Ticker

6/recent/ticker-posts

A Sha Ruwan Tsuntsaye

5.8 A Sha RuwanTsuntsaye

Wannan ma wasayara maza ne. A ƙalla yara uku ne suke gudanar da shiYana jerin wasannin yara maza na motsa jiki.

5.8.1 Wuri Da LokacinWasa

i. An fi gudanar da wannan wasa a dandali.

ii. Akan gudanar da wannan wasa ne da dare.

5.8.2 Yadda Ake Wasa

Yara uku ne ke haɗuwa domin gudanar da wannan wasa. Biyu daga cikin yaran za su tsaya a layi, manne da jikin juna. Sannan za su sanya hannuwansu ta baya, su sarƙafa yatsunsu yadda za su iya tallafar nauyi. Yaro na ukun kuwa zai taka hannuwan nasu sannan ya dafa kafaɗunsu ya tsaya. Daga nan za su riƙa yawo da shi a daidai iyaka filin wasa da suka ƙayyade. Yaron zai riƙa ba da waƙa yayin da biyun za su riƙa amsawa. Waƙar kuwa ita ce:

Yaro: A sha ruwan tsuntsaye,

Yara: Daga sama.

Yaro: Ba daga saman ba,

Yara: Daga sama.

Yaro: Shuuur na ƙoshi,

Yara: Daga sama.

 

Bayan an kamala zagawa da wannan yaro, sai ya sauka. Wani kuma zai hau shi ma a zaga da shi. Haka za su ci gaba da yi har su gaji.

 

5.8.3 Tsokaci

Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments