Ticker

    Loading......

Hukuncin Zama Da Mijin Da Ba Ya Sallah

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam tanbayana shi ne ina da miji yanzu a haka 'ya'yanmu 3 amma baya sallah. Ba yadda banyi ba idan ya fara sai ya bari amma sallar juma'a baya wuce shi yanzu a haka mahaifina yace zaiyi kararsa ya sake ni tunda baya Sallah to malam in kashe auren ne ko yaya?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Tabbas idan har an yi masa nasiha amma bai ji ba, to bai halatta ki cigaba da zama amatsayin matarsa ba. Domin kuwa akwai sashen Malaman Musulunci dake ganin cewa koda sallah guda ce mutum ya barta da gangan to ya kafirta, balle kuma shi Mijin naki wanda ba ya yin dukkan sallolin ma in banda Juma'a.

Abin lura anan shi ne tun ranar da aka daura aurenku aka damqa masa amanar ciyar dake da tufatar dake, da kuma koyar dake addini. To Mutumin da shi kansa ba ya yin sallah, ta yaya zai koyar dake addini?. Ta yaya zai koya ma 'ya'yanku kulawa da muhimmancin sallah? Cigaba da zama dashi awannan halin zai iya kaiwa zuwa ga lalacewar taki tarbiyyar ma. Kuma zai wahala bai lalata tarbiyyar yaran naku ba.

Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam Ya ce: "SALLAH ITA CE GINSHIKIN ADDINI. WANDA YA TSAYAR DA ITA, TO HAKIKA YA TSAYAR DA ADDINI. WANDA KUMA YA RUSHETA TO HAKIKA YA RUSA ADDINI". Kuma ya faɗa acikin wani hadisin wanda Muslim ya ruwaito : "TSAKANIN MUTUM DA TSAKANIN SHIRKA DA KAFIRCI SHI NE BARIN YIN SALLAH".

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments