Ingancin Hadisin Sallar Ranar Juma'ar Karshen Watan Ramadan

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malan dafatan antashi lfy ya ibada, Allah yasa karbebbiyace ameeen. Malam dan Allah mene ne gaskiyar wannan hadisin? 👇

SALLAR FANSAR SALLOLI: Aranar juma'ar karshen watan ramadan Wannar Sallar Wanda yayita awannan ranar zata fanshi sallolinshi dabasu cikaba ta shekara dubu Imam Ali (A) shine yaruwaito daga manzan Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) da aka tambayi manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam akan mutun baya wuce shekara 60 zuwa 70 sai yace sauran shekarun zasu fanshi iyayenshi, matarshi, yan uwanshi dama mutanen garinsu. YADDA AKEYIN SALLAR: raka,a 4 kowace raka'a fatiha 1 inna anzalnahu 15 inna A'adaina 15 bayan sallama sai salatin annabi sau 100 Sannan Wanda yayi wannar addu'ar tozai haɗu da dayan biyu kode Allah yatsawaita rayuwarshi har yakai wata shekarar ko kuma ya kafartamasa in ya mutu

ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻻ ﺗﺠﻌﻠﻪ ﺃﺧﺮ ﺍﻟﻌﻬﺪ ﻣﻦ ﺻﻴﺎﻣﻨﺎ ﺇﻳﺎﻩ، ﻓﺎﺀﺟﻌﻠﺘﻪ ﻓﺎﺟﻌﻠﻨﻲ ﻣﺮﺣﻮﻣﺎ، ﻭﻻ ﺗﺠﻌﻠﻨﻲ ﻣﺤﺮﻭﻣﺎ .

Ana yin wannar Sallar daga bitowar ranar zuwa zawalinta, dan Allah Wanda yasamu yataimaka wasuma susamu wslm

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To Bayin Allah wannan sallar bata tabbata a sunnah ba sabida haka yin sallar bidi'a ne. An yiwa kwamitin fatawa na malaman duniya dake saudiyya Tambaya game da ingancin waccan sallar ta ranar juma'ar karshen watan ramadan, Sai suka bada amsa da cewa: Sallar bata tabbata daga Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ba kuma ba'a sameta daga sahabbai da tabi'ai dasauran magabata na kwarai ba, Lallai ita sallar 'kir'kirarriyar sallah ce sabida haka bidi'a ce kuma Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yace: Duk wanda ya 'kir'kiro wani abu ya shigo dashi cikin addini kuma abin ba daga garemu yake ba to shi abin cillarwa ne wato an mayarmasa dashi baza'a karɓa ba.

...

Hakanan an yiwa babban malami Shiek Uthaymeen Rahimahullah Tambaya game da ingancin waccan sallar Sai ya bada amsa da cewa: Ita sallar bidi'a ce domin bata da asali a cikin addini, Yin sallarma yana iya nisanta mutum daga ubanginsa Sabida Faɗin Annabi Sallallahu alaihi Wasallam cewa: Dukkan bidi'a ɓata ce dukkan ɓata kuma yana wuta, kuma duk yadda masu yin sallar suke ganin cewa yin sallar abune me kyau a tunaninsu, to lallai kuwa ita wata a bace mara kyau sabida faɗin Annabi Sallallahu alaihi Wasallam cewa: Duk wanda ya 'kir'kiro wani abu ya shigo dashi cikin addini kuma abin ba daga garemu yake ba to shi abin abin cillarwa ne wato an mayarmasa dashi baza'a karɓa ba.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RƘbbrzgW

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments