Ticker

Dillancin Hotunan 'Yan Mata

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam menene hukuncin 'yan matan da suke bada hotunansu ga tsofaffi don su nema musu mijin aure ?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Addinin musulunci ya haramta kallo zuwa ga matar da ba muharrama ba, sai in akwai larura, amma ya halatta ka kalli mace idan kana so ka aure ta, kamar yadda yazo a cikin hadisi inda Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yake cewa "Idan dayanku yana neman aure, to in ya sami damar kallon abin da zai kira shi zuwa aurenta, to ya aikata hakan" ABU DAWUD. Malamai sun yi saɓani akan wurin da ya kamata mutum ya kalla a jikin mace lokacin da yaje neman aure

1. Akwai waɗanda suka ce zai kalli fuska da tafin hannu ne kawai.

2. Zai kalleta a kayan da take sawa a cikin gida, ta fuskance shi ya kalle ta, sannan ta juya baya ya kalleta. Wannan ra'ayin shine yafi dacewa, saboda ta haka mutum zai san yanayin matar da zai aura.

Bisa abin da ya gabata, za mu iya fahimtar cewa aikin dalilin aure ya hallata, amma da sharuda. Ga wasu daga ciki

1. Ya zama hoton ya fito da asalin fuskar matar, bai kwarzanta ta ba, ta yadda za'a iya yaudarar namijin, ko a ruɗe shi.

2. Ya zama wacce za'a bawa hoton mai amana ce, ta yadda ba za ta nunawa wanda ba shi da nufin aure ba, saboda asali ya haramta ayi kallo zuwa ga matar da ba muharrama ba, sai in

akwai larura, sai ga wanda yake nufin aurenta. Wannan yana nuna cewa, bai halatta asa irin wannan hoton na neman aure ba a Facebook ko a jarida.

3. Kada hoton ya ƙunshi fito da tsaraici, ya wajaba a tsaya a iya inda shari'a ta bada umarni.

4. Zai fi dacewa ace mace ce za ta yi dalilin aure, saboda idan namiji ne, zai iya fitinuwa da hotunan da yake gani, sai ɓarna ta auku, don haka ita ma macen ya wajaba taji tsoron Allah a cikin aikinta.

Allah shi ne mafi sani.

Amsa daga Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments