Addu’ar Saduwa Da Sabuwar Amarya

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Dan Allah malam wacce addu'ar mutum zai karanta idan yayi sabon Aure ? Kuma wacce addu'ar zai karanta idan zai sadu da matarsa ?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahamtullahi Wabarkatuh

Idan mutum yayi sabon Aure anaso yaɗora hannunsa, akan goshin amaryarsa ya karanta

wannan addu'a kamar haka

اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ خَيْرَهَا وَخَيْرَ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهَا وَشَرِّ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ

FASSARA»»

Ya Allah ina roqonka Alkhairinta, da Alkhairin abinda ka dabi'antar da ita akansa. Sannan ina neman tsarinka daga sharrinta da sharrin abinda ka dabi'antar dashi akanta.

Addu'ar Saduwa da iyali kuma itace kamar haka

بِسْمِ اللَّهِ اللَّهُمَّ جَنِّبْنَا  الشَّيْطَانَ، وَجَنِّبِ الشَّيْطَانَ مَا رَزَقْتَنَا‏.‏

FASSARA»»

Da sunan Allah, Ya Allah ka nisantar da shaiɗan daga garemu, sannan ka nisantar da shaiɗan daga abinda ka azurtamu dashi.

Za'a karanta wannan addu'arne kafin afara

saduwar. Wannan addu’ar duk yayin da ka zo saduwa da matarka ana buqatarka da ka karanta ta, ita ma matar tana iya karantawa babu laifi.

Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam Yace duk wanda ya yi addu'a yayin Jima'i, idan Allah ya qaddara samun ɗa a lokacin saduwar (Jima’i), shaiɗan ba zai cutar shi ba da iznin Allah.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments