Ticker

6/recent/ticker-posts

Hausar Masu Sana’ar Tuggu

 Takardar ƙara wa juna sani da aka gabatar a ajin ALH 400: Seminars, a Sashen Nazarin Harsuna Da Aladu, Jamiar Tarayya Gusau, Nijeriya, (2022/2023 Academic Session).

Federal University Gusau (FUG) Nigeria

Hausar Masu Sana’ar Tuggu

Na

SA’ADU ISAH

G.S.M: 08065223927

Email: isasa’adau92@gmail.com

Tsakure

Sana’a dai aka ce, “sa’a” bisa ga muhimmancin sana’a ga rayuwar Bahaushe, da bai yarda da zaman hannu Rabbana ba, ko zaman kashe wando ba ne. Ya sa wannan takardar, ta himmatu ga bibiyar kadin sana’ar tuggu ga Bahaushe. Domin rarrabewa tsakanin ɗan duma da kabewa, aka dubi sana’ar ita kanta ta tuggu, da yadda ‘yan tuggun, suke sarrafa harshen Hausa, a cikin sana’ar, da ake fatan takardar, za ta zamo ƙari wanda ya fi ƙara, ko kuma ta cike giɓi a fagen ilimi.

1.0 Gabatarwa

Sana’ar tuggu (Saye da sayar war dabbobi), sana’a ce daga cikin sana’o’in gargajiyar Hausawa, da ta ke cikin kashin biyar na sana’o’in Hausawa, da ake nemo abinci kaitsaye a cikinta kamar yadda masana suka ambata, Alhassan, (1984) da Zurmi, (2010: 44).

A cikin sana’o’in gargajiya na Hauswa, kowace daga cikinsu, tana ƙunshe da wani tsarin da ake aiwatar da ita, na muhalli da sarrafa harse, da a ciki ne ake samun Hausar ɓangarorin ma su aiwatar da sana’o’in, da a nan ne batun Hausar masu sana’ar tuggu ta taso. Wanan ne batun dubawar muƙalar, da ake fatar ta cike giɓin da ke akwai, ko kuma ta zamo ƙari, wanda aka ce, ya fi ƙara, a cikin fagen ilimi.

2.0 Dabarun Bincike

A wannan bincike, an yi amfani da tsurar bayanai (qualitative form of research), haka ma an yi amfani da babbar hanyar tattara bayanai daga tushe na farko (primary souces), da kuma hanyar tattara bayanai daga majiya ta biyu (secondary souces), inda aka yi bita tare da nazartar ayukkan magabata, musamman bubbugaggun littattafai, da kundayen digiri na farko, da kuma muƙalu.

2.1 Bitar Ma’anar Sana’a

Abbas M.H (2021) “Sana’ar tuggu a Kasar Maru” Kundin Digirin farko Jami’ar Tarayya Gusau,

Ƙamusun Hausa, (C.N.H.N, 2006: 387), an bayyana, “Sana’a da aikin da mutun ya ke yi domin dogaro da kai da kuma samun abinci.” Amma a wurin Garba, (1991: 1) cikin Kundin Digirin farko mai taken Sana’ar Tuggu a Kasara Maru ya ce, “Sana’a ita ce ginshiƙin rayuwa da tattalin arzikin yau da kullum na Hausawa, tare da kasancewa ɗaya daga cikin muhaimmai, kuma manyan gano martabar mutum da ƙasaitarsa, da matsayinsa a cikin alumma. Yayinda shi kuwa Durumin Iya, (2006) Duk a cikin Kundin Digirin farko mai taken Sana’ar Tuggu a Kasar Maru ya ce, “Sana’a wata hanyace da ɗan’Adam kan ta’allaƙa kansa domin samun abin masarufi da ya shafi, shaanin kasuwanci, wato shaani na saye da sayarwa.

2.2 Ma’anar Tuggu

Bargery, (1934), a cikin Kundin Digirin Farko mai taken Sana’ar tuggu a Kasar Maru Jami’ar Tarayya Gusau ya ambata, “Tuggu shi ne saye da sayarwa ne na bayi da dabbobi.” Sai dai a wurin Ummaru, (2022) duk a cikin a cikin Kundin Digirin Farko ya ce, “Tuggu sana’a ce ta saye da sayarwar dabbobi na gida da tsuntsaye.” Amma a wurin Ibrahim, (2023) yana ganin, “Tuggu sana’a ce da ake aiwatarwa a tsaye, ta hanyar saye da sayarwa na dabbobi, kuma dabbobin na gida da ake kiwo, da ake aiwatarwa cikin kasuwar dabbobi (k{r|a ta dabbobi).”

2.2.1 Ire-iren Tuggu

Sana’ar tuggun dabbobi ta kasu biyu kamar haka: (i) Tuggun Ƙanann Dabbobi. (ii) Tuggun Manyan Dabbobi.

i-Tuggun Ƙanannan Dabbobi:- Shi ne saye da sayarwar ƙananan dabbobi, da galibi ake samun wani mutun ya killace wuri, da ake cewa dangali, ya ɗaura ‘yaggiya mai tsawo, duk mai ƙaramar dabba, ya kawo zai amsa ya ɗaure a dangalinsa, da nufin tallatawa ga maisaye, yana a matsayin tsakanin mai dabbar da wanda ya zo saye, a wannan muhalin a kan samu shi dillali da yaransa. Misalin Dabbobin da ake sayarwa a wannan tuggun: Tumaki, da Raguna, da Awaki, da Bunsurai.

ii- Tuggun Manyan Dabbobi:- Shi ne saye da sayar da manyan dabbobin da ake kiwatawa cikin gida, in aka tashi sayar wa sai a samu jagoran dangali tare da yaransa, a cikin da’irarsa an kafa manyan turakun ɗaure dabbobi, a ba shi talla, duk mai saya ya zo da shi zai cinaki, in ya fahimci dabbar ta sayu, sai ya bayar da shawara ga mai ita in ya sallama, sai a amshi kuɗin dabbar, in kuma bai sallama ba, ƙari yake nema in Allah Ya yi abin da mai saye na farko shikenan, in kuma ya fita ga cinakin wani ya shigo, haka dai za a yi, har cikani ya faɗi. Abiya dabbar, mai saye ya biya kuɗin dabba da la’ada, kana wanda aka sayar wa da dabbar, ya biya ladan talla ga dillali da ya shiga tsakani ya zuwa faɗuwar cinakin dabbar. Misalin Manyan dabbobi sune kamar haka: Raƙumma, da Shanu, da Dawaki, da Jakai. Da sauransu

2.3 Matallafa Sana’ar Tuggu

Matallafa gudanar da sana’ar tuggu su ne kayayyaki da ake amfani da su wurin aiwatar da sana’ar, su ne kamar haka:

a-Yaggiya ko Yaggwai    b-Kuɗi     c-Abincin Dabbobi

e-Baho     

f-Dabaibaya da Gindi g-Bel dogo h-Falen iggiyar kora i-Ruwa

j-Takunkumi,     k- Dangwali.D.S

2.4 Muhimmancin Sana’ar Tuggu

Binciken ya nuna sana’ar tuggu na da matuƙar muhimmanci, kamar haka:

 i-Sana’ar tuggu sana’ace ta dogaro dakai.

ii-Sana’ar tuggu na taimaka wa gwamnatoci wurin samar da kuɗin shiga. iii-Sana’ar tuggu na taimaka wa sana’ar fawa wurin, sawo dabbobin da ake yankawa a mahauta.

iv-Sana’ar tuggu na taimaka wa sana’ar Jima wurin samar da fatun da dabbobin da ake jemewa. v- Sana’ara tuggu na taimaka wa sana’ar dukanci. Domin sai an sayi dabba an yanka ta kana masu jima su saye fatu su jeme, kana dukawa su kuma su sayi jemammar fatar su gudanar da ta su sana’ar.

3.0 Ma’anar Harshe

Tijjani M.S (2012:4) A cikin Littafinsa mai suna Sakace akan Karin Harshen Hausa, Fagge (1987) Ya bayyana cewa, Harshe hanya ce ta sadarwa wadda ake amfani da sauti bisa tsari na wasu dokoki.

Yakasai S.A (2020:3) A cikn Littafinsa mai suna Jagoran Ilimin walwarar Harshe, Ya bayyana cewa, Harshe wata hanya ce ta bayyana kai da kuma hulda tsakanin Mutane wadda Dabbobi basu da irinta.

3.1 Ma’anar Karin Harshe

Tijjani M.S (2012:5) A cikin Littafinsa mai suna Sakace akan Karin Harshen Hausa, Zaruk da wasu (1990) Sun bayyana cewa, Karin Harshe wasu yan ban-bance ban-bance ne na lafazi da na Kalmomi da Jimloli tsakanin rukunin Al’umma ko shiyoyin Kasa mai Harshe daya  

3.2 Hausar Masu Sana’ar Tuggu

A nan za a dubi yadda ‘yan tuggu suke sarrafa harshen Hausa ta kalmomi da ma’noninsu, da kuma yadda ‘yan tuggun suke sarrafa harshen Hausa, ta ɓangaren jumloli da ma’anoninsu, kamar haka:

3.2.1 Kalmomin ‘Yan Tuggu da Ma’anoninsu

 

Lambobi

Kalmomin ‘Yan Tuggu

Ma’anonin Kalmomin

 1

Goga

Taya dabba tare da sallama wa

 2

Kasgaya

Matashiya akuya

 3

Burguma

Budurwar akuya mai ɗauke da juna biyu

 4

Alhaji

Farin sa tas

 5

Batala

Ƙosassar tunkiya

 6

Juya

Tunkiya ko Akuya Ko Saniyar da ba ta haihuwa ta yi sosai

 7

Guzuma

Tsohuwar shanuwa kuma mai yunwa

 8

Uda

Dabba mai ratsin fari da baƙi

 9

Dungu

Kuɗɗi naira dubu goma katse

 10

Jaka

Naira ɗari biyu

 11

Dangali

Wurin da ake ɗaure dabbobi a kasuwar kar

 12

Garke

Nau’in dabbobi masu yawa, ko kuma wurin da ake ɗaure dabbobin

 13

Falke

Mai sayen dabbobi domin ya sayar ya samu riba

 14

Dillali

Wanda ke shiga tsakanin mai dabbar da ya kawo kasuwa da kuma mai sayen dabbar

 15

Ɗauri

Naira dubu goma ƙirgaggi

 16

Fammetin

Naira dubu ɗari uku cas

 17

Danga

Keɓaɓɓe ko killataccen wurin da ake ajiye dabbobi a cikin kasuwar kara, da ake kulawa da su.

 18

Jargwali

Shedar da makiya suke yi wa dabbo, ko yi dabbab wuta ko kuma tsaga kunnen dabba

 19

Zari ko Asurka

‘Yaggiyar da ake hude hancinsa mai faɗa ana sa mashi

 20

Gindi

‘Yaggiya ce da ake ɗaurawa ga ƙafafu biyu na gaba ga sa ko nagge in an kawota kasuwar kara wurin sayarwa

 21

Dabaibaya

‘Yaggiya ce da ake ɗaurawa ga ƙafafu biyu na gaba jaki ko raƙumi ko doki in an kawo shi kasuwar kara sayarwa

 22

Nocewa

Wata ‘yaggiya ce da ake ɗauro wa nagge ko sa a wuya sai alaƙamota ga ƙafa ta gaba ɗaya, in a ka samu dabba na da faɗa a wurin sayarwa a kasuwar kara

 23

Yaro

Wanda aka kawo wurin Dillali ko falke a dangalin dilalli ko dangar falke, domin ya koyi sana’ar tuggu

 24

Nà hùráa

Kyautatawar da dillalai ke yi wa yara masu kawo dabbobi a wurinsu

 25

Kame

Falake ne da yaransa ke taro dabba kafin a shigo kasuwar kara domin ya saye bayan an hannunta dabbar ga dillali

 26

Dame

Ruwa na musamman da ake ba dabba

 27

Ɗure

Maganin da ake girgizawa akwalba a ɗurawa dabba

 28

Bama

Yi wa wani cuwa-cuwa

 29

Buzurwa

Tunkiya ko Akuya mai gashi tukus a gefen cinya

 30

Ɓale

Akuya ko Tunkiya ko Saniya baƙa ƙirin

 31

Duna

Jaki ko sa ko bunsuru baƙi ƙirin

 32

Abadan

Bunsuru mai manyan kunnuwa

 33

Komi

Wurin zuba wa dabbobi abinci mai zurfi

 34

Sule-sule

Sa mai fari da baƙi

 35

Kargo

Jan sa ne ake cewa haka

 

3.2.2 Jumlolin ‘Yan Tuggu da Ma’anoninsu

Lambobi

Jumloli ‘Yan Tuggu

Ma’anonin Jumlolin ‘Yan Tuggu

 1

Farte ne

Mai kuɗɗi ne

 2

Ta je kokuwa ne

An yanka dabbar ne wato ta kasa kenan

 3

Ya yi man tsurku

Ya ɓata man ciniki

 4

Za mu je riga

Za mu je cikin gari sayen dabba

 5

Kasuwa ta yi ambazo

Dabbobi sun yi tsada a kasuwa

 6

Kar a yi muna nudu

A hargitsa cinakin

 7

Ana yi ne

Ana kan cinikin dabba

 8

Nawa za ka sara ?

Cinaki da baƙauye

 9

An ciyo riga

An ƙwari mai saye kenan

 10

Ya biyo sama

An sa yi akuya an sallama ba kuɗɗi

 

4.0 Sakamako Bicike

Sakamakon da aka samu a wannan bincike shi ne kamar haka:

a-     an gano ‘yan tuggu wato masu sana’ar dabbobi, suna da harshen da suke amfani da shi domin ɓadda bami.

b-    an gano ‘yan tuggu ɓangarori uku ne, (i) masu tuggun ƙanan dabbobi wato awaki, da tumki, da raaguna, da bunsurai (ii) masu tuggun shanu (iii) masu tuggun jakai, da raumai, da dawaki.

c-     an gano ɗan tuggu shi ne msanin ƙuɗin dabba in za a sayar da ita, kuma shi ne ke shiga tsakanin mai sayen dabba da kuma mai dabbar a wurin cinikin dabbar.

d-    an gano wanda ke sawo dabbobi daga wata kasuwar kara ya zuwa wata kasuwar karar domin ya sayar ya samu riba, sunansa falke.

e-     kazalika an gano sana’ar tuggu ta wata fuskar ta goya wasu sana’o’in gargajiya, kamar sana’ar fawa da jima, dukanci.

4.1 Kammalawa

Wannan takarda, an gudanar da binciken ta ne, ta yin amfani da tsurar bayanai, da kuma yin amfani da babbar hanyar tattara bayanai, daga tushe na farko, da kuma hanyar tattara bayanai daga majiya, sai daɗin daɗawa, bin hanyar nazarin ayukkan magabata, musamman bubbugaggun littattafai, da kundayen digiri na farko, da kuma muƙalu, duka dai, domin a sami ganin an cimma gacin, muƙalar ta share fage, ko kuma ta cike giɓin da ke akwai fagen ilimi.

 Manzarta

Abbas, M.H. (2021). “Sana’ar Tuggu a Ƙasar Maru Kundin Digirin Farko a Jamiar Tarayya, Gusau.

Tijjani M.S (2012 )”Sakace a kan Karin Harshen Hausa, Typeset and Published ABSUR Comprint F.C.E Kano.

Yakasai S.A (2020) “ Jagoran Ilimin Walwarar Harshe” Printed by Amal Printing Press Limited.

Ahmad B. (2020) “ Daidaitacciyar Hausa da Kare-karen Harshen Hausa” Ahmadu Bello University Press Limited zaria. 

Post a Comment

0 Comments