𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Menene Hukuncin Barka Da Sabuwar Shekarar Musulunci, Da
Turawa Mutum Sako Kanayi Masa Addu'ar Alkhairi Da Albarka Asabuwar Shekarar
Daya Shiga?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
الحمد
لله.
Shaik Usaimeen rahimahullah yace: Idan wani yafara yi maka
barka da sabuwar shekara ka amsa masa, amma kada kafara yiwa kowa wannan shine
dai-dai awannan mas'alar da wani zaice maka inai maka barka da sabuwar shekara
zakace: masa Inaima barka da sabuwar shekara Allah yabamu alkhairi yasanya mana
albarka acikinta, saidai kada kafara yiwa mutane domin ba'a samu koda mutum ɗaya cikin magabata
Nakwarai sunaiwa juna barka da sabuwar shekarar musulunci ba, Saidaima Su salaf
basa ɗaukar muharram
amtsayin farkon shekarar musulunci, sai azamanin kalifancin Umar bin khaddab
Allah yakara yarda dashi.
Imamu Ahmad bin hambal rahimahullah yace: Bana fara yiwa
koya barka da wani idi cikin idukan musulmai amma idan wani yafara yimun ina
amsa masa domin amsa gaisuwa wajibine, Amma fara yiwa wani barka ba sunnah bace
da'akai Umarni da ita, kuma baya cikin abunda aka hana.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.