Takardar ƙara wa juna sani da aka gabatar a ajin ALH 400: Seminars, a Sashen Nazarin Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau, Nijeriya, (2022/2023 Academic Session).
Dan Kwarai A Tunanin Bahaushe
NA
MANSUR USMAN
ADMISSION NUMBER: 1810104009
GMAIL: ababiyo@gmail.com
TSAKURE
wannan aiki da na gabatar,
mai suna dankwarai a tunanin bahaushe, aiki ne akan yadda bahaushe yake kallon
wau kyawawan dabi’u da idan mutum ya siffantu dasu das hi ake kirannsa da
dankwarai, kuma a cikin wannan aike na a ka fitar da wadannan kyawawan dabi’un
da akan sami dankwarai das u.
GABATARWA
wannan aiki zai yi Magana a
kan daya daga cikin nau’oin adabi ne, kamar yadda aka sani ne cewa akwai
nau’oin adabi guda uku, watau wakada zube da kuma wasan kwaikwayo. wannan aiki
zai ta’allaka akan zube, abun da kuma za’ayi nazarinsa shi ne ‘Dankwarai a
tunanin Bahaushe’.
A cikin wannan aiki zamu
kalli ma’anar Dankwarai a tunanin bahaushe, sannan kuma wannan aiki zai bayyana
dalilin bincike da mahimmancin bincike da kuma manufarsa da kuma gundarin
bincike da kuma hanyoyin da akabi wajen gudanar da aikin, sai kuma nadewa da
manazarta.
DANKWARI
Ana
kallon mutun dankwarai ne tayin la’akari da halayen sa. akan dubi halaye na
kirki na kwarai wadan dab a haka kawai ake samunsu ba, kuma ba kawai kara zube
suke ba. Baya yiwuwa ayi Magana kan kowane mutumen kirki ba tare da an fito an
baiyyana halayen da in mutun yana dasu ya isa yazama mutumen kwarai. A Hausa,
mutum yana zama dan kwaraine idan yasamu tarbiyar jiki da hali. A Hausa hali
shi yafi komi ga mutum. hakan tasa hausawa kance ‘halin mutum jarinsa’.
Adamu (2000:8-9) ya bayyana
cewa shahararren masaninnan Kirk Green, (1973) ya gabatar da wata takarda a
taron da akayi don tunawa da wani shahararren masani mai suna Hans wolf, wanda
yaama suna ‘mutumen kirki’ (The Concept Of Good Man In Hausa) acikin wannan
mukala, marubucin yayi bayani daya bayan daya akan halayen mutumen kirki a
hausa. Halayen kuwa sun hada da amana, aminci, da yadda, da karama, da hakuri,
da hankali, da kunya, da ladabi, da mutunci, da hikima, da kuma adalci.
Haka kuma Habib da Usman Musa
da Zaruk, (1982) sunyi karin bayani akan tarbiyar bahaushe, a inda suka kawo
ire iren tarbiyar hausawa har guda goma sha biyu, wadan da suka hada da
mu’amala da zumunta da rikon addini da gaskiya da dattako da adalci da kawaici
da rashin tsegumi da kama sana’a da juriya da jarunta. Don haka a dunkule dan
kwarai shi ne mutumen kirki, kuma mutumen kirke shi ne dan kwarai, dole sai
mutun ya siffantu da irin wayannan dabi’u da aka lissafo yake zama dan kwarai,
duk da dai ance mutun dan tara ne bai cika goma ba, to amma idon ya mallaki
kaso mai yawa daga cikin jerin dabi’un da aka zayyano ya iya zama mutumen kirki
watau dan kwarai.
1.0.2 TUNIN BAHAUSHE
Masana da manazarta da dama musamman ma dai
masana a kan yana yin halayyar dan Adam sunyi ta gwaro suna kai mari a
kokarinsu na bayyana ma’anar Kalmar falsafa ko tunani.
Isah, z. (2006), ta bayyana Kalmar tunani da
cewa Kalmar tunani tasamo asali ne daga ‘tuno’ wato dauko wani abu da aka adana
a kwakwalwa adawo dashi kusa da zuciya don ayi amfani dashi. Tunani kuma kan
iya daukar ma’anar dawo da abinda aka sani domin a tunkari abin da ake
fuskanta, ta kara da cewa ‘a wajen tunani abubuwa biyu ne ake aiki da su, akwai
kwakwalwa da kuma zuciya. zuciya ita ce take kawo abin a kwakwalwa kuma ta
taskace shi, har wayau ta kara da cewa idan aka fadada ma’anar tunani tana iya
daukar ma’anar akidar al’umma yadda suke kallon wani abu watau amfani da sani
wajen auna al’amurran da ke faruwa na yau da kullun.
Bergery (1993) ya bayyana ma’anar tunani da
cewa, kawo abin da ya gabata, wato maido da sura ta wani abu da ya wuce ko kuma
hasashe a kan wani abin da ya gabata ko zai zo. ya kuma sake bada ma’anar da
cewa “ wata manufa ce da aka auna bayan zurfafa bincike ta hanyar amfani da
kwakwalwa yadda hankali zai dauka.
Horneby, (2000) ya bayyana
Kalmar tunani da ‘cewa wata manufa ce ko ra’ayi da ake samu daga kwakwalwar dan
Adam” ya kuma sake bayyana tunani da cewa “Hanya ce ta sarrafa abubuwan da za a
iya nazarin su ta yin amfani da kwakwalwa sannan ya kara da cewa “ tunani na
nufin mayar da hankali kan wani abu don a nazarce shi.
kakangi, (2006) yace tunani taska ce da
Al’ummar Hausawa kan adana ire-iren dabi’unsu walau kyawawa ko akasin su.
1.0.3 DALILIN BINCIKE
kamar ko wane irin aiki da aka gudanar, a kan
yi shi ne domin zakulo wasu muhimman abubuwa da ta yi yuwa ba’a sani ba da
farko ko kuma an sani amma ba a tara shi ba kuma ba’a tsara ba domin masu
nazari, Hausawa na cewa “Banza ba ta kai zomo kasuwa” wannan maganar tayi dai
dai da nufina na yin wanna aiki. shi ya sa na dage damtse da nufin nazarin akan
wannan batu mai take da Dankwarai tunani Bahaushe.
Malaman falsafa da dama irin su Socrates da
plato da Dewey, da Aristotle da sauran su, sunyi rubuce rubuce wadan da suka
jibinci al’amura na duniya da dama, to, sai naga cewa in dai falsafa ta shafi
al’ada da dabi’un kowace al’umma, ken an akwai muhimmanci idan aka fito da
kyawawan dabi’un da ake samun dankwarai da su.
Dalilin na yin wannan bincike
shi ne, mana yadda kowa yake fatan samun Dan kwarai a cikin zuriyyarsa naga ya
dace a rika yiwa dalibbai matashiya kasancewar su manya gobe, don haka naga
yana da kyau su kara fahimtar wadannan dabi’un domin amfaninsu, sanan kuma su
san irin sakamakon da ake samu idanmutum ya zama dankwarai a rayuwa.
Wani dalilin bincike shi ne, ganin yadda
mutane suka ginu a kan wadannan dabi’u wato suka rike wadannan kyawawan dabi’u
sai na lura da cewa yanzu kuma a wannan zamani an rage aiki da wadannan dabi’u
don haka naga yana da kyau a kara zaburar da Haussawa a kan riko da wadannan
kyawawan dabi’un domin su zama na kwarai domin bahaushe. Na cewa “kowane
tsuntsu kukan gidansu ya keji”.
1.0.4 MANUFAR BINCIKE
A kowane bincike mutum ya yi nufin yin wani
abu, to lallai babu shakka yana da manufar sa ta yin wannan abu. Kamar yadda
Hausawa suka ce” kowane aiki da nasa manufa ta yin sa saboda haka babu wani
bincike da zai faru ba tare da wata manufa ba.
Babar manufar wannan bincike shi ne kokarin
gano kyawawan dabi’un da ke kunshe a cikin rayuwar Bahaushe, da kuma bayyanar
da wadannan kyawawan dabi’un ga alumma, domin kuwa ta kyawawan dabi’un ne ake
samun dan kwarai wani Karin manufa ta yin wannan bincike. Shi ne, domin in susa
ma Hausawa ra’ayin a kan su rike wadannan kyawawan dabi’un hannu bibbiyu ka da
su yi ma su rikon sakainar kashi don ganin yadda suke da amfani matuka.
1.0.5. MUHIMMANCIN BINCIKE
Masu iya Magana na cewa “don lada ake yin
salla” ma’ana kowa ne abu yana da fa’idar da za’a samu daga gareshi, haka abin
yake ta fuskar wannan bincike. Babu shakka, wannan bincike zai amfanar da
al’umma musamman ta bangaren Adabi, domin za’afito da irin sakonnin da kyawawan
dabi’u suke da su. Domin ta haka mutane / al’umma zasu kara fahimtar
muhimmancin wadannan kyawawan dabi’u na Hausawa wanda da su ne mutum yake zama
dan kwarai.
1.0.6. FARFAJIYAR BINCIKE
Kamar yadda taken wannan makala ya nuna wato
dankwarai a tunanin Bahaushe. Don haka wannan bincike zai ta’allaka ne a kan
rubutun zube. daga abubuwan da na samo daga kyawawan Dabi’un Hausawa.
1.0.7. HANYOYIN BINCIKE
Yana da wuya ayi binciken irin wannan don
amfanin al’umma da kuma dalibai masu nazarin hausa ba tare da anbi wasu
muhimman hanyoyi ba, babu shakka dukkan wanda ya yi aniyar tafiya, to dole ne
ya bi hanyar da zata kai shi inda zashi, haka ma dai alamarin yake dangane da
wannan bincike. Dakin karatu mallakar jaha na ciki daga hanyoyin da aka bi
wajen bincike littafai wajen gudanar da wannan bincike da wasu kundayen digiri.
Wata hanyar da aka bi wajen
gudanar da wannan bincike shi ne, wasu littatafai da malamai masana suka rubuta
a kan wannan fannin na falsafa (Tunani) da ya shafi dabi’un dan kwarai.
1.0.8. SHAWARWARI
Rayuwa ta kwarai a tunanin Bahaushe ta kunshi
hankali da tunani, shi hankali shi ke tallafawa tunani wajen dora al’umma a
turba ta kwarai, a duk inda aka rasa hankali to tunani ba zai zo ba.
1.0.9. NADEWA
Tun farko an yi shimfida ne wadda ta ke kunshe
da ma’anar dankwarai da ma’anar tunani, sanan sai aka bayyana dalilin bincike
da manufar bincike da muhimmancin bincike da hanyoyin bincike da dai sauran su.
MANAZARTA
Adamu A.U (2000) “Tarbiyar
Bahaushe, mutumin kirki and Hausa prose fiction, toward an analytical
framework” seminer presentation department of English and elopement language
Beyero University, Kano.
Abubakar A (1994) “Tunanin
Bahaushe game da duniyar adabin baka kundin bincike don neman digiri nafarko,
sashen Harsuna da Al’adun Afrika, jami’ar Ahmadu Bello university, Zaria.
M.L (2002) the Hausa
metaphysical worldview poramiological exposition’ Phd. Thesis submitted to the
Department of Nigeria and African languages, Ahmadu Bello University, Zaria.
Kirk green, amk (1973) mutuminkirki! The concept
of good man in Hausa’ (Hans Wef Memorial Lecture) Bloomington Indiana. African
studies program.
Oxford (1948) oxford advanced
leaner Dictionary, oxford University, press.
Ibrahim Y.Y, Da wasu, (2006)
Darussan Hausa don Manyan Makaratun sakandare littafina uku. University press
Plc Ibadan.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.