Alkunya/Lakabin "Moyi" A Sakkwato

    Masu Suna ko Alkunya ko Laƙabin "Moyi" na da yawa, musamman a Yankin Sakkwato inda ake hasashen daga nan ne ya soma tun a lokacin Jihadin Jaddada Addinin Musulunci da ya haifar da Daular Usmaniya.

    A cikin 'yayan/ɗiyan Amirul Muminina Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi wanda ya shugabanci Daular Usmaniya daga shekarar 1817 zuwa wafatinsa a shekarar 1837 akwai mai suna Muhammad da ake yi wa alkunya /laƙabi da "Moyi".
    Malam Muhammad Moyi ɗan Amirul Muminina Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio ya samu kansa a matsayin Sarki a wani garin Ribaɗi da ake kira Silame( Silame hedikwata ce ta Ƙaramar Hukumar Mulkin Silame a Jihar Sakkwato ta yanzu). Masu Jihadi ne suka ƙirƙiri Silame kusa da wurin nan da ake kira "Surame", wato Tsohuwar hedikwatar Sarki Muhammadu Kanta na Kabi, domin su samu wurin zaman dakon tayar da ƙayar bayan da ka iya tuzgowa daga masu adawa da Daula da ayyukan ta.
    Zaman sa Sarki a Silame da laƙabin Sarautar Sarkin Kabi( ya zuwa yau masu Sarautar Silame suna amfani da laƙabin Sarautar Sarkin Kabi ne) ba zai rasa nasaba da zaman Kabawa a wannan wuri ba.
    Bayan wafatin Sarkin Kabin Silame Malam Muhammad Moyi ɗan Amirul Muminina Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio an samu bayyanar wannan suna /alkunya /laƙabi na "Moyi" a wasu sassa dake ƙarƙashin ikon Cibiyar Daular Usmaniya, wato Sakkwato.
    Misali, a gidan Mai Alfarma Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio dake Dange an samu Muhammad Moyi, haka ma a gidan Sarkin Ƙayan Maradun, Malam Muhammadu Mu'alliyeɗi ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio dake Maradun a halin yanzu an samu Moyi wanda ya yi sarautar Sarkin Ƙayan Maradun daga shekarar 1923 zuwa 1928.
    Allah ya jiƙan magabatanmu da rahama, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.
    www.amsoshi.com
    Daga Taskar:
    Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
    Ɗanmadamin Birnin Magaji
    Imel: birninbagaji4040@gmail.com
    Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.