TAMBAYA (59)❓
Malam dan Allah idan ina son wani xan iya yin addu'a cewa
Allah yasa wane ya zamo alkhairi agare ni?ya zamo miji nagari a gare ni?
Ba tare dana bi son zuciya ta ba
AMSA❗
Addua ibada ce kuma ba laifi bane ka yi ta idan har kaji
wani ya kwanta maka a rai amman kamar yanda muka sani cewar addinin musulunci
ya koyar damu komai sai mu koma hadisin Annabi SAW mu ji wacce shawara ya bada
ga wanda yake son wani ko wata
Ya tabbata a cikin sahihin hadisi (Da littafin Hisnul
Muslim) cewar Annabi SAW yana koyawa sahabbansa Addu'ar Sallar Istihara (Neman
Zabin Allah Idan Mutum Zai AikaTa Wani Abu)
Jabir Ibn Abdullah, Allah ya yarda da shi da mahaifinsa, ya
ce; Manzon Allah (SAW), tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya
kasance yana koya mana yin istihara (neman zabin Allah) a Cikin dukkan al'amura
kamar yadda yake koya mana sura daga Cikin Alkur'ani, yakan ce, "Idan
dayanku ya yi niyyar yin wani al'amari to ya yi sallah raka'a biyu ba ta
farilla ba, sannan ya ce;
اَللَّهُمَّ
إِنِّي أَسْتَخِيرُكَ بِعِلْمِكَ، وَأسْتَقْدِرُكَ بِقُدْرَتِكَ، وَأَسْألُكَ مِنْ
فَضْلِكَ الْعَظِيم، فَإِنَّكَ تَقْدِرُ وَلا أَقْدِر، وَتَعْلَمُ وَلا أَعْلَم، وَأَنْتَ
عَلاّمُ الغُيوبِ، اللّهُمَّ إِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا اْلأَمْرَ- وَيُسَمِّي
حَاجَتَهُ - خَيْرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، عَاجِلِهِ وَأَجِلِهِ
فَاقْدُرْهُ لِي وَيَسِّرْهُ لِي ثُمَّ بَارِكْ لِي فِيهِ، وَإِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ
أَنَّ هَذَا اْلأَمْرَ شَرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، فَاصْرِفْهُ
وَاصْرِفْنِي عَنْهُ وَاقْدُرْ لِي الْخَيْرَ
حَيْثُ كَانَ ثُمَّ أَرْضِنِي بِهِ.
Allahumma innee astakheeruka bi'ilmik, wa-astaqdiruka
biqudratik, wa-as-aluka min fadlikal-'azeem, fa-innaka taqdiru wala aqdir,
wata'lamu wala a'lam ,wa-anta 'allamul ghuyoob, allahumma in kunta ta'lamu anna
hazal-amr (sai ki fadi sunan wanda kike so din) khayrun lee fee deenee
wama'ashee wa'akibati amree fakqurhu lee, wayassirhu lee, thumma barik lee
feeh, wa-in kunta ta'lamu anna hazal-amr (sai ki fadi sunansa) sharrun lee fee
deenee wama'ashee wa'aqibati amree fasrifhu 'annee wasrifnee 'anh, waqdur liyal-khayra
haythu kan, thumma ardinee bihi.
Ya Allah ! Ina neman zabinka domin iliminka, kuma ina neman
Ka ba ni iko domin Ikonka, kuma ina rokonka daga falalarka Mai girma; domin Kai
ne mai iko ni kuwa ba ni iko, kuma Kai ne Masani, ni kuwa ban sani ba, kuma Kai
ne masanin abubuwan fake. Ya Allah! Idan ka san cewa wannan al'amari sai ya
ambaci bukata tasa alheri ne gare ni a cikin addinina, da rayuwata, da kuma
karshen al'amarina a wata rayuwar; da magaggaucin ala'marina da majinkircinsa
Ka kaddara mini shi, kuma Ka saukake mini shi, sannan Ka albarkance ni a cikin
sa. Kuma idan Ka san wannan al'amari sharri ne gare ni a cikin addinina, da
rayuwata da karshen al'amarina a wata ruwayar; da magaggaucin al'amarina da
majinkircinsa – Ka kawar da shi daga gare ni, kuma Ka kawar da ni daga gare shi, kuma Ka kaddara
mini alherin a duk inda yake, kuma Ka sanya ni in yarda da shi".
Duk wanda ya nemi zabin mahalicci, kuma ya yi shawara da
talikai muminai, kuma ya yi azama a Cikin lamarinsa, to ba zai yi nadama ba, domin
Allah madaukakin sarki Ya ce;
(وَشَاوِرْهُمْ
فِي اْلأَمْرِ فَإِذَا عَزَمْتَ فَتَوَكَّلْ عَلَى اللهِ)
"Kuma ka shawarce su cikin lamarinka, idan kuma ka
kuduri aniya, to ka dogara ga Allah".
Kinga kenan a shawarce sai ki bincika halayyarsa idan yana
da addini da kyakkyawar iya mu'amala da mutane shi kenan ba abin kunya bane ki
fada masa kina son sa, saboda Nana Khadija RA ita ta buqaci auren Annabi SAW
sabida kyawawan halayensa
Ina fatan idan shine alkhairi a gare ki - Allah ya baki shi,
akasin haka kuma Allah ya musanya miki da wanda yafi alkhairi
Wallahu ta'ala a'alam
Amsawa;
Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.