Jollof Din Shinkafa Da Taliya, Jollof Din Shinkafa Da Ganye, Jollof Din Shinkafa Da Doya

    ShimfiÉ—a

    A babi na tara, an kawo bayanai a kan dafa-duka amma a gargajiyance. Zamani ya zo da sauye-sauye daban-daban a wannan nau’in abinci na dafa-duka. Wasu daga cikin sauye-sauyen sun shafi kayan haÉ—in abincin ne kawai. A nan, ana nufin nau’ukan kayayyakin sarrafa dafa-duka, misali kayan É—anÉ—ano da na Æ™amshi. A É“angare guda kuwa, akwai sababbin nau’o’in dafa duka na zamani da suka zo wa Bahaushe. Ya same su ne daga baÆ™in al’ummu da ya yi cuÉ—anya da su. Wannan babi na ashirin da uku zai bibiyi waÉ—annan nau’o’in abincin na dafa-duka da ke Æ™unshe da tasirin zamani.

    Dafa-Dukan Shinkafa da Taliya

    i. Albasa

    ii. Gishiri

    iii. Kayan yaji

    iv. Magi

    v. Mai

    vi. Nama

    vii. Ruwa

    viii. Shinkafa

    ix. Taliya

    x. Tarugu

    xi. Tattasai

    xii. Tumatur

    Dafa-dukan shinkafa da taliya ita ma haka za a yi ta kamar wadda ta gabata. Sai dai za a tafasa nama da albasa kafin a saka shi a cikin sanwa. Haka ma, idan za a saka taliya sai an zuba dafaffiyar shinkafa daga baya a saka taliya.

    Dafa-Dukan Shinkafa da Ganye

    i. Alayyafu

    ii. Albasa

    iii. Ganda

    iv. Gishiri

    v. Kayan yaji

    vi. Magi

    vii. Mai

    viii. Ruwa

    ix. Shinkafa

    x. Tarugu

    xi. Tattasai

    xii. Tumatur

    xiii. Zogale

    Wannan dafa-duka ita ma kamar yadda aka yi ta wake haka za a yi ta. Sai dai a wurin ganda za a tafasa ta da gishiri da albasa sosai kafin a saka ta bayan an yi sanwa. Shi kuma zogale za a murje shi sosai a saka cikin sanwa saboda ya nuna sosai. Daga nan, sai a saka shinkafa. Idan alayyafu ne, sai an saka shinkafa sannan a saka alayyafu.

    Dafa-Duka Shinkafa da Doya

    i. Albasa

    ii. Doya

    iii. Gishiri

    iv. Kayan yaji

    v. Kukumba

    vi. Magi

    vii. Mai

    viii. Ruwa

    ix. Shinkafa

    x. Tarugu

    xi. Tattasai

    xii. Tumatur

    Ita ma dafa-dukan shinkafa da doya akan yi ta ne kamar sauran da aka yi bayani a sama. Bayan nan, ita ma doyar za a fere ta a ajiye gefe. Sai dai idan za a saka shinkafa tare za a saka su. Idan ana buÆ™ata za a iya yayyanka kukumba a saka a ciki.

    NaÉ—ewa

    Dafa-duka abinci ce da ta tara abubuwa da yawa, kamar dai yadda aka ga bayanin a sama. Akwai wasu nau’o’in dafa-duka da za a iya samu a Æ™asar Hausa bayan waÉ—annan, musamman da yake kullum sababbin ilimomi na Æ™ara zuwa ga al’umma a fannonin rayuwa daban-daban, ciki har da yadda suke samar da abincinsu na yau-da-kullum.

    The book “Cimakar Bahaushe” (Diets of the Hausa People) is a collection of 293 traditional and modern diets of the Hausa people. Detailed explanations of the recipes and ingredients are provided. Comments are provided on the areas of the Hausa land where specific diets are mostly found, the age categories of people that usually use it, as well as the scientific impact of some of the diets to human biology.  Data is collected from interviews with different categories of people including:  i.                    Food sellers within the Hausa land: Mainly to have an idea of recipes on the diets.  ii.                  People of older age: Mainly to have insights on traditional diets of the Hausas.  iii.               Hausa scholars: Mainly to verify and justify the validity of the information obtained as well as provide further expert explanations on the diets.  Moreover, over two hundred (200) pieces of literature were reviewed to have better insight on the topic in question as well as get scientific and professional clarifications on some key concepts relevant to the research. The pieces of literature cover major relevant phenomena such as diet and hunger. Others are on the Hausa land and the Hausas.  The book contains thirty-three (33) chapters. Chapter one is the main introduction in which a concise explanation is provided on the Hausas, their history, their land, social life, and transformations due to globalization, acculturation, and modernity. Chapter two detailly discusses the concepts of diet and food from the Hausa point of view. That includes the meaning and the usage of diets in some Hausa works of literature both verbal and written (i.e. prose, poetry, proverbs, etc.).  Chapters three and four discuss the sources of Hausa diets and their forms accordingly. Chapters five to seventeen discuss some traditional Hausa diets including hard and soft ones. Chapter eighteen concentrates on the influence of modernity and globalization on Hausa diets. It has been discovered that there have been some significant changes in the Hausa diets ranging from recipes to kitchenettes.  Chapters nineteen to thirty-two discuss modern Hausa diets. Some traditional diets are still retained with little modifications, while on the other hand, there are a lot of new ones. Chapter thirty-three discusses “hunger” from the Hausa point of view. The relationship between hunger and food is examined. Additionally, the use of hunger in various Hausa literary works is studied. It is concluded that hunger is like a disease whereby its cure is food.  7th November 2022
    Citation (Manazartar Littafin): Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

    Get a copy:
    To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
    +2348133529736

    You can also write an email to:

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.