Ambassador MZ Anka Magajin Garin Anka

     

    Ambassador MZ Anka Magajin Garin Anka
    Allah SWT ya yi wa Ambassador MZ Anka, Magajin garin Anka, Jihar Zamfara rasuwa a Ranar Juma'a, 29/12/2023. Mai shekaru 81 a duniya, kafin rasuwar sa ya halarci Makarantar Middle ta Sakkwato (Nagarta College, Sokoto ta yanzu) da Jami'ar Ahmadu Bello, Zaria inda ya samu Digirin sa na farko. 

    Ya taÉ“a riÆ™e muÆ™aman Di'o(District Officer) a Æ™arÆ™ashin N'e(N. A /Native Authority), Jekadan Nijeriya a Libya da kuma Minista a lokacin mulkin Marigayi Janaral Sani Abacha. Shi ne ÆŠantakarar Mataimakin Gwamnan  Jam'iyyar GNPP  a Tsohuwar Jihar Sakkwato (Sokoto, Kebbi, Zamfara States) Dr. Bello Haliru Mohammed a ZaÉ“en Shekarar 1979 wanda Marigayi Alhaji Shehu Mohammed Kangiwa da Mataimakin sa Dr. Garba Nadama suka lashe. Shi ne ÆŠantakarar Gwamnan Jam'iyyar PDP na Jihar Zamfara a zaÉ“en shekarar 1999 wanda Alhaji Ahmed Sani Yariman Bakura na Jam'iyyar APP ya lashe. Ya bar matan aure 2, 'yaya/É—iya 13, Maza 7, Mata 6 da jikoki da dama. Allah ya jiÆ™an sa da rahama, amin. Ibrahim Muhammad ÆŠanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara.

    Daga Taskar:
    Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
    ÆŠanmadamin Birnin Magaji
    Imel: birninbagaji4040@gmail.com
    Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.