Amsa Sallamar Kafiri

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Idan wanda ba musulmi ba ya ce wa musulmi: ‘As-Salaamu Alaikum Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuhu’, wace amsa zai ba shi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Sahihiyar magana a wurin malamai ita ce: Sai ya amsa masa da cewa: ‘Wa Alaikumus-Salaamu Alaikum Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuhu’.

MEYASA?

Saboda maganar Ubangiji Maɗaukakin Sarki

وَإِذَا حُيِّيتُم بِتَحِيَّةٍ فَحَيُّوا بِأَحْسَنَ مِنْهَآ أَوْ رُدُّوهَا

Idan kuma aka gaishe ku da wata gaisuwa, to sai ku yi gaisuwa da wacce ta fi ta, ko kuma ku mayar da irin ta. (Surah An-Nisaa’i: 86)

A nan bai bambanta a tsakanin mai yin gaisuwar farko gare mu ba: Babba ne ko yaro ne, namiji ne ko mace ce, mun san shi ko ba mu san shi ba, kuma musulmi ne ko wanda ba musulmi ba ne. ‘Idan kuma aka gaishe ku…’ kawai ya ce!

Amma idan ya fahimci cewa akwai manufa ta isgili ko shegantaka a cikin gaisuwar, to a nan ne sai ya amsa masa da: ‘Alaikum’ ko ‘Wa Alaikum’.

Haka Hadisin Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya nuna

« إِنَّ الْيَهُودَ إِذَا سَلَّمُوا عَلَيْكُمْ يَقُولُ أَحَدُهُمُ السَّامُ عَلَيْكُمْ فَقُلْ عَلَيْكَ »

Su Yahudawa idan suka zo yi muku sallama ɗayansu cewa yake yi: As-Saamu Alaikum (watau: mutuwa a kan ku). To, sai ka ce: Alaika (watau: A kan ka). (Sahih Muslim: 5782).

Ta yaya ma wanda ba musulmi ba zai gaishe ka da gaisuwar da asalinta daga Allaah ta ke, daddaɗar gaisuwa mai albarka, wacce ke ɗauke da addu’ar tabbatar da samun Aminci da Rahamar Allaah da Albarkarsa gare ka, kai kuma sai ka ƙi saka masa! Alhali kuwa ga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) yana cewa

« وَمَنْ صَنَعَ إِلَيْكُمْ مَعْرُوفًا فَكَافِئُوهُ فَإِنْ لَمْ تَجِدُوا مَا تُكَافِئُونَهُ فَادْعُوا لَهُ حَتَّى تَرَوْا أَنَّكُمْ قَدْ كَافَأْتُمُوهُ ».

Kuma duk wanda ya yi muku alkhairi to ku saka masa. Idan kuma ba ku samu abin da za ku saka masa ba, sai ku yi ta yi masa addu’a har sai kun ga cewa, lallai kam kun saka masa. (Sahih Abi-Daawud: 1469; As-Saheehah: 254)

Allaah ya ƙare mu da ilimi mai amfani.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Tambayad Abdullaah assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅��𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments