𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. Wani malami ne ya ce wai idan mace ta
kashe namiji za a kashe ta, amma idan shi ya kashe ta ba za a kashe shi ba.
Yaya abin ya ke?
𝐀𝐌��𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.
Shi da ya faɗi
maganar ce za a nemi bayani da hujja daga gare shi. Allaah Ta’aala ya ce
قُلۡ
هَاتُوا۟ بُرۡهَـٰنَكُمۡ إِن كُنتُمۡ صَـٰدِقِینَ
Ka ce: Ku kawo hujjojinku in kun kasance masu gaskiya.
(Surah Al-Baqarah: 111; Surah An-Naml: 64)
Kisan kai dai kowa ya san haram ne, saboda maganar Allaah
Ta’aala
وَمَن
یَقۡتُلۡ مُؤۡمِنࣰا مُّتَعَمِّدࣰا فَجَزَاۤؤُهُۥ جَهَنَّمُ خَـٰلِدࣰا فِیهَا وَغَضِبَ
ٱللَّهُ عَلَیۡهِ وَلَعَنَهُۥ وَأَعَدَّ لَهُۥ عَذَابًا عَظِیمࣰا
Kuma duk wanda ya kashe mumini da gangar, to sakamakonsa
Wutar Jahannama ce, yana madawwami a cikinta, kuma Allaah ya yi fushi da shi,
kuma ya la’ance shi, kuma ya yi masa tattalin azaba mai girma. (Surah
An-Nisaa’i: 93).
Kuma Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)
ya ce
« كُلُّ
الْمُسْلِمِ عَلَى الْمُسْلِمِ حَرَامٌ دَمُهُ وَمَالُهُ وَعِرْضُهُ
»
Kowane musulmi a kan musulmi haram ne: Jininsa da dukiyarsa
da mutuncinsa. (Sahih Muslim: 6706).
Sannan kuma ya ƙara cewa
« لَزَوَالُ
الدُّنْيَا أَهْوَنُ عَلَى اللَّهِ مِنْ قَتْلِ رَجُلٍ مُسْلِمٍ
»
Wallahi, gushewar duniya shi ya fi sauƙi a
wurin Allaah fiye da kashe wani mutum musulmi. (At-Tirmiziy: 1455).
Don haka, ba a samun musulmi da wannan laifin sai dai a bisa
kuskure
وَمَا
كَانَ لِمُؤۡمِنٍ أَن یَقۡتُلَ مُؤۡمِنًا إِلَّا خَطَـࣰٔاۚ
Kuma bai kamaci mumini ya kashe wani mumini ba sai dai a
bisa kuskure. (Surah An-Nisaa’i: 92).
Shiyasa malamai suka yi saɓani
a kan tuban mai wannan laifin, kamar yadda Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi
Wa Sallam) ya ce
« كُلُّ
ذَنْبٍ عَسَى اللَّهُ أَنْ يَغْفِرَهُ إِلاَّ مَنْ مَاتَ مُشْرِكًا أَوْ مُؤْمِنٌ قَتَلَ
مُؤْمِنًا مُتَعَمِّدًا »
Kowane zunubi ana fatar Allaah ya gafarta masa sai dai wanda
ya mutu a halin yana mushiriki, ko muminin da ya kashe wani mumini da gangar.
(Abu-Daawud: 4272).
Hukuncin mai kisan kai da gangar a asali shi ne: Qisas,
watau wanda ya yi kisan shi ma a kamo shi a kashe shi, kamar yadda Ubangiji
Ta’aala ya ce
یَـٰۤأَیُّهَا
ٱلَّذِینَ ءَامَنُوا۟ كُتِبَ عَلَیۡكُمُ ٱلۡقِصَاصُ فِی ٱلۡقَتۡلَىۖ ٱلۡحُرُّ بِٱلۡحُرِّ
وَٱلۡعَبۡدُ بِٱلۡعَبۡدِ وَٱلۡأُنثَىٰ بِٱلۡأُنثَىٰۚ فَمَنۡ عُفِیَ لَهُۥ مِنۡ أَخِیهِ
شَیۡءࣱ فَٱتِّبَاعُۢ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَأَدَاۤءٌ إِلَیۡهِ بِإِحۡسَـٰنࣲۗ ذَ ٰلِكَ تَخۡفِیفࣱ مِّن رَّبِّكُمۡ وَرَحۡمَةࣱۗ
فَمَنِ ٱعۡتَدَىٰ بَعۡدَ ذَ ٰلِكَ فَلَهُۥ عَذَابٌ أَلِیمࣱ
Ya ku waɗanda
suka yi Imani! An wajabta muku yin Qisasi a kan kisan kai: Ɗa
domin ɗa, kuma bawa
domin bawa, kuma mace domin mace. (Surah Al-Baqarah: 178).
Sharɗɗan
zartar da qisas, in ji malamai su ne
1. Mai kisan ya zama mukallafi. Domin an ɗauke alƙami
a kan wanda ba mukallafi ba, kamar yaro ko mahaukaci.
2. Ya zama da gangar ya yi kisan. In da kuskure ne to babu
qisas sai dai diyya kawai.
3. Ya zama ya kashe wanda bai halatta a kashe shi ba. Amma
idan ya kashe ridadde ko mazinacin da ya taɓa
aure, ko ɗan fashi
ko ɗan tawayen da
jininsa ya halatta, a nan babu diyya, babu qisasi.
4. Kar ya zama wanda ya yi kisan mahaifi ne ga wanda aka
kashe. Saboda
« لاَ يُقْتَلُ
بِالْوَلَدِ الْوَالِدُ »
Ba a kashe uba domin ya kashe ɗa.
(Ibn Maajah: 2763).
5. Ya zama dukkansu musulmi ne. Domin kamar yadda Annabi
(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya faɗa
« وَلاَ
يُقْتَلُ مُسْلِمٌ بِكَافِرٍ »
Ba a kashe musulmi domin ya kashe kafiri. (Sahih
Al-Bukhaariy: 111)
6. Haɗuwar
waliyyan mamacin a kan qisasin. Domin in aka samu ko da mutum ɗaya bai amince da qisas
ba, to ba za a tsayar masa da shi ba.
7. Wannan shi ne abin da na sani daga bayanan malamai a kan
wannan mas’alar. Watau Babu bambanci a tsakanin mace da namiji a nan
Ana kashe mace don ta kashe namiji, haka kuma ana kashe
namiji don ya kashe mace.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
08021117734
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.