𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Naji ance wai Namiji Musulmi zai iya auren mace Kirista,
amma Mace Musulma ba zata auri Namiji Kirista ba, Shin aya ce ko hadisi ko kuma
magana ce kawai?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Haƙiƙa Shari'ar Muslunci ta halattawa Musulmi ya auri Mace Kirista
ko Bayahudiya, wannan itace Maganar mafi yawa daga cikin Malamai Ma'abota
Ilimi, kuma halaccin hakan ya samo Asaline daga cikin Al-ƙur-ani faɗin Allah(ﷻ)
وَطَعَامُ
الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ حِلٌّ لَّكُمْ وَطَعَامُكُمْ حِلٌّ لَّهُمْ وَالْمُحْصَنَاتُ
مِنَ الْمُؤْمِنَاتِ وَالْمُحْصَنَاتُ مِنَ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ مِن قَبْلِكُمْ
MA'ANA
Abincin waɗan
da aka zo musu da Littafi (Yahudu da Nasara) halal ne a gare ku, haka kuma
abincin ku (ku Musulmi) halal ne a gare su, Haka nan (halal ne ku auri)
kamammun Mata (waɗanda
basa zina) daga cikin Muminai, (Musulmai) da kuma kamammun Mata daga cikin waɗanda aka zo musu da
Littafi kafinku, (Yahudu da Nasara) (suratul Má'ida aya 5)
Danhaka Malamai sukace idan Ahlul-kitabi (Kirista ko
Bayahudiya) ta kasance ta kame kanta bata aikata zina, to ya halatta a aureta,
duk da cewa suma Ahlul-Kitabi kafirai ne Mushrikai da Nassin Al-ƙur-ani
Mai girma, to amma waccan aya ta keɓance
su da wannan hukunci, danhaka su kaɗai
ne Allah(ﷻ) ya halatta mana muci
yankan su da abincin su kuma mu auri Matan su, shi yasa wannan halacci ya taƙaita
ne kaɗai akan
Ahlul-kitabi (Yahudu da Nasara), amma sauran Kafirai da suke bautar waɗansu abubuwa dabam-dabam
kokuma waɗan dama
basu da wani abin bauta (Majusawa) haramun ne a aure su, saboda faɗin Allah(ﷻ)
وَلَا
تَنكِحُوا الْمُشْرِكَاتِ حَتَّىٰ يُؤْمِنَّ وَلَأَمَةٌ مُّؤْمِنَةٌ خَيْرٌ مِّن مُّشْرِكَةٍ
وَلَوْ أَعْجَبَتْكُمْ ...
MA'ANA
Kada ku auri Mata Mushrikai (Kafirai), domin (ku auri) Baiwa
Mumina shi yafi alkhairi akan ku auri Mushrika koda kuwa kyawunta ya ƙayatar
daku…… (suratul Bakara
aya 221)
Haka nan wannan Halacci ya taƙaita ne kaɗai
akan Maza Musulmai, amma baya halatta ga Mace Musulma ta auri Kirista, ko kuma
dukkan wani wanda ba Musulmiba
Saidai abin lura anan shine, halacci ne kawai akace Musulmi
ya auri Ahlul-kitabi, amma ko Matsayin Mustahabbi hakan bai kaiba, danhaka
Malamai sukace idan Musulmi ya aminta da cewa wannan Matar Kirista da zai aura
ba zata iya rinjayarsa ba ya yi Ridda kokuma ta iya rinjayar 'ya'yansa zuwa ga
addinin ta to shikenan ya halatta ya aureta, danhaka ana buƙatar
Mutum ya kasance yana da Ƙarfin imani dakuma ilimin addini atare dashi, sannan ya
kasance niyyarsa ta yin auren itace ya yi ta ƙoƙarin nuna mata addinin Musulnci har ta
gane ta karɓa, to
amma duk dahaka Malamai sukace barin auren su ɗin
shine yafi alkhairi, Musamman ma a irin wannan zamanin da muke cikinsa wanda
galibi idan anyi irin wannan auren to Kallabi ne yake jan Rawani a madadin
Rawani yaja Kallabi, abin nufi da yawa mazan sukan yi ridda ne, kuma koda Mutum
yana da ƙarfin
imanin da ba zata iya rinjayar sa ba, to abu ne mai sauƙi awajenta ta iya
rinjayar 'yaa'yan da suka haifa tare dashi, shi yasa Malamai sukace barinsa ɗin zaifi sa Mutum yatsira
da imaninsa da kuma na 'ya'yansa, danhaka gara Mutum yaje ya nemi 'yar'uwar sa
Musulma ya aura
шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ
Mυѕтαρнα
Uѕмαи
08032531505
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
HUKUNCIN AUREN KIRISTA
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Naji ance wai Namiji Musulmi zai iya auren mace Kirista, amma Mace
Musulma ba zata auri Namiji Kirista ba, Shin aya ce ko hadisi ko kuma magana ce
kawai?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Haƙiƙa Shari'ar Muslunci ta
halattawa Musulmi ya auri Mace Kirista ko Bayahudiya, wannan itace Maganar mafi
yawa daga cikin Malamai Ma'abota Ilimi, kuma halaccin hakan ya samo Asaline
daga cikin Alƙur'āni faɗin Allah(ﷻ):
وَطَعَامُ
الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ حِلٌّ لَّكُمْ وَطَعَامُكُمْ حِلٌّ لَّهُمْ وَالْمُحْصَنَاتُ
مِنَ الْمُؤْمِنَاتِ وَالْمُحْصَنَاتُ مِنَ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ مِن قَبْلِكُمْ
Abincin waɗan da
aka zo musu da Littafi (Yahudu da Nasara) halal ne a gare ku, haka kuma abincin
ku (ku Musulmi) halal ne a gare su, Haka nan (halal ne ku auri) kamammun Mata
(waɗanda basa zina) daga cikin Muminai,
(Musulmai) da kuma kamammun Mata daga cikin waɗanda aka zo musu da Littafi kafinku, (Yahudu da Nasara) (suratul Má'ida
aya 5)
Danhaka Malamai sukace idan Ahlul-kitabi (Kirista ko Bayahudiya) ta
kasance ta kame kanta bata aikata zina, to ya halatta a aureta, duk da cewa
suma Ahlul-Kitabi kafirai ne Mushrikai da Nassin Alƙur'ani Mai girma, to
amma waccan aya ta keɓance
su da wannan hukunci, danhaka su kaɗai ne Allah(ﷻ)
ya halatta mana muci yankan su da abincin su kuma mu auri Matan su, shi yasa
wannan halacci ya taƙaita ne kaɗai
akan Ahlul-kitabi (Yahudu da Nasara), amma sauran Kafirai da suke bautar waɗansu abubuwa dabam-dabam kokuma waɗanda ma basu da wani abin bauta (Majusawa)
haramun ne a aure su, saboda faɗin Allah(ﷻ):
وَلَا
تَنكِحُوا الْمُشْرِكَاتِ حَتَّىٰ يُؤْمِنَّ وَلَأَمَةٌ مُّؤْمِنَةٌ خَيْرٌ مِّن مُّشْرِكَةٍ
وَلَوْ أَعْجَبَتْكُمْ
...
Kada ku auri Mata Mushrikai (Kafirai), domin (ku auri) Baiwa Mumina shi
yafi alkhairi akan ku auri Mushrika koda kuwa kyawunta ya ƙayatar daku…… (suratul Bakara aya 221)
Haka nan wannan Halacci ya taƙaita ne kaɗai akan Maza Musulmai, amma baya halatta ga Mace Musulma ta auri
Kirista, ko kuma dukkan wani wanda ba Musulmiba:
Saidai abin lura anan shine, halacci ne kawai akace Musulmi ya auri
Ahlul-kitabi, amma ko Matsayin Mustahabbi hakan bai kaiba, danhaka Malamai
sukace idan Musulmi ya aminta da cewa wannan Matar Kirista da zai aura ba zata
iya rinjayarsa ba yayi Ridda kokuma ta iya rinjayar 'ya'yansa zuwa ga addinin
ta to shikenan ya halatta ya aureta, danhaka ana buƙatar Mutum ya kasance
yana da Ƙarfin
imani dakuma ilimin addini atare dashi, sannan ya kasance niyyarsa ta yin auren
itace yayi ta ƙoƙarin nuna mata addinin
Musulnci har ta gane ta karɓa, to amma duk dahaka Malamai sukace barin auren su ɗin shine yafi alkhairi, Musamman ma a irin
wannan zamanin da muke cikinsa wanda galibi idan anyi irin wannan auren to
Kallabi ne yake jan Rawani a madadin Rawani yaja Kallabi, abin nufi da yawa
mazan sukan yi ridda ne, kuma koda Mutum yana da ƙarfin imanin da ba zata iya rinjayar sa ba,
to abu ne mai sauƙi awajenta ta iya rinjayar 'ya'yan da suka haifa tare dashi, shi yasa
Malamai sukace barinsa ɗin zaifi sa Mutum yatsira da imaninsa da kuma na 'ya'yansa, danhaka
gara Mutum yaje ya nemi 'yar'uwar sa Musulma ya aura.
шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ
Mυѕтαρнα Uѕмαи
08032531505
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8qu9GT
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓��𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAmsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.