Shimfiɗa
An gina babi na takwas sukutum a kan nau’o’in faten gargajiya da yadda ake sarrafa su. Dukkanin nau’ukan faten da aka lissafa a babin na takwas akan same su a zamanance. Duk da haka, akwai sauye-sauye dangane da yadda ake sarrafawa da kuma kayan haɗin da ake amfani da su. Wannan babi zai mayar da hankali kan nau’o’in faten da suka samu a dalilan sauyawar zamani.
Faten Kabewa
a. Alayyafu
b. Gishiri
c. Kabewa
d. Kayan miya
e. Kayan ƙamshi
f. Magi
g. Mai
h. Nama
i. Ruwa
A tafasa nama da kayan ƙamshi, idan ya dafu sai a sauƙe a aje gefe guda.
Daga nan,
za a jajjaga tattasai da tumatur da albasa da tarugu a sa mai ga tukunya a soya kayan su soyu. Sanan a zuba ruwa tare
da tafasasshen nama da
sauran ruwan naman,
idan ya tafasa, sai a
yanka kabewa kamar yankan dankali, a wanke a zuba a ciki a sa magi da ajino da kayan ƙamshi. Idan kabewar ta nuna, za a yanka alayyafu a zuba a ciki, sai kuma a rage wutar sosai har ya dafu da ɗan ruwa-ruwansa.
Naɗewa
Fate abinci ne mai mutuƙar muhimmanci daga cikin abincin Hausawa. Wannan ya sa suka ɗauke shi ɗaya daga cikin abincin da ake yi musamman da rana. Baya ga wannan, abinci ne mai sauƙin aiwatarwa da bai cika ɗaukar lokaci ba a yayin dafa shi; sannan ya kasance abin marmari ga mutane da dama. Wannan ya nuna Hausawa suna da dabaru a ɓangaren sarrafa abincinsu na gargajiya har ma da na zamani.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.