Ticker

    Loading......

Firimiyan Jihar Arewa Na Farko Kuma Na Karshe, Sir Ahmadu Bello, GCON, KBE Sardaunan Sakkwato

Jagora:
Tambari a jika sama'u na Bello,
Gudu ɗan yaro ga Giwa nan,

Y/Amshi :
Ko yaro ya san wari nai,

Jagora /Y/Amshi :
Ta tabbata ko yaro ya san wari nai,

Jagora:
Sai yaƙ ƙi gudu don gudun jahadi,

Y/Amshi :
Ko Baban ka shahada,
Ibirafin ko Baban ka shahada....
Nan Giginya,
Ko Baban ka shahada yay yi,
Ya wuce reni ba a yi mai shi..

Waɗan nan ☝️☝️☝️☝️wasu kalmomi ne da Marigayi Mai Turu Ƙanen Makaɗa Kurna, Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun, Mawaƙin Marigayi Mai Girma Firimiyan Jihar Arewa Na Farko kuma na ƙarshe, Sir Ahmadu Bello, GCON, KBE Sardaunan Sakkwato ya tsara a cikin wannan Waƙar mai amshi "Ya wuce reni ba a yi mai shi, Amadu jikan Garba sadauki" domin ya fito da wani lamarin dake nuna jarunta da  sadaukarwa da tsananin tauhidin wanda ya yiwa wannan Waƙar duk kuwa da fuskantar barazanar rasa rayuwarsa a Rana mai kama ta yau, a  shekarar 1966(15/01/1966) daga hannun sojojin da suka taru a gidan Gwamnatin Jihar Arewa/Arewa House, Unguwar Sarki, Kaduna domin su kashe shi. Allahu Akbar!!!

Duba da ma'anar wannan muƙami/laƙabi na "Sardaunan Sakkwato" da ɗan uwansa, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar III ya bashi tabbas wannan hali da ya nuna a wannan rana da ya haɗu da ajalinsa, ya daɗa tabbatar da cancantarsa na riƙe muƙamin/laƙabin "Sardauna".

Bayan kammala Jihadin Jaddada Addinin Musulunci a farkon ƙarni na 19 da ya yi sanadiyar kafuwar Daular Usmaniya, Jagororin Daular musamman musamman Amirul Muminina Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi sun kawo tsare-tsare a sha'anin gudanar da Daular ta hanyar shigowa da muƙaman/laƙabin sarautu daga Daular Gobir.

A cikin irin waɗan nan muƙaman/laƙabin ne da  Amirul Muminina Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio ya kawo, ya naɗa Malam Halilu ɗan ƙanensa Malam Hassan ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio a matsayin Sardaunan Sakkwato na farko ya kuma kai shi a garin Marnona ( Marnona a halin yanzu na cikin Ƙaramar Hukumar Mulkin Wurno, Jihar Sakkwato) domin ya yi hakimci.

La'akari da matsayin muƙamin Sardauna a Daular Gobir da ake baiwa ɗan Sarkin da ya yi fice wajen yak'i  ne ya sanya aka naɗa Malam Halilu ɗan Malam Hassan ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio a matsayin Sardaunan Sakkwato na farko aka kuma girke shi a Marnona domin tariyar abokan gabar da ka iya ɓullowa Cibiyar Daular Usmaniya daga  Gabashi da Arewancinta . Ya kuma tsare wannan aiki da aka bashi bilhak'k'i, aka kuma samu gagarumar nasarar dak'ile dukan barazanar abokan gaba. Allah ya kyauta makwanci, amin.

A lokacin da Turawan Mulkin Mallaka Na Ingila suka shata daga da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Attahiru I da Jama'arsa  a wurin da ake kira Giginya dake Birnin Sakkwato, Ranar 15/03/1903, yaƙi bayar da kai ga Turawan, domin  kaucewa walaƙanci shi da Jama'arsa  suka  zaɓi su yi shahada da imanin hakan zai fi zama mafi a'ala ga Al'ummar Daular kwaata!

A lokacin da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar III ya baiwa Malam Ahmadu Bello ɗan Sarkin Raɓah Ibrahimu ɗan Sarkin Musulmi Abubakar II/Mai Raɓah ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio wannan sarauta ta Sardauna ( wadda ita ce shi Sarkin Musulmi Abubakar III ɗan Modibbo Usman ɗan Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio ke riƙe da ita gabanin ya zama Sarkin Musulmi a shekarar 1938) kamar sai da ya yi la'akari da  samun ɗan Sarkin da zai iya kare mutuncin Daular Usmaniya a kowane irin hali ya samu kansa. Allahu Akbar!

Cikin hukuncin Allah SWT sai kuwa gashi Sardaunan sa bai bashi kunya ba, domin yak'i amincewa ya yi gudun Jihadi, ya sadaukar da rayuwarsa kamar yadda iyaye da kakanninsa suka yi a lokacin yaƙin jaddada addinin musulunci na Daular Usmaniya har ya zuwa kutsowar Turawan Mulkin Mallaka na Ingila a cikin Daular.

A daidai wannan rana ta Litinin, 15/01/2024 da muke alhinin rashin wannan hazik'i, gwarzon jagora shi da sauran danginsa da aka yiwa kisan gilla shekaru 58 da suka wuce, muna addu'ar Allah SWT ya jaddada masu rahama, ya jiƙan dukan magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.

Daga Taskar:
Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments