TAMBAYA (70)❓
Shin menene hujjar cewar komai dawafi (Bautar Allah) yake a
sama da kasa ?
AMSA❗
Alhamdulillah
Allah Azzawajallah yace;
( وَلِلَّهِ
يَسْجُدُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ مِن دَابَّةٍ وَالْمَلَائِكَةُ
وَهُمْ لَا يَسْتَكْبِرُونَ )
النحل
(49) An-Nahl
Kuma ga Allah, abin da yake a cikin sammai da ƙasa
na dabba da mala'iku, suke yin sujada, kuma ba su kangara."
Tabbas, ba abune baqo ba idan akace maka musulmi suna zagaye
dakin ka'abah a matsayin dawafi, amman idan akace maka "Duniya, wata da
rana duk dawafi suma suke" dole mamaki zai baibaye mutum tareda tambayar
to me sukeyiwa dawafin su kuma ?
Ilimin kimiyya a sararin samaniya (Astronomy) ne kadai
yakeda cikakkiyar amsar wannan tambaya mai cikeda sarqaqiya. Masana ilimin kasa
sun gano cewar garin Makkah shi ne tsakiyar duniya, tsakiyar Makka kuma dakin
Ka'abah ne wanda aka fitarda Google map dinsa wanda kamar yanda bayani ya
gabata cewar latitude na coordinate dinsa shi ne 21° degree, 25' minutes wanda
idan ka dauki 2 din tafarko ita ce Sura ta 2 wato Suratul Baqara sauran
numbobin kuma (125) na Suratu Baqara din shi ne ayar farko a cikin Qur'ani
wadda tayi magana akan dakin na Ka'abah, inda Allah SWT yace;
( وَإِذْ
جَعَلْنَا الْبَيْتَ مَثَابَةً لِّلنَّاسِ
البقرة
(125) Al-Baqara
Kuma a lokacin da Muka sanya dakin ya zama makoma ga mutane,
Tun shekaru wajen 1,400 anfitarda location din Ka'aba a
Qur'ani kafinma Geographers su gano (Allahu Akbar!)
Kamar yanda marigayi Dr. Bashir Usman Tofa yace a cikin
littafinsa mai suna "Kimiyya a sararin samaniya": da awon matsawar
launin shudin birnin Andromeda (Daya daga cikin samada galaxy miliyon 100 dake
maqotaka da tamu acan sama) ne aka lissafa cewar yana dosomune da saurin
kilometer 300 a kowanne second, amman kada muji tsoro domin muma birninmu
(Milkyway Galaxy dake jihar Virgo) ba a tsaye yake ba, kuma da akwai dayawa
masu nisantarmu da sauri fiyeda kilometer 1,000 a second daya
Abin lura anan shi ne, komai a sararin samaniya tafiya yake
yana zagaya wani abu "tamkar dawafi" dukkansu daga dama zuwa hagu
(anticlockwise direction) yadda musulmi suke zagaya Ka'abah a doron wannan
duniyar tamu ta Ard, haka wata (moon) yake zagaye duniyarmu, ita kuma tana
zagaye yar Shams (Rana), ita kuma ranar tana zagaya badalar anguwarta (Suratu
Yasin 36:38) da saurin kilometer 250 a kowanne second, ita kuma anguwar tana
zagaya tsakiyar birnin Milky way, shikuma yana zagaya Jihar Virgo, ita kuma
tana zagaya babbar jihar (Super Cluster ta hannun gefen Orion) ita kuma tana
zagaya wani, shikuma yana zagaya wani abu, shikuma yana zagaya samaniya ta
daya, ita kuma tana zagaya ta 2, har zuwa dai sama ta 7
Dakata da karatu, kadan duba babban dan yatsan hannunka
(fingerprints) zakafi gane bayanan dalla dalla, domin kuwa zakaga alamun kamar
zagayen dawafi. Allahu Akbar! Nauyin Shams yakai kokuma ya zarce tonnes
200,000,000,000,000,000, amman dukda haka tana tafiya zagayenta (dawafi) da
saurin kilometer 2,150 a kowanne second. Da wannan sauri takan dauki shekaru
250 kafin tayi zagaye daya, Ita kuma duniyarmu (Ard) tana zagaye daya a cikin
23 hours 56 minutes (24hrs approximately) dakuma kewaye (dawafi) daya a cikin
kwanaki 365, wato shekara daya kenan. Allahu Akbar!
Muna roqon Allah Ya tabbatardamu akan musulunci bisa bin
sunnar Ma'aiki SAW, ya rusa kafirci da kafirai
Burina mu duqufa wajen binciken ilimin Astronomy domin mu
kara sanin ayoyin Allah SWT dake sararin Sama'ud Dunya
Wallahu ta'ala a'alam
Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa
anta, astaghfiruka wa'atubi ilayk
Amsawa;
Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.