Argungu

    Argungu
    "Argungu gungun Nabame.." 
    Inji MakaÉ—a Gero Zartu Argungu. Wannan  wani É“angaren bikin kamun kifi ne da ake gudanarwa na shekara - shekara a garin Argungu hedikwatar Masarautar Kabawa, na Shekarar 1980 ne.

    Argungu... /Sarkin Kabi Yakubu Nabame ne(wanda ya yi Sarauta daga shekarar 1849 zuwa shekarar 1854) ya ƙirƙiri Argungu a matsayin sabuwar hedikwatar Kabawa/Daular Kabi wadda Malam Muhammadu Kanta ya samar tun a shekarar 1515, bayan sun rasa Birnin Kabi/Birnin Kebbi da ake yi wa laƙabi da Takalafiya a Yaƙin da suka gwabza tsakanin su da masu jihadin jaddada Addinin Musulunci na Daular Usmaniya.

    An fara wannan biki na kamun kifi da wasannin al'adun gargajiya na Kabawa a Argungu a shekarar 1934 a lokacin mulkin Sarkin Kabi Muhammadu Sani wanda ya yi Sarauta daga shekarar 1934 zuwa shekarar 1942. Shi ne Mahaifin Sarkin Kabi Muhammadu Mera wanda ya yi Sarauta daga shekarar 1959 zuwa shekarar 1996. Sarki Muhammadu Mera shi ne Mahaifin Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu na yanzu, Alhaji Sama'ila Muhammad Mera CON wanda ke sarauta daga shekarar 1996 ya zuwa yau.

    Dalilin fara wannan biki shi ne wata ziyarar aiki da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Hassan ɗan Mu'azu (1931-1937/38) ya samu damar kaiwa a Masarautar Argungu bayan dukan yunkurin da waɗan da ya gada suka yi na neman kyautata taren Sakkwato da Kabawa/Argungu saboda rashin jituwar dake tsakanin su ta tun lokacin yaƙe - yaƙe ya ci tura. Allah cikin ikon shi, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Hassan ɗan Mu'azu ya nemi amincewar Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu Muhammadu Sani cewa ya na son ya kawo mashi ziyara a Argungu. Bayan ya amince ne, sai kuma ya shirya mashi wannan biki wanda ya zamo al'ada a kusan kowace shekara tun daga wannan ziyarar ta shekerar 1934. Allah SWT ya jiƙan magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.