Ticker

Barkwanci

Barkwanci...

Duk budurwa mai yaudara, Allah ya sa ta manta kayan sallarta a kekenapep. 🛺🛺
Barkwanci
Barkwanci...

An yi wa wani gwauro faɗa, ya yi zuciya. Aka ba shi kunu ya ƙi sha. A gabansa aka ƙara wa kunun ruwa aka ba wa awaki. 🦌🐐

Barkwanci
Barkwanci...

A Sakkwato da Kebbi da Zamfara aka azumu alaji!
Tun ƙarhe goma na swahe za ka hwara jin ana zwazwahat cikinka. Ko da azzuhur ka yi an yashe komi. Kahin a ce La'asar ka ida zukkucewa! 😴

Barkwanci

Barkwanci...

Farar mace lantarkin gida. 💡Baƙar mace mai jawo sauro. 🦟
Barkwanci
Barkwanci...

Ba auren baƙar mace ba, sai an ɗauke wuta ka rasa ina take. 🌚
Barkwanci

Barkwanci...

Ni fa Indomie ba ta mini daɗi. Sai in ji wani tsami-tsami da kanwa-kanwa. Na fi son taliyar Hausa ko ɗanwake.
Barkwanci

Barkwanci...

Ni masoyin al'ada ne. Ba abin da zai haɗa ni da Indomie. 😴
Barkwanci

Barkwanci...

Zan je in faɗa wa matata cewa, likita ya ce sanya sikari a kunu ko shayi na janyo ciwon sanyi. 👨‍🦯💡
Barkwanci

Barkwanci...
Wani ɗan Arewa ya je neman aure. Da baban yarinyar ya tambaye shi mene ne sana'arsa, sai ya ce ya gama makaranta yanzu yana ɗan buge-buge.
Sai baban yarinyar nan ya ce: "To ɗan matsa kar ka buge ni." 😂
Barkwanci

Barkwanci...

Wani abu sai azumi. Kafin a sha ruwa, wahalar irin ta talakawa ce. Bayan an sha ruwa, wahalar sai ta koma irin ta masu juna biyu.🤰🫃🫄
Barkwanci

Barkwanci...
Ba za ka taɓa jin kamfanin bisko (biscuits) suna kuka da tashin dala ba, sai dai kawai su cire guda biyu ko uku a wuce wurin.👨‍🦯👨‍🦯
Barkwanci

Post a Comment

0 Comments