𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Meye Hukuncin Wacce Take Kiran Mijinta Baba Ko Miji Yakira
Matarsa Mama Ko Wasu Kalamai Masu Kama Da Haka
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
الحمد
لله.
Miji yacewa matarsa ke babatace ko ke 'yar'uwatace ko ya mamata
zai iya ɗaukar zihari, zai kuma iya zama ba zihari bane, gwargwadon niyyar
mutum saboda faɗin Annabi sallallahu Alaihi wasallam ( dukkan ayyuka saida
niyya kowanne mutum akwai abunda ya niyyata). Bukhari da muslim
Galibi miji yakan faɗi Waɗannan kalmomin ne abisa tausasawa
matarsa dakuma girmamawa, baya zama zihari, kuma matarsa bata haramta a gareshi
ba.
Ibnu qudamah rahimahullah ya ce: Idan miji yace da matarsa, ke
kamar mahaifiyata kike, ko kamar babata kike, kuma azuciyarsa yana nufin
zihari, to wannan ziharine, a maganar dukkan malamai, amma idan yana nufin
karamcine dakuma girmamawa to ba zihari bane, Almugny (6/8).
hakama dazaice ke babata, ko mamata babata.
An tambayi malaman lajnatul da'ima: wasu mutane suna cewa matayensu
" ni Dan'uwankine kema 'yar'uwatace, menene hukunci?
Sai suka amsa: Idan miji yacewa matarsa ni dan'uwankine kema
'yar'uwatace, ko ke babatace ko ke kamar babata kike, ko ke awajena kamar
babata kike, ko ke kamar 'yar'uwata kike awajena, idan yana nufin karramawa da
kuma girmamawa ko sada zumunci, ko kyakkyawan abu ko kuma bashi dawata niyya
matukar babu wasu ababe dazasu nuna zihari yake nufi, to abunda yafada ba
zihari bane, kuma babu wani abu akansa.
Idan kuma wadannan kalmomin da ire irensu yana nufin zihari
dasune, ko an samu wasu ababe dazasu nuna yana nufin zihari yake nufi kamar
yafurtasu cikin fushi da yayi da ita, ko kuma yana mata kashedi da gargadine sai
ya fadesu, to kalmomin ziharine, taharamta a gareshi, wajibine kuma yatuba
sannan kaffara tawajaba akansa, shi ne ya 'yanta baiwa, idan babu sai yayi
azumi sittin ajere, idan bazai iyaba sai yaciyar da miskinai guda sittin,
fatawa lajnatul da',ima ( 20/274).
Wasu malaman sun karhanta miji yacewa matarsa, ya babata, ko ya
'yar'uwata, saboda hadisin da Abu dauda yaruwaito (2210) Wani mutum yacewa
matarsa ya 'yar'uwata, sai Annabi sallallahu Alaihi wasallam ya ce:
'Yar'uwarkace ita! sai ya karhanta masa hakan yahaneshi.
Amma abunda yake dai dai shi ne babu wani karhanci dan miji
yafadawa matarsa wadancan kalmomin dan girmamawa da karramawa haka itama dan
tagaya masa, saboda hadisin bai ingantaba, Albani ya raunanashi acikin za'ifu
Abu dauda.
An tambayi shaik usaimin rahimahullah cewa: Yahalatta ga miji
ya cewa matarsa, ya 'yar'uwata dan so
kawai, koya babata ko mamata dan so kawai ?
Sai ya amsa: Na'am yahalatta gareshi yace mata ya 'yar'uwata,
ko ya babata ko mamata, dawadanda sukai kama da wannan na kalmomi wadanda suke
sa soyayyah da kauna, koda wasu malamai sun karhanta miji yafadawa matarsa irin
wadannan kalmomi, saidai babu wani dalili na karhancin, saboda dukkan ayyuka
saida niyyah, saboda mutum bai niyyaci cewa 'yar'uwarsace ta haramci ba, ko
maharramiyyah ba, kawai yayi nufin yanuna mata kauna da soyayyane, duk wani abu
dazai janyo kauna da soyayya tsakanin ma'aurata, daka mace ne ko daka namijine,
wannan abune da'akeso kuma ake nema tsakanin ma'aurata.
Dan haka babu laifi cikin wadannan kalmomi dan miji yafadawa
matarsa su ko ita tagaya masa su, amma aguji fadarsu lokacin bacin rai ko fushi,
anan suna iya zama zihari.
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.