Jollof Din Doya Da Jollfo Din Dankalin Turawa Da Kwai

    Dafa-Dukan Doya

    Kayan haɗin da za a tanada su ne:

    i. Doya

    ii. Gishiri

    iii. Kayan miya

    iv. Ruwa

    Ita ma wannan dafa-duka kamar yadda ake yin sauran dafa-duka haka za a yi ta. Inda suka bambanta da sauran shi ne, ba a saka mata wasu ganyaye. Haka nan za a dafa ta tare da da kayan miya haɗi da gishiri. Haka kuma ana iya dafa doyar ita kaɗai ba tare da an saka mata komai a cikinta ba; wato ko fere doya ba za a yi ba. Da zarar an farfasa ta, haka nan za a saka ta a cikin tukunya tare da gishiri da ruwa, a dafa.

    Dafa-Dukan Dankalin Turawa da Ƙwai

    Kayan haɗin da za a tanada su ne:

    i. Albasa

    ii. Dankalin Turawa

    iii. Gishiri

    iv. Kayan ciki

    v. Kayan yaji

    vi. Kori

    vii. Magi

    viii. Mai

    ix. Ƙwai

    x. Ruwa

    xi. Tafarnuwa

    xii. Tarugu

    xiii. Tattasai

    xiv. Tumatur

    Za a fere dankali a wanke shi, sai a saka mashi gishiri a sama a dafa shi shi kaɗai. Kada a bar shi ya nune sosai. Da zarar ya ɗan nuna sama-sama, sai a fitar da shi a tace da kwando a rufe. Daga nan sai a jajjaga tumatur da tattasai da tarugu da albasa a aje gefe ɗaya. Sannan a daka kayan yaji a saka a cikin jajjagen. Bayan nan za a wanke kayan ciki sosai a saka magi da albasa da kori. Kada a saka ruwa a cikin tafasa, zai tafasa da sauran ruwan da ke ciki. Za a soya mai a cikin tukunya a saka albasa, idan ya soyu a kawo jajjagen kayan miya a saka, a yi ta juya su sai sun soyu sosai. Bayan sun soyu, za a ɗauko kayan cikin nan da aka tafasa a saka a ci gaba da juyawa. Sannan a ɗauko ƙwai a fasa gwargwadon yadda ake buƙata a kaɗe shi sosai a saka yankakken tarugu da dakakkiyar tafarnuwa a zuba a cikin kayan ciki da jajjage a ci gaba da juyawa har sai ya fitar da mai. Za a ɗauko dankalin nan a saka shi ciki, a riƙa juyawa a hankali har sai ya haɗe, sai a jaye wuta saboda kar ya farfashe a ciki. Da zarar ya ƙarasa, to dafa-dukan dankalin Turawa da ƙwai ta kammala.

    The book “Cimakar Bahaushe” (Diets of the Hausa People) is a collection of 293 traditional and modern diets of the Hausa people. Detailed explanations of the recipes and ingredients are provided. Comments are provided on the areas of the Hausa land where specific diets are mostly found, the age categories of people that usually use it, as well as the scientific impact of some of the diets to human biology.  Data is collected from interviews with different categories of people including:  i.                    Food sellers within the Hausa land: Mainly to have an idea of recipes on the diets.  ii.                  People of older age: Mainly to have insights on traditional diets of the Hausas.  iii.               Hausa scholars: Mainly to verify and justify the validity of the information obtained as well as provide further expert explanations on the diets.  Moreover, over two hundred (200) pieces of literature were reviewed to have better insight on the topic in question as well as get scientific and professional clarifications on some key concepts relevant to the research. The pieces of literature cover major relevant phenomena such as diet and hunger. Others are on the Hausa land and the Hausas.  The book contains thirty-three (33) chapters. Chapter one is the main introduction in which a concise explanation is provided on the Hausas, their history, their land, social life, and transformations due to globalization, acculturation, and modernity. Chapter two detailly discusses the concepts of diet and food from the Hausa point of view. That includes the meaning and the usage of diets in some Hausa works of literature both verbal and written (i.e. prose, poetry, proverbs, etc.).  Chapters three and four discuss the sources of Hausa diets and their forms accordingly. Chapters five to seventeen discuss some traditional Hausa diets including hard and soft ones. Chapter eighteen concentrates on the influence of modernity and globalization on Hausa diets. It has been discovered that there have been some significant changes in the Hausa diets ranging from recipes to kitchenettes.  Chapters nineteen to thirty-two discuss modern Hausa diets. Some traditional diets are still retained with little modifications, while on the other hand, there are a lot of new ones. Chapter thirty-three discusses “hunger” from the Hausa point of view. The relationship between hunger and food is examined. Additionally, the use of hunger in various Hausa literary works is studied. It is concluded that hunger is like a disease whereby its cure is food.  7th November 2022
    Citation (Manazartar Littafin): Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

    Get a copy:
    To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
    +2348133529736

    You can also write an email to:

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.