1. Sardaunan farko, Malam Halilu ɗan Malam Hassan ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio /zamanin mulkin Amirul Muminina Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio (wanda shi Amirul Muminina Muhammadu Bello ya yi mulki ne daga 1817-1837).
2. Malam Abubakar ɗan
Malam Usman ɗan Sarkin
Musulmi Mu'azu ɗan
Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan
Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio / Sarkin Musulmi Abubakar III, a lokacin mulkin Sarkin
Musulmi Hassan ɗan
Mu'azu ( shi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Hassan ɗan
Mu'azu ya yi mulki ne daga 1931-1938).
3. Sir Ahmadu Bello, GCON, KBE ɗan Sarkin Raɓah
Ibrahimu ɗan Sarkin
Musulmi Abubakar II /Mai Raɓah
ɗan Sarkin Musulmi
Muhammadu Bello ɗan
Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio /zamanin mulkin Sarkin Musulmi Abubakar III (1938 zuwa
1966 lokacin da shi Sardaunan ya yi wafati).
4. Sir Alhaji Abubakar Alhaji Ɗan Sarkin Shanu Alhaji Muhammadu Alhaji Ɗan
Bara'u ɗan Haliru Ɗan
Malam Buhari Ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio /zamanin mulkin Mai Alfarma
Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuƙi (an naɗa
shi Sardauna a cikin 1990s ya zuwa yau).
Allah ya jiƙan
magabatanmu da rahama, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.