Hukuncin Matar Da Ta Kashe Mijinta

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamun Alaikum Malam menene Hukuncin matar da ta kashe mijinta, Shin Matar zata gaje shi?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salam warahamtullahi Wabarkatuh

    Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un, Hakika halin da al-umma ta samu kanta a ciki na cin zarafin ma’aurata ta hanyan cutar da abokin zama harma da kisa. Wannan mummunar dabi’a ce da Allah ya haramtawa musulmi mace ko namiji.

    Duk mutumin da ya kashe wani ba zai gaje shi ba, shin miji ne ya kashe matarsa ko matar ce ta kashe mijin ta? Ma-haifi ne ya kashe ɗansa ko ɗan ne ya kashe babansa? Yaya ne ya kashe kaninsa ko kani ne ya kashe yayansa? Mace ce ta kashe namiji ko namiji ne ya kashe mace? To, kowane ne ya kashe wanda zai gada, to baida gadon wanda ya kashe a shari’ance.

    Duniyar musulunci baki ɗaya tayi hukunci da cewa duk wanda ya kashe mutumin da zai gada, to bai da gadonsa. Imam Malik da Ahmad sun ruwaito Hadisi daga Umar (RA) cewa Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam  Ya ce: Wanda ya kashe magajinsa ba shi da gado.

    Magaji bai da gado idan ya kashe mutumin da zai gada, kisan ganganci ne, ko na kuskure ne, ko kuma mai kamar ganganci ne. Bugu da kari ma duk wanda ya kashe wata rai kisan ganganci to, shari’a ta kashe shi kawai, don zaman lafiya. Amma idan kisan kuskure ne, to kisan ta wajabta masa

    1- Biyan diyyar rai: kimanin Naira miliyan hamsin da takawas da wani abu (N58,443,639).

    2- Kaffara azumi sittin.

    3- Haramcin Gado.

    4- Haramcin Wasiyya

    Ya Allah! Ka tsare wannan al-umma daga munanan halaye. Amin

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.