ta rikiɗa ta zama mace kyakkyawa, ta ɗauki ɗan
kwatashinta ta ɗora a kanta, ta tafi tsakiyar karofi ta ajiye.Ta ce duk
wanda ya jefa ‘yar tsakuwa ta buɗe
kwatashin shi ne mijinta, sai wannan ya ɗauki tsakuwa ya jefa, bai buɗe ba.Wancan ya jefa tsakuwa bai buɗe ba, sai aka samu wani ya jefa ‘yar tsakuwa sai ya buɗe, sai ta ce ta samu miji shi za ta aura, sai suka tafi
garin su yarinyar wurin iyayenta, aka ɗaura mata aure da wannan mutumin, ta zo ta zauna a gidan miji.
Kullum ranar girkin ta sai a ce ta je, ta ciro kuɓewa a gonar miji ta yi miya.Da ta je gonar sai ta yar da
zaninta, ta yi birgima a ƙasa ta zama barewa, sai ta yi kiran ‘yan’uwanta, ta hanyar waƙa, ta ce:
Cikal-cinkal, cinkali kalaya.
Turmin ‘yankale ya yi fure, ceɗiya.
Tudu na korar tudu marina.
Tudu na korar tudu da ƙaho.
Ban da kwatsakwatsan ban da ƙanƙana.
Nan da nan sai ‘yan uwanta su zo su taro su ciccinye kuɓewa, in sun gama sai su tafi ta gida, ita kuma sai ta yi
birgima ta koma mutum ta ɗauki
zaninta ta ɗaura, ta koma gida tana cewa ni da gangan aka tura ni ga shi
nan ban samo komai ba. To wata rana sai mijinta ya bi ta gonar sai ya gan ta tana
birgima, da ta gama birgimar sai ya ga ta rikiɗe ta zama barewa,
sai ya ga ta yi kiran ‘yan’uwanta bareyi da waƙa. Bareyi suka taru a gonar jingim, duk suka cinye kuɓewar suna cikin ci
sai ya fasa su sai ya ga matarsa ta gan shi, ya koma gida sai ta ɗauko kuɓewar ta biyo shi
ta tarar da shi a gida. Ya ce wace ce? Ta
ce ni ce. Ya ce ina za ki? Ta ce ɗaki
za ni. Ya ce a’a koma daji. Sai ta ce ta ƙi. Sai ya biyo ta a guje ya kora ta daji daga nan ba ta sake
dawowa ba (Muhammad, 2014).
Abin lura a nan shi ne, duk da tatsuniyar tana ɗauke da wani saƙo na daban, amma tana ƙarfafa aikin gayya. Idan
aka yi la’akari da yadda barewa take yin waƙa ‘yan’uwanta su taho su taya ta cinye kuɓewa, wanda in ita kaɗai ce
ba za ta iya cinyewa ba. Wannan ya yi daidai da karin maganar da ke cewa hannu
da yawa maganin ƙazamar miya, ko
kuma hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka, da
sauransu. Bugu da ƙari, tatsuniyar ta
nuna hoton rayuwa irin ta zaman gandu wadda Bahaushe ke yi. A irin wannan zama
tamkar ana ayyukan gayya wajen taruwa a riƙe gida da ƙarfafa
zumunci da ‘yan’uwantaka da zaman tare.
A yau zamani ya banzantar da aikin gayya, komai sai dai kuɗinka ya ba ka, in ba ka da shi sai dai ka haƙura, ashe kuwa da za a koma a rungumi irin waccan rayuwa mai
ruhin taimakon juna ta fuskar aikin gayya kamar yadda suka fito a tatsuniyar
Barewa ta Auri Mutum, lallai da an gina rayuwar gobe ingantacciya.
4.3
Taimakon Juna
Bahaushe mutum ne mai taimakon juna a tsarin zamantakewarsa.
Tun ta hanyar duba da yadda gidansa yake za a tabbatar da haka. Har ila yau,
duk inda Bahaushe yake a da, za a same shi ba ya ƙaunar wani abu mara daɗi
ya sami ɗan’uwansa, kamar ciwo ko mutuwa, ko wata asara kamar gobara,
ko sata da sauransu. In kuma wata ƙaddara ta sami ɗan’uwansa,
yana taya shi jaje da alhini. In kuma abin alheri ya samu ɗan’uwansa, misali idan aka yi wa wani haihuwa, ko kuma aure,
a nan ma Bahaushe yana taya juna farinciki da murna (Muhammad, 2014). Duk waɗannan suna ƙara
ƙulla zumunci da taimakon juna a
tsakanin al’umma.
A wannan fuskar ma za a iya amfani da labaran baka a matsayin hanyar gina kyakkyawar
al’umma ta fuskar taimakon juna. Alal misali, idana muka dubi almarar Ɗanfulani da Kaɗo, za ta haska mana wannan fasali.
Almarar Ɗanfulani da Kaɗo.
Wata rana an yi wa Ɗanfulani haihuwa, ranar suna sai ya gayyaci Kaɗo zuwa taron suna. Gari ya waye Kaɗo ya shirya ya nufi ruga, don amsa gayyata. Bayan an yi taro
an sanya wa jariri suna, aka yi shagali aka watse. Ɗanfulani bai ba Kaɗo
komai ba, sai ya ɗauko ƙahon sa, wanda aka yanka ya ce da Kaɗo ga shi ka yi tururu (ƙahon hura). Kaɗo
ya karɓa ya yi godiya, bai nuna ya damu ko ɓacin rai ba. Ashe Kaɗo ya yi alƙawarin sai ya rama….. (Muhammad, 2014).
Idan aka yi la’akari da wannan almarar,
za a iske cewa tana nuna muhimmancin taimakon juna da kuma gudummawa da
taimakekeniya a tsakanin al’umma, musamman a yanayi na sha’ani ko buki na aure
ko haihuwa. Shi ya sa ko da Kaɗo ya zo suna gidan
Ɗanfulani, a bisa yadda al’ada ta tanadar ya kamata ya zo masa da
gudummaw, amma bai zo da shi ba, shi kuma Ɗanfulani sai cikin hikima ya nuna masa ya dace ko don nan
gaba ya lura da muhimmancin taimakekeniya a mu’amalarsa da jama’a. Saboda haka ne Ɗanfulanin ya ba Kaɗo
kyautar ƙahon sa. Almarar
tana nuna mana muhimmancin taimakon juna, don haka za ta iya zama hanya ta gina
rayuwar al’umma.
4.4
Illar Ƙarya
Ƙarya mugun guzuri! Ƙarya na nufin maganar da ba ta gaskiya
ba ce. (Sa’id, 2006). A ra’ayin Bunza (2009) yana ganin cewa, ƙarya ita ce faɗar maganar da ba a yi ba, ko ba a gani
ba, ko ba a tabbatar ba, da kuma yin ƙari ga abin da aka
ji ko aka gani, ko yin ragi a gare shi. Idan aka yi la’akari da labaran baka za a ga cewa, Bahaushe ba ya son ƙarya, ya ƙyamace ta, wannan
ya sa ma yake kiran ta mau gajeren zango. A cikin tatsuniyoyin Hausa za a ga duk
tauraron da ya yi ƙarya, komin nasarar da ya samu kafin
tatsuniyar ta ƙare, sai an nuna ƙarshensa bai yi masa kyau ba. Ga
misali daga tastuniyar Gizo da Dodanniya:
Tatsuniyar Gizo da Dodanniya
Wata rana Gizo ya
tafi gidan Dodanniya ya karɓo bashin bajimin
sa, da alƙawarin zai biya
shekara mai zuwa. Ya zo ya cinye, ya hana kowa. Ko da shekara ta zagayo, sai
Dodanniya ta zo bin bashi gidan Gizo. Bayan Dodanniya ta iso gidan sai Ƙoƙi ta ce gizo ya mutu. Har ta kama hanya za ta koma, sai
Kurciya ta ce ƙarya ne. Daga nan
sai suka koma gidan Gizo, ta fara waƙa tana cewa:
Kurciya:
Mabiyan bashin Gizo sun iso,
Mabiyan
bashin Gizo sun iso,
Zai
yi biyan bashi a kushewa.
Gizo:
Un uhun wai ya kurciya,
Ki
biyo ta gidan mu ki sha ruwa,
Ruwanki
na nan a kururrumi,
Bari
in fita in taɓa ‘yar rawa,
Bari in fita in taɓa ‘yar rawa.
Daga nan sai Gizo
ya fito, Dodanniya ta kama shi ta tafi da shi gidanta (Muhammad, 2014).
Wannan ya nuna mana muhimmancin gaskiya tare da horar da
al’umma cewa komi rintsi kada ka yi ƙarya, ka tsaya a kan gaskiyarka. Domin kuwa ko da ka yi ƙaryar, to fa ramin ƙarya ƙurarre ne. Shi ya
sa ko da Ƙoƙi ta yi ƙaryar
cewa Gizo ba ya nan, har Dodanniya ta juya za ta tafi, sai Kurciya ta tona
asiri ta hanyar yin waƙa shi kuma Gizo ya
amsa mata. Ke nan, ramin ƙaryar Gizo ya ƙure ne a daidai lokacin da raujin waƙa ya ɗebe shi ya manta an zo kama shi, ya amsa waƙar har Dodanniya ta kama shi.
4.5
Mutunta Ɗan’adam
Labaran baka na Bahaushe suna koya mana
sanin mutuncin ɗan’adam, ta yadda wasu labaran ke jaddada kada ka raina matsayin
mutum don halin da ka tsince shi. A kodayaushe ka mutunta mutum, ko ba komai ba
ka san baiwar da Allah ya yi masa ba wadda in aka yi dubi na tsanaki, ƙila yana da wani abin burgewa ko wani abin da kai ba ka da
shi. Mu dubi almarar Ɓeran Birni da Ɓeran Daji:
Ɓeran Birni da Ɓeran Daji
Wata
rana ɓeran birni ya tafi daji wurin ɓe ran daji. Ko da ya je sai ya ga abincin ɓeran daji daga harawa, sai dankali, sai ciyawa. Nan take sai
ɓeran birni ya kushe abincin, sai ya ce ɓeran daji shi ma ya zo birni don ya ga irin daɗin da yake ci. Watarana sai ɓeran daji ya tashi
ya tafi birni. Da isarsa sai ɓeran birni ya
tarbe shi, sai ga soyayyen nama, ɓeran daji zai ci
ke nan sai ɓeran birni ya hana
shi ya ce kar ka taɓa tarko ne, suka
wuce. Daga nan kuma, sai ga wani abincin har zai taɓa, ɓeran birni ya ce
wannan da magani in ka ci za ka mutu. Bayan wannan kuma suna cikin tattaunawa
kawai sai ɓeran birni ya ce
yi maza ka shiga rami ga mage nan, suka shige rami a guje. Ganin irin wannan
rayuwa mai cike da haɗari wadda ɓeran birni ke ciki, sai ɓeran daji ya ce: A
gaskiya raka ni in koma daji in cigaba da rayuwata a sake, ba irin wannan ba.
Da arziƙi da tashin
hankali, ai gwamma tsiya da kwanciyar rai, in ji ɓeran daji (Muhammad, 2014).
Wannan
almara ta nuna mana cewa duk halin da kake ciki ka fi wani, wanda kake ganin ya
fi ka. Shi ya sa ko da ɓeran birni ya raina abincin ɓeran ƙauye, ya gayyace shi zuwa birni domin ya ga irin abincin da ɓeran birnin
ke ci, da ya je kuwa sai ya ga cewa bayan tiya akwai wata cacar, domin kuwa
abincin ba ya ciwo cikin kwanciyar hankali. A kodayaushe yana cikin zullumin
tarko ko magani ko kuma mage. Haka wannan batun yake a zahiri, saboda haka
wannan ya sake jaddada cewa za a iya amfani da labaran baka wajen gina rayuwar
gobe, musamman gyara tunanin mutane a kan darajanta ɗan’adam a
kowane matsayi ka same shi.
A tunani
irin na wannan yanayi, ya sa hukumomi da dama sun sha yin kira a kan mutanen
karkara da su rage kwararowa zuwa birane, domin hangen dala ba shiga birni ba
ne. Ko ba komai kallon kitsen rogo da ake yi wa rayuwar birni ta fito fili a
cikin wannan almarar. Domin kuwa duk da
ɓeran
birni yana jin cewa shi yana cikin jin daɗi, yana cin abinci mai kyau fiye da na ɓeran ƙauye, amma ya rasa
kwanciyar hankali irin na ɓeran ƙauye.
5.0
Sakamakon Bincike
Labaran baka kamar kowane nau’i na adabi sukan kasance hoto ne da ke ɗauke da
kwatankwacin rayuwa ta jiya da yau da kintatar gobe. Suna ɗauke da
fasalce-fasalcen rayuwar al’umma tare da kuma nuna rayuwa mai kyau da maras
kyau. Wannan ne ya sa labaran baka suka kasance su ne ke inganta rayuwar ɗan’Adam,
har ya zama mutum. Tun da farko, wannan nazari ya ƙudiri aniyar gano
yadda adabin bakan Bahaushe musamman labarai kan kasance tamkar wata taskar
adana ilimin rayuwa ga al’ummar jiya da ma ta yau.
A cikin wannan nazari an fahimci cewa
labaran bakan Bahaushe wata makaranta ce wadda ke koya dabarun rayuwa ta hanyar
hani da horo cikin nishaɗi. A cikin nazarin an gano cewa akwai
abubuwa da dama waɗanda labaran suka ƙunsa waɗanda ke nuna rayuwar Bahaushe ta asali wanda ya shafi tarihinsa da
kimiyyarsa da fasaha da zamantakewa wanda ya shafi yanayin taamakon juna ta
hanyar aikin gayya da sauransu.
A cikin naazarin an riƙa yi ana kafa hujja da wasu labarai na baka waɗanda daga cikinsu
ne aka fito da waɗannan abubuwa ta hanyar bayani da fashin baƙin labaran.
Wani abin da nazarin ya gano kuma shi
ne, yadda labaran za su taimaka wurin gyarawa da daidaita rayuwar yau ta
la’akari da irin hikimomin rayuwar da aka kawo a cikinsu waɗanda in da
al’ummar yau za su ɗabbaƙa su cikin al’amuransu na yau da kullum a wannan
zamanin da an samu sauƙi a wasu lamura da dama.
6.0
Kammalawa
A wannan aikin, an yi ƙoƙarin fito da muhimmancin labaran baka
ne ga Bahaushen yau. Bayan shimfiɗa tare da ma’anar labari da labaran baka, an
kawo ire-iren labaran
bakan Bahaushe, inda aka ɗauki wasu daga
ciki aka yi bayaninsu daidai gwargwado domin fito da su fili a fahimce su. Daga nan sai aka fayyace yadda labaran suka kasance
taskar ilimi ta fuskokin tarihi da kimiyya da fasaha da falsafa da sana’o’i.
Daga bisani aka bayyana yadda labaran suke kasancewa hanyar gina rayuwar gobe, inda aka riƙa bayani ana kawo misalai daga labaran. A ƙarshe, an kawo sakamakon bincike sannan aka kammala nazarin tare da
manazarta.
Manazarta
Babajo, A.K (2018). Orature, Meaning, Nature and Forms. A Study
Guide. Kaduna-Nigera: Slimline
Communications Ltd.
Bunza, U. A. (2012). “Katsina Ɗakin Kara: Gudummawar Qasar Katsina Ga Samuwar Wasu Labaran Bakan Bahaushe. Takardar da aka gabatar a taron Ranar Katsinawa da Ɗaliban Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato ‘yan asalin Katsina suka shirya a babban Ɗakin ETF3 na mazaunin jami’ar na dindindin a ranar Assabar, 24 ga watan Nuwamba, 2012 da ƙarfe goma na safe.
Bunza, U. A. (2013). “Tarbiya a Cikin Adabin Hausa: Tsokaci
Daga Karin Magana. Cikin Malumfashi, I.A.M. (ed); Kada: Journal of Liberal Arts, Vol 7 No. 1. Kaduna-Nigeria: Faculty of Arts, Kaduna State University,
Kaduna.
Bunza,
U.A (2015). “Talife-Talifen Hausa a Zamanin Mulkin Mallaka: Sigoginsu Yanayinsu
Da Sigoginsu.” Kundin Digiri na Uku. Sakkwato: Sashen Nazarin Harsunan
Nijeriya, Jami’ar Usman Ɗanfodiyo.
Dunfawa, A.A. (2013). “Tunanin Bahaushe
Cikin Littafin Ruwan Bagaja”. Cikin Special
Research in Humanities. Katsina: Umaru
Musa Yar’adua University.
Ɗangambo, A. (2008). Rabe-Raben Adabin Hausa. Sabon Tsari.
Zaria : Amana Publishers.
Gusau, S.M (1995). Dabarun Nazarin
Hausa. Kaduna : Fisbas Media Services.
Gusau, S.M. (2006). “Tatsuniya (Gatana):Sigoginta da Hikimominta”.Cikin Mujallar Algaita,
Malumfashi, I. (2019) (ed). Labarin Hausa a Rubuce: 1927-2018. Zaria: Ahmadu Bello University
Press Limited.
Muhammad, M. S. (2014). “Rowa (Hali, Wayau, ko Ciwo?): Tsokaci a kan Ɗabi’ar Rowa a Rayuwar Bahaushe Jiya da Yau”. Takardar da Aka Gabatar a Taron Tallafa wa Marayu a Garin
Kudan a Zauren Taro (Town Hall) da ke Likoro Road Sabon Garin Kudan. Ranar
Asabar 5 ga Yuli 2014, 8 ga Ramadan da Ƙarfe 09:00 na Safe.
Muhammad, M. S. (2014). “Wayon Dabbobi a Ma’aunin Adabin Bahaushe Jiya da Yau”. Being a
Mandatory Ph.D Seminar Paper, Presented at the Department of Nigerian
Languages. Faculty of Arts and Islamic Studies Usmanu Ɗanfodiyo University Sokoto.
Muhammad, M. S. (2014). “Rikiɗa a Falsafar Bahaushe.”
Being a Mandatory PhD Seminar Paper, Presented at
the Department of Nigerian Languages. Faculty of Arts and Islamic Studies
Usmanu Ɗanfodiyo University
Sokoto.
Sabe, B. A. (2011). “Adabin Kasuwar Kano: Nazari Da Sharhi Game Da Ƙagaggun Labaran Hausa, 1984-2008”. Kundin Digiri Na Biyu. Sashen Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Sa’id, B. (2006) Ƙamusun Hausa. Zariya: Ahmadu Bello University Press
Yahaya I.Y. da
Wasu (1992). Darrusan Hausa Don
Manyan Makarantun Sakandire, Littafi na Uku.
Ibadan: University Press PLC.
Yahaya I.Y. (1971). Tatsunniyoyi da Wasanni. Ibadan: Oxford
University Press.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.