Farfesun Kaza, Soyayyiyar Kaza Da Kayan Lambu, Gasasshiyar Kaza, Soyayyiyar Kaza Da Nama, Farfesun Kifi Da Kayan Lambu, Soyayyiyar Fara

    Wannan rubutu ya kawo bayani game da yadda ake Farfesun Kaza, Soyayyiyar Kaza Da Kayan Lambu, Gasasshiyar Kaza, Soyayyiyar Kaza Da Nama, Farfesun Kifi Da Kayan Lambu, Soyayyiyar Fara. Ku turo mana sharhi ko tambayoyi a sashen comment da ke ƙasa.

    Farfesun Kayan Ciki

    a. Albasa

    b. Gishiri

    c. Kayan ciki

    d. Kayan yaji

    e. Magi

    f. Mai

    g. Ruwa

    h. Tafarnuwa

    i. Tarugu

    j. Tattasai

    k. Zogale

    Za a wanke  nama, sannan a tafasa tare da albasa  da kayan da kayan É—anÉ—ano da kayan yaji. Bayan ya tafasa, idan akwai sauran ruwa cikin tukunyar akan zubar da shi. A gefe guda kuwa za a yi jajjagen tarugu da tattasai da albasa, sannan a soya su sama-sama tare da kayan yaji. Idan waÉ—annan sun samu, sai a yi sanwa da É—an ruwa kaÉ—an ba mai yawa ba. Bayan ruwan ya tafasa, sai a sanya wannan  jajjage da nama ciki. Sannan sai a wanke zogale  É—an daidai ba mai yawa ba a sanya ciki. Haka za a bar su su Æ™arasa nuna tare.

    Soyayyiyar Kaza Tare Da Kayan Lambu

    i. Albasa

    ii. Gishiri

    iii. Kabeji

    iv. Karas

    v. Kayan yaji

    vi. Kaza

    vii. Kori

    viii. Kukumba

    ix. Magi

    x. Mai

    xi. Ruwa

    xii. Tarugu

    xiii. Tattasai

    Yadda ake soyayyen nama, haka ake sarrafa wannan  nau’in nama na soyayyiyar kaza da kayan lambu. Bambancin kawai shi ne, a nan akan sanya kayan lambu iri-iri kamar yadda aka bayyana a sama.

    Gasasshiyar Kaza

    i. Attarugu

    ii. Gishiri

    iii. Kaza

    iv. Kori

    v. Magi

    vi. Mai

    vii. Ruwa

    viii. Tafarnuwa

    Bayan an yanka kaza an fige an wanke , za a tsaga ta ta Æ™asa ko sama daidai yadda za a iya cire kayan cikin (ba tare da an feÉ—e ba). Daga nan sai a sake wanke ta sarai. A gefe guda kuwa, za a jajjaga kayan lambu sannan a soya su sama-sama. Za a sanya wannan  jajjagen da aka soya cikin kazar. Wajenta kuwa za a shafe shi da magi wanda aka É—an kwaÉ“a. Yawanci akan yi amfani da zare domin a É—aure wurin da aka tsaga domin fitar da kayan ciki (wanda kuma ta nan ne aka sanya jajjagen da aka soya). Daga nan za a tura cikin obun. Idan ba obun kuwa, sai a ayi amfani da madambaci.

    Gasasheyar Kaza Banƙarara

    i. Barkono (tonka)

    ii. Gishiri

    iii. Kayan yaji

    iv. Kaza

    v. Magi

    vi. Mai

    vii. Ruwa

    viii. Tafarnuwa

    Yadda ake sarrafa wannan  nau’i na nama na matuÆ™ar kama da yadda ake tsire na kan tukuba. A nan bayan an gyara kaza, akan feÉ—e ta a banÆ™are sannan a tsire da tsinke. Haka a banÆ™are za a ajiye ta gefen wuta . Zafin wutan ne zai gasa ta har ta dawo kamar an soya.

    Soyayyar Kaza Da Nama

    i. Albasa

    ii. Dankalin Turwa

    iii. Gishiri

    iv. Kabeji

    v. Karas

    vi. Kaza

    vii. Magi

    viii. Mai

    ix. Nama

    x. Ruwa

    Wannan nau’in sarrafa nama daidai yake da sauran nau’o’in suyar nama. Bambancin kawai shi ne, a nan ana haÉ—a naman sa ne ko na rago (ko makamancin waÉ— annan) da na kaza.

    Farfesun Kifi da Kayan Lambu

    a. Albasa

    b. Citta

    c. Kayan miya

    d. Kifi

    e. Koren tattasai

    f. Mai

    g. Ruwa

    h. Tafarnuwa

    Za a yi amfani da lemon tsami  ko É—oÉ—oya domin a wanke  kifi, sai a sanya shi domin ya tsane. A gefe guda kuwa, za a jajjaga tattasai da tarugu da albasa  a soya sama-sama (za a iya amfani da su ba tare da an soya ba). Bayan waÉ— annan sun samu, sai a tanadi kayan yaji. Sannan sai a goge karas a kuma yayyanka koren tattasai.

    Bayan waÉ—annan duka sun samu, za a É—ora sanwa da ruwa kaÉ—an, daidai adadin kifin da ake da shi. Bayan ruwan ya tafasa, sai a sanya wannan  kifi. Da zarar ya fara jin wuta , sai a saka jajjagen da aka tanada da kuma karas da koren tattasai.

    Soyayyan Kifi Da Soyayyiyar Miya

    i. Albasa

    ii. Gishiri

    iii. Kifi

    iv. Magi

    v.   Ruwa

    vi. Tarugu

    vii. Tattasi

    viii. Zogale

    Za a wanke  kifi sannan a soya shi tare da magi da albasa . A gefe guda za a jajjaga tattasai da tarugu sannan a soya su. Za a sanya kayan yaji yayin soyawar, sannan kuma za a watsa zogale  a cikin wannan  soyayyen jajjagen.

    Soyayyiyar Fara

    i. Albasa

    ii. Barkono (tonka)

    iii. Fara

    iv. Gishiri

    v. HaÉ—aÉ—É—en Yaji

    vi. Magi

    vii. Mai

    Za a gyara fara sarai a cire gashin da ke jiki, sai kuma a tafasa ta. Bayan ta tafasa sai a zubar da wannan  tafasasshen ruwan. Za a ajiye wannan fara ta sha iska har sai ta fara bushewa. Daga nan za a cire cinya da fiffike a jiye su daban. A gefe guda kuma za a tanadi kayan yaji. Za a iya sanya waÉ—annan kayan yajin kafin a soya ta. Za kuma a iya ajiye kayan yajin har sai an kammala soyawa kafin a saka.

     

    Citation (Manazartar Littafin):  Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

    Get a copy:
    To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
    +2348133529736

    You can also write an email to:

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.