𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Ko cin yanke-yanken Kiristoci a wannan zamani namu na yau
yana halatta, duk kuwa da cewa hanyoyin yanka a wurinsu sun yawaita, watau
kamar yin amfani da injuna, da kuma abubuwa masu daskarar da kwakwalwa a wurin
yankan?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Cin yanke-yankensu yana halatta, matukar dai ba a san da
cewa an yanka dabbar ne ta hanyar da ba ta dace da Shari'a ba, saboda asalin
lamari shi ne halaccin cin sa, kamar dai yankan musulmi, saboda faɗin Maɗaukaki: Da abincin waɗannan da aka ba su
littafi halal ne yake a gare ku, kuma abincin ku halal yake gare su)).
Sheik Uthaimeen ya ce cikin littafinsa Ash-Sharhul Mumtii
12/148:-
ﻓﺎﻟﺤﺎﺻﻞ : ﺍﻥ ﺍﻟﺬﻱ ﻋﻠﻴﻪ ﺟﻤﻬﻮﺭ
ﺍﻫﻞ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﺍﻥ ﻣﻦ ﺗﺪﻳﻦ ﺑﺪﻳﻦ ﺍﻫﻞ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻧﺘﺴﺐ ﺍﻟﻴﻬﻢ ﻭﻟﻮ ﻛﺎﻥ ﻳﻘﻮﻝ ﺑﺎﻟﺘﺜﻠﻴﺚ ﻓﺎﻧﻪ ﺗﺤﻞ
ﺫﺑﻴﺤﺘﻪ، ﻭﻳﺤﻞ ﻧﻜﺎﺣﻪ
Ma'ana: ((A takaice dai: Abin da majoratin masu ilmi suka ce
shi ne duk wanda ya yi Addini da addinin Ahlul kitabi, ya kuma danganta kansa
zuwa gare su koda kuwa yana cewa Allah uku ne, to lallai ne cin wannan yankan
halal ne, kuma auren su halal ne)).
Sa'annan Al Imamul Dabarani, Abul Dar'da, wata an yi masa
Fatawa akan cin Yankan Kirista, suka ce masa Kiristoti ne suka yanka Dabba daga
Coci Suka kawo mana shin ya halatta mu ci? sai da ya girgiza kansa yace Allah
yafe mana, sai ya tambaye su shin su ɗin
ba Ahlul-Qitabbi bane? Sai suka ce ahlul-qitab ne, sai yace ai Abincin su halal ne, sabida haka
cewar ba'a San ya suka yanka ba a Ina suka yanka, duk wannan ba hujja bane na
nuna Haramcin cin sa ba. Kawai in kana Bukata ka ci in ba ka Bukata ka bari,
shikenan shin ba Allah ya halatta mana cin abin Yankan su ba? Mun yi bayanin
Ayar jiya a Dayan Fatawar mu, sa'annan Duk Imanin ka duk Tsarkin ka duk Kyan-Kyamin
ka, shin mun Kai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam ne? Duk Ayar da mutum
zai karanta ko ya fassara ka tsaya ka dubi ya rayuwar Annabi yake?
Har kullum Ahlus Sunnah wal Jama'ah a duk inda suke suna
gina Addinin su ne a kan abin da ya tabbata daga Alkur'ani Mai girma da kuma
ingantattun hadithan Annabi mai tsira da amincin Allah masu daraja. Amma
sabanin su, su kan gina Addinin su ne kawai a kan abin da ya dace da son
zuciyar su.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Fb6qgYPXfEeHb8CD1SWAkK
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.