TAMBAYA (65)❓
Assalamualaikum Warahamatullahi wabarakahtuhu MLM dan Allah
tanbaya nake ya ake istikara
AMSA❗
Waalaikumussalam, Warahmatullahi, Wabarakatuhum
Alhamdulillah.
Jabir Ibn Abdullah, Allah ya yarda da shi da mahaifinsa, ya ce;
Manzon Allah (SAW), tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance
yana koya mana yin istihara (neman zabin Allah) a Cikin dukkan al'amura kamar
yadda yake koya mana sura daga Cikin Alkur'ani, yakan ce, "Idan dayanku ya
yi niyyar yin wani al'amari to ya yi sallah raka'a biyu ba ta farilla ba,
sannan ya ce;
اَللَّهُمَّ
إِنِّي أَسْتَخِيرُكَ بِعِلْمِكَ، وَأسْتَقْدِرُكَ بِقُدْرَتِكَ، وَأَسْألُكَ مِنْ
فَضْلِكَ الْعَظِيم، فَإِنَّكَ تَقْدِرُ وَلا أَقْدِر، وَتَعْلَمُ وَلا أَعْلَم، وَأَنْتَ
عَلاّمُ الغُيوبِ، اللّهُمَّ إِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا اْلأَمْرَ- وَيُسَمِّي
حَاجَتَهُ - خَيْرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، عَاجِلِهِ وَأَجِلِهِ
فَاقْدُرْهُ لِي وَيَسِّرْهُ لِي ثُمَّ بَارِكْ لِي فِيهِ، وَإِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ
أَنَّ هَذَا اْلأَمْرَ شَرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، فَاصْرِفْهُ
وَاصْرِفْنِي عَنْهُ وَاقْدُرْ لِي الْخَيْرَ
حَيْثُ كَانَ ثُمَّ أَرْضِنِي بِهِ.
Allahumma innee astakheeruka bi'ilmik, wa-astaqdiruka
biqudratik, wa-as-aluka min fadlikal-'azeem, fa-innaka taqdiru wala aqdir,
wata'lamu wala a'lam ,wa-anta 'allamul ghuyoob, allahumma in kunta ta'lamu anna
hazal-amr (sai ka fadi buqatar taka) khayrun lee fee deenee wama'ashee
wa'akibati amree fakqurhu lee, wayassirhu lee, thumma barik lee feeh, wa-in
kunta ta'lamu anna hazal-amr (saika sake fadar buqatar taka) sharrun lee fee
deenee wama'ashee wa'aqibati amree fasrifhu 'annee wasrifnee 'anh, waqdur
liyal-khayra haythu kan, thumma ardinee bihi.
Ma'ana; Ya Allah! Ina neman zabinka domin iliminka, kuma ina
neman Ka ba ni iko domin Ikonka, kuma ina rokonka daga falalarka Mai girma;
domin Kai ne mai iko ni kuwa ba ni iko, kuma Kai ne Masani, ni kuwa ban sani
ba, kuma Kai ne masanin abubuwan fake. Ya Allah! Idan ka san cewa wannan
al'amari sai ya ambaci bukata tasa alheri ne gare ni a cikin addinina, da
rayuwata, da kuma karshen al'amarina a wata rayuwar; da magaggaucin ala'marina
da majinkircinsa Ka kaddara mini shi, kuma Ka saukake mini shi, sannan Ka
albarkance ni a cikin sa. Kuma idan Ka san wannan al'amari sharri ne gare ni a
cikin addinina, da rayuwata da karshen al'amarina a wata ruwayar; da
magaggaucin al'amarina da majinkircinsa – Ka kawar da shi daga gare ni, kuma
Ka kawar da ni daga gare shi, kuma Ka kaddara
mini alherin a duk inda yake, kuma Ka sanya ni in yarda da shi".
Duk wanda ya nemi zabin mahalicci, kuma ya yi shawara da
talikai muminai, kuma ya yi azama a Cikin lamarinsa, to ba zai yi nadama ba,
domin Allah madaukakin sarki Ya ce;
(وَشَاوِرْهُمْ فِي اْلأَمْرِ
فَإِذَا عَزَمْتَ فَتَوَكَّلْ عَلَى اللهِ)
(Washawirhum Fiyl Amri Fa'iza Azamta Fatawakkal Alallahi).
"Kuma ka shawarce su cikin lamarinka, idan kuma ka kuduri
aniya, to ka dogara ga Allah".
(Hisnul Muslim)
Sannan kuma bawai mafarki ake ba kamar yanda wasu mutanen suke
fada, saidai idan akwai alkhairi a cikin al'amarin zaka ga son abin yana qaruwa
kuma zuciyarka ta aminta da abin komai qanqantarsa amman idan akwai sharri a
tattare da lamarin, zakaji zuciyarka bata kwanta da abin ba komai girmansa
Wallahu ta'ala a'alam
Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta,
astaghfiruka wa'atubi ilayk
Amsawa;
Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.