Ticker

Yaushe Ake Ketarar Siraɗi?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum, Yaa Sheik. Malam a wanne lokaci ne a ke shayar da ruwan Alkhausara Kafin Hisabi ne ko bayan Hisabi ? Yaushe ne a ke ketarar siraɗi? Kafin Hisabi ne ko bayan Hisabi? Allah saka ma Mallam da alkhairinSa.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam

Duka guda biyun bayan Hisabi ne.

Amma shi siraɗi ana ketara shi ne kafin a shiga aljanna, nassoshi sun nuna cewa, shi siraɗi gada ce akan Jahannama, kowa zai wuce gwargwadon nauyin aikinsa, wasu mutanan daga nan za su faɗa cikin wuta.

Shi kuwa Alkausara a zancen da yafi inganci sai bayan an shiga aljanna za a sha.

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana da tafki yana Kuma da Alkausara, abubuwa guda biyu ne mabambanta

Allah Ne Mafi Sani

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏��👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments