Zakkar Miliyan 6

    TAMBAYA (55)

    Slm. Ina wuni. Dan Allah Ina tambaya ne Akan wanda zaa iya nawa zakka. Uwa zata iya bawa yaranta? Nawa ne zakka da zaa cire wa miliyan shida.

    AMSA

    Waalaikumussalam, Warahmatullahi, Wabarakatuhum

    Nisabin Zakkah kamar yanda kwamitin ganin wata na kasa suka sanar, 3rd Muharram 1445H (21st July, 2023), cewar nisabin Zakkah ya fara ne daga N4,152,960

    Da farko mutum zai fara lissafa adadin zallar dukiyar da ya mallaka sai ya fitarda bashin da ake binsa sai ya fitarda abinda ya samu daganan sai ya fitar da kaso biyu da rabi cikin dari (2.5%)

    A sauqaqe mutum zai fitarda kaso daya a cikin arba'in (1/40) bi ma'ana idan idan kinada N40 to zaki fitarda N1 ne kacal

    Tunda anan kinyi magana ne akan N6,000,000 to za'a raba ta kamar yanda nayi bayani a sama (6,000,000 ÷ 40 = 150,000)

    Kenan haqqin Allah Azzawajallah a cikin mikiyan shida dincan shine N150,000 kacal. Allahu Akbar !

    Dangane da batun ya halatta mahaifiyarku ta baku Zakkah kuma, wannan kam saidai idan mutum ya kasance mabuqaci ne. Mabuqaci anan shine wanda samunsa bai kai Nisabi ba. Kada ya zamo a cikin iyalanka, kamar matar ka, yayanka, iyayenka da kakanninka

    Saidai a mazhabar shafi'iyya mace zata iya bawa mijinta Zakkah amman ya kasance mabuqaci

    Bayarda Zakkah yana daya daga cikin shiqa shiqan musulunci guda 5, kuma duk wanda ya bayar kamar ya bawa Allah rance ne, kamar yanda Allah SWT ya fada;

    ( مَّن ذَا الَّذِي يُقْرِضُ اللَّهَ قَرْضًا حَسَنًا فَيُضَاعِفَهُ لَهُ أَضْعَافًا كَثِيرَةً ۚ وَاللَّهُ يَقْبِضُ وَيَبْسُطُ وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ )

    البقرة (245) Al-Baqara

    Wãne ne wanda zai bai wa Allah rance, rance mai kyau, dõmin Ya riɓanya masa, riɓanyãwa mai yawa? Kuma Allah Shi ne ke damƙewa, kuma yana shimfiɗawa, kuma zuwa a gare Shi ake mayar da ku

    An karbo daga Abu Hurairah (RA), Annabi SAW yace: "Duk wanda ya bayarda sadaqa kwatankwacin dabino wanda ya samu da halal, saboda Allah SWT yana karbar abinda yake halal ne, Allah SWT zai karbi wannan sadaqa da hannunsa na dama ya kula da ita kamar yanda mutum zai dinga kula da karamin doki (wanda aka haifa ko kuma doki dan kasa da shekara daya), har sai wannan sadaqa ta koma kamar girman dutse"

    (Muttafaqun alaihi)

    Ka'ab ibn 'Ujrah (RA) yace, Annabi SAW yace: "...bayarda Zakkah yana kawar da munanan ayyuka kamar yanda ruwa yake kashe wuta"

    (At-Tirmidhi)

    Haka kuma Annabi SAW yace wadanda suke bada sadaqa a boye da ikhlasi ba da riya ba suna cikin mutane 7 dinnan wadanda Allah SWT zai sakasu a inuwarsu ta Al-arshi a ranar da babu wata inuwa sai ita

    (Muttafaqun alaihi)

    Wallahu taala aalam

    Amsawa;

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.