Garau-Garau Na Zamani a Abincin Hausawa (Kuskus, Dambu, Taliya, Makaroni)

    Gabatarwa

    A babi na goma an yi bayani dangane da nau’o’in abincin wasa -wasa na Hausawa  a gargajiyance. Nau’o’in wasa-wasar da aka lissafo a ƙ ar ƙ ashin babi na goma, duk akan same su a zamanance. Bambancin da ke tsakani bai wuce na kayan ha ɗ i ba. Nau’o’in wasa-wasar gargajiya da ake samu a zamani sun ha ɗ a da:

    i. Wasa-wasar dawa

    ii. Wasa-wasar shinkafa

    iii. Wasa-wasar gero

    iv. Wasa-wasar dambu

    v. Wasa-wasar burabusko

    vi. Wasa-wasar wake

    Wasa-Wasa r Kuskus

    Kayan haɗin da za a tanada su ne:

    i. Gishiri

    ii. Kuskus

    iii. Mai

    iv. Ruwa

    v. Yaji

    Wannan nau’in abinci kuwa, ruwa za a tafasa daidai adadin sanwar da za a yi. Za zuba kuskus a cikin ruwan tare da gishiri. Da zarar ya yi, za a ga ya kumbura sannan ya yi wasar-wasar. Sai a lura sosai, domin kada a cika masa ruwa yadda zai cakuɗe. Akan ci wannan  nau’in abinci da mai da yaji, wani lokaci har ma da miya .

    Wasa-Wasa r Dambu

    Kayan haɗin da za a tanada su ne:

    a. Mai

    b. Ɓarzazziyar Masara ko Shinkafa 

    c. Ruwa

    d. Yaji

    Za dafa dambun masara  ko na shinkafa haka nan ba tare da an saka masa komai ba. Akan yi wannan  dafuwa ne ta hanyar turara shi a madanbaci. Idan ya dafu, sai a kwashe shi. Za a iya cin sa da mai da gishiri da Barkono (tonka). Haka kuma, shi ma za a iya saka ganye a yi kwaɗo  da shi tare da ƙuli. Haka kuma, za a iya saka masa miya  idan ana buƙata a ci da ita.

    Wasa-Wasa r Taliya

    Kayan haɗin da za a tanada su ne:

    i. Gishiri

    ii. Mai

    iii. Ruwa

    iv. Taliya

    v. Yaji

    Za a dafa taliya da gishiri a tukunya  da farko. Ana kula da adadin ruwan da za a sanya domin kada ta cakuɗe. Bayan ta nuna kuma ta tsane, ana cin ta da mai da yaji, ko kuma a sanya miya .

    Wasa-Wasar Makaroni

    Kayan haɗin da za a tanada su ne:

    i. Gishiri

    ii. Mai

    iii. Makaroni

    iv. Ruwa

    v. Yaji

    Za a dafa makaroni da gishiri a tukunya  tamkar yadda ake dafa taliya (wanda aka yi bayani a 24.1.3 a sama). Za a kula da adadin ruwan da za a sanya domin kada ta cakuɗe. Bayan ta nuna kuma ta tsane, ana cin ta da mai da yaji, ko kuma a sanya miya .

    Kammalawa

    Abincin  wasa -wasa, abinci ne mai sauƙin dafuwa ba tare da an saka kayayakin lambu a wajen dafuwa ko cinsa ba. Duk da haka, akan samu waɗanda ke amfani da kayan lambun yayin cin wasa-wasar. Mafi yawanci abinci ne da ake cin sa da mai da yaji. Wani lokaci kuma akan sanya miya , musamman a zamanin yau.

     

    Citation (Manazartar Littafin):   Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

    Get a copy:
    To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
    +2348133529736

    You can also write an email to:

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.