TAMBAYA (57)❓
Sai kuma Addu ar da akewa yaro idan yana firgita acikin
bacci
AMSA❗
Wanda ya Razana a cikin barci, Da wanda Ya Kasa Barci zai
ce;
أَعُوذُ
بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّاتِ مِنْ غَضَبِهِ وَعِقَابِهِ، وَشَرِّ عِبَادِهِ وَمِنْ
هَمَزَاتِ الشَّيَاطِينِ وَأَنْ يَحْضُرُونَ.
A'oozu bikalimatil-lahit-tammat min ghadabih,wa'iqabih,
washarri 'ibadih, wamin hamazatish-shayateen, wa-an yahduroon.
Ma'ana: Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga
fushinsa, da ukubarsa, da sharrin bayinsa, da kuma wasuwasin shaidanu, da kuma
kada su zo mini (a cikin al'amurana)
(Hisnul Muslim)
Idan kuma jaririyarki zaki yiwa to kinga anan maimakon kice
"A'oozu..." sai ki ce "O'eezuki..."
Sannan kuma ki dinga karanta mata "Mu'awwidatayn"
(Falaqi da Nasi), da safe da yamma
Kamar yanda ya tabbata a cikin Sahihul Bukhari hadisi mai
lambata 5748
Wallahu ta'ala aalam
Subhanakallahumma, wabi hamdika, ash-hadu anla'ilaha illa
anta, astaghfiruka, wa'atubi ilayk
Amsawa;
Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/G5NSbo2TyHMD6bcoEfds5E
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.