Kacici-Kacici A Faifan Nazari: Tambayoyi Hamsin (50) Da Amsoshin Su

     Takardar ƙara wa juna sani da aka gabatar a ajin ALH 400: Seminars, a Sashen Nazarin Harsuna Da Aladu, Jamiar Tarayya Gusau, Nijeriya, (2022/2023 Academic Session).

    Federal University Gusau (FUG) Nigeria

    Kacici-Kacici A Faifan Nazari: Tambayoyi Hamsin (50) Da Amsoshin Su

    NA

    ILIYASU MUSA

    G.S.M NUMBER: 08068482478

    gmail: iliyasumusa201744@gmail.com

    TSAKURE

    Wannan bincike ya mayar da hankali ne kacokam a kan kacici-kacici a harshen Hausa.Wannan fanni na adabin baka, ɗaya ne daga cikin ƙananan rassa na maganganun hikima da sarrafa harshe. Manufar wannan bincike ita ce domin asamar wa yara kanana da masu nazarin harshen Hausa wani rumbu da za a adana ma su waɗannan maganganun hikima don gudun ɓacewar su a nan gaba. Kacici-kacici dai wasu ‘Yan guntayen jimloli ne ko dogaye da ake amfani da su ta hanyar yin tambaya sai a bukaci wani ko wasu da su gane amsar. Ana yin haka ne da zimmar ƙara zurfin tunani, nishaɗantarwa, raya al’adun Hausawa tare da sanin sunayen abubuwan da ke kewaye da su. Wannan bincike ya gano cewa akwai hasashen cewa nan da ‘yan shekaru masu zuwa wannan fanni na kacici-kacici na iya ɓacewa. Bisa ga haka ne wannan muƙala ke bayar da shawarar cewa masu ruwa da tsaki da su tashi tsaye, tsayin daka wajen ganin sun kundace wannan fannin, duba da irin rawar da yake takawa wajen raya adabi.

    1.0     GABATARWA

    Baya ga samar da nishaɗi tare da ilmantarwa, kacici-kacici ya zama wata babbar ma’adana inda ake adana rumbun kalmomi waɗanda banda ta hanyar tatsuniyoyi ko irin waɗannan mutum ba zai ji ana yin amfani da su sosai ba. Bugu da kari, kacici-kacici na koyar da wani abu wanda yake muhimmi ne a halin rayuwar dan Adam. Wannan abu kuwa shi ne, Hausawa sukan ce wai ba kullum akan kwana a kan gado ba. Wato idan yau kai ne, to gobe ba kai ne ba; sai wani. Wannan kuwa na fitowa ne ta hanyar ‘’ Na ba ka gari’’. Yayin da waɗanda ake yin kacici-kacici da su ba su canki amsar ba, sukan ce ‘’ Na ba ka gari’’. Wannan na nuna cewa dai mutum ba zai iya sanin komai na duniya ba. Saboda haka yayin da duk aka tambaye shi abin da bai sani ba, ba tare da jin kunya ko nauyi ba, zai ce ‘’ Na ba ka gari’’. Haka kuma yayin da duk bai san wani abu ba, ba a bin da ya kamata ya yi fiye da ya tambaya a gaya masa.

    Kacici-kacici tamkar wata makaranta ce ta farko a gargajiyance wadda take koya wa yara tafarkin rayuwa. Misali da jin ma’anar ‘’ Tsohuwar gidanmu kullum zata fita sai ta raba muna goro’’ wato kashin awaki’’. A nan mutum zai iya gane cewa Hausawa mutane ne masu yin kiwon dabbobi. Daga ƙarshe dai makasudin binciken shi ne a farfado da wannan hanya ta ilimantar da ‘ya’yan Hausawa tare da kundace wannan kafa don gudun ɓacewarta baki daya.

    1.1DABARUN BINCIKE

    A wannan bincike an yi amfani da tsarin tsurar bayani ne wato (Qualitative form of research). An yi amfani da babbar hanyar tattara bayanai daga tushe na farko wato (primary source). Da kuma babbar hanyar tattara bayanai daga majiya ta biyu wato (secondary source). Inda aka binciki rubuce-rubucen magabata, musamman bugaggun littaffai a ɗakunan karatu.

    2.0 MA’ANAR KACICI-KACICI A BAKIN MASANA

    Kacici-kacici yana ɗaya daga cikin zantukan hikima wanda yake raya adabin baka na Hausa,ko a can da kacici-kacici yana da matuƙar muhimmanci ga adabin Hausa, musamman idan aka yi la’ari da irin rawar da ya ke takawa wajen ilmantarwa, nishaɗantarwa, da samar da rumbun kalmomi tare da raya al’adun Hausawa. Ga wasu daga cikin ra’ayoyin masana game da ma’anar kacici-kacici.

    Muhammad,Y.M (2015:94) a cikin littafinsa mai suna Adabin Hausa ya bayyana kacici-kacici da cewa waɗansu gajerun zantuka ne na azanci wadanɗa sukan zo a cikin jimloli ɗai-ɗai, ko jeren jimloli masu siffanta abin nufi guda ɗaya.

    Dangambo A. (1984:40) A littafinsa mai suna Rabe-raben Adabin Hausa da muhimmancinsa ga rayuwar Hausawa ya ce ‘’ kacici-kacici ya ƙunshi hikima da sarrafa harshe. Ana siffanta wasu kalmomi da ma’anarsu a sa mutum ko yaro ya yi ƙoƙari, ya danganta kalmomin da aka bayyana da ma’anarsu, ya kuma gano su.

    Owomoyela (1996:42) Says ‘’Riddles are a form of verbal art that pose a question to an audience, challenging them to find the correct answer by utilizing their knowledge, logic,and intuition’’.

     Owomoyela (1996:42) Ta ce kacici-kacici wata maganar hikima ce da ake tsarawa ta hanyar yin tambaya ga masu saurare domin su gano amsar a ilmance tare da amfani da kaifin tunaninsu

    Wasu masanan na ganin cewa ‘’kacici-kacici tatsuniya ce wadda ake shiryawa domin auna fahimtar yara. Ana aiwatar da ita ne ta hanyar sakaya sunan wani abu amma sai a fadi wata sifa ta sa, daga baya a nemi yaro ya gane mene ne.

     Duba da wadannan ra’ayoyi na masana, ni ma a tawa fahimta ina da ra’ayin cewa kacici-kacici wani salo ne na yin tambaya nan take a bayar da amsa a tsakanin yara don ƙara kwarewa da harshe.

    2.1 ASALIN KACICI-KACICI

    Kamar yadda Muhammad Y.M (2015:93) Ya faɗa a cikin littafinsa mai suna Adabin Hausa inda ya nuna da cewa asalin Kalmar kacici-kacici daga Kalmar ‘’cinta ce’’ wato kintaci fadi. Yara biyu sukan yi wa juna wasa da canki. Ta yadda sukan yi haka kuwa shi ne, ɗaya yakan rufe wani abu, misali kwabo, a tafin hannunsa ya ce wa ɗayan ya cinka, wato ya yi kirdado ya faɗi abin da ya rufe a hannunsa. Siffar tambayar takan zo ne kamar haka. Kacici-kacici, me ye a hannuna? Shi kuma wanda aka tambaya, zai yi ta kokari ne ya ambaci abin da tafin tafin hannun zai iya damƙewa ya rufe ruf, ba tare da ana ganinsa ba. Kuma zai yi ta tuntuno da abubuwan da ake ma’amala da su ne yau da kullum, misali kamar tsabar kuɗi, da wasu abubuwa na ci kamar goro, ko gyaɗa, ko abubuwan wasa kamar tsakuwa, da sauransu.

    2.2 NAU’O’IN KACICI-KACICI

    A wannan muƙala an kasa nau’o’in kacici-kacici zuwa gida huɗu,kamar haka

    1 kacici-kacici da aka gina a kan siffa

    2 Kacici-kacicin ɓoyo (sakayawa)

    3 Kacici-kacici mai sauti

    4 Kacici-kacici mai kirari

    I Kacici-kacici da aka gina a kan siffa: Irin wannan tambaya ce ko bayani wanda a cikin ta aka siffanta wani abu. Shi abin da aka siffanta ɗin nan mutum zai kasance mai sauƙin ganewa ne, da zaran dai ya yi ɗan gajeren tunani, zai iya gane abin da ake nufi. Misali idan mai kacici-kacici ya ce ‘’Waina a dawa’’ amsar wannan ita ce ‘’Kashin shanu’’.

     Da zarar mutum ya san kashin shanu, ya kuma san waina, to zai san cewa dai an gina wannan kacici-kacicin ne ta hanyar siffantawa. haka kuma kamar irin su: Shirin ba ci ba’’Wato ‘’baba’’ da dai sauransu.

    II Kacici-kacicin ɓoyo (sakayawa):- Ita ma irin wannan takan zo ne kamar sauran zantuka, ko bayanai waɗanda idan mutum ya ji zai iya gane ma’anar su; amma maimakon abar su a haka a fili, sai akan yi dabara a ɗan ɓoye su don a ruɗa mutun. Misali : ‘yar burguma da fata goma. Amsar it ace ‘’albasa’’

    III kacici-kacici mai sauti :-

    Irin wannan tambaya ce ko bayani wacce ta kunshi sauti ko murya ta musamman wacce daga muryar ko sautin mutun na iya cankar amsar. Misali

    Daga nesa na ji muryar ƙawata. wato ‘’ganga’’ An dai san ganga na da ƙara kuma mutum na iya jin ƙararta daga nesa. Haka kuma akwai wannan, misali

    Bullum bar bullum bullum na bulloji. Haka ma da jin wannan sauti mutum na iya hasashen cewa, kaza bari ƙoto shaho na kallon ki.

     Kamar yadda ɗillin ta kan yi ɗillin hakanan ma ɗillin takan yi ɗillin. Shi ma wannan sautin mutun na iya hasashen shi da cewa, kamar yadda kaza takan yi ƙwannan hakanan ma ƙwan yakan yi kaza.

    IV Kacici-kacici mai kirari:-

    Irin wannan kacici-kacici yakan zo ne ta fannin kirari ko yabo. Anan akan dauki wani abu ne a kambama shi da nufin yabon abin don muhimmancinsa ga rayuwar Ɗan-adam. Misali masu kacici-kacici sukan ce. ‘’Tsumagiyar kan hanya fyaɗi yaro fyaɗi babba’’ wato ‘’yinwa’’ wannan ba kowa ake wa kirari ba ban da ‘’yinwa’’. Daga jin wannan idan mutum bai sani ba zai tsammaci cewa wani abu ne muhimmi.

     2.3 LOKACIN DA AKE YIN KACICI-KACICI

    Ana yin kacici-kacici ne lokacin hutawa, kuma a cikin raha watau a cikin wasa da dariya. Kacici-kacici dai da daddare ake yin sa, amma idan ana son a yi da rana ko wani lokaci da yake ba dare bane, to ana iya ɗaure gizo, sannan a fara. Muhimmancin abin da ya kamata a yi la’akari da shi, dangane kacici-kacici, shi ne an fi yin sa da dare bayan kamala cin abincin dare. Domin shi kacici-kacici abin raha ne da hutawa. Hausawa kuma na cewa wai ‘’ Dare mahutar bawa’’. A she in haka ne kuwa ba wani lokacin da ya fi dare dacewa ayi.

     2.4 YADDA AKE YIN KACICI-KACICI

    Yayin da ake wannan hutawa, yara sukan share fagen tatsuniyoyi ko labarum raha da kacici-kacici.

     Wani lokaci kuma akan yi kacici-kacici ne yayin da ake yin tatsuniyoyi da sauran raha, idan an fara gajiya sai a jefo kacici-kacici don a dan shakata. A wasa ƙwaƙwalwa, a kuma bar mai yin tatsuniyar ko labaran ya dan huta.

     Wani lokaci ma akan zauna ne kawai don shi kacici-kacicin kawai don wasa ƙwaƙwalwa.

     3.0 WURIN YIN KACICI-KACICI

    Akan yi kacici-kacici ne a wurare kamar haka

     1 Gidan amarya ko gidan biki

     2 Yayin da yara suka taru a dandali don wasa

     3 Tare da kakanni mata a gida

    3.1 MASU YIN KACICI-KACICI

    Kacici-kacici dai ana iya cewa a taƙaice, wasan yara ne, don yara aka fi sani na yin shi. Amma wani lokaci akan samu manya na yi, musamman mata.

     3.2 MUHIMMANCIN KACICI-KACICI

     Kacici-kacici na da matuƙar muhimmanci, duba da irin gagarumar gudummuwar da yake bayarwa ga yara ƙanana

    1 Koyar da dubarun zaman duniya da ƙara masu kaifin tunani

    2 Samar da nishaɗi

    3 Bunƙasa harshe

    4 Sanin abubuwan amfani da ke kewaye da yara na gida da waje

    5 Sanin al’adun al’uma

    6 Iya sarrafa kalmomi d.s

     3.3 DARUSSAN CIKIN KACICI-KACICI

    Shi dai wannan salon Magana na kacici-kacici wanda galibi yara da samari, kai har ma da waɗanda manya ke yi din, suna da matukar amfani wajen nuna zurfin hikimomi da harshen Hausa ya ƙunsa.

     Ga wasu daga cikin darussan kamar haka

    I Kacici-kacici na sanya tunani ga masu yinsu, sai a gano abin nufi wanda aka ƙudundune a cikin zuzzurfar Hausa.

    II Kacici-kacici na sa yara su san sunayen waɗansu abubuwa a cikin al’adunsu.

    III Kacici-kacici na koyar da gasa, da son mutum ya nuna bajinta wajen amsa tambayoyin da aka yi masa

    IV Kacici-kacici na ƙara danƙon zumunta da haɗa kan yara tsakaninsu, domin ana yin su ne a dandali wurin haɗuwar abokai da sauransu.

    3.4 MISALAN KACICI-KACICI GUDA HAMSIN ‘50’ DA AMSOSHINSU

    1 Tambaya: Ƙulinƙulibita

    Amsa: Gauta

    2 Tambaya: Matar ƙuilbita

    Amsa: Yalo

    3 Tambaya: Kututturu uku gagara ɗauri

    Amsa: Ƙwai

    4 Tambaya: Abu siriri abu zarara, abu tufkar Allah

    Amsa: Gashi

    5 Tambaya: Tsohuwar gidanmu ta ƙwarƙwashe ta na roƙon Allah

    Amsa: Rumfa

    6 Tambaya: Bullum bar bullum, bullum na bulloji

    Amsa: Kaza bar tono shaho na kallonki

    7 Tambaya: Gwanda lili da liyo

    Amsa: Gwanda noma da awo

    8 Tambaya: Kurkucir kucif

    Amsa: Kwanciyar kare

    9 Tambaya: Ɗan tsako da linzami

    Amsa: Allura da zare

    10 Tambaya: Waina a dawa

    Amsa: Kashin shanu

    11 Tambaya: Angulu bisa kuka uku

    Amsa: Tukunya

    12 Tambaya: Ana haya haya kutukku na tsaye

    Amsa: Turmi

    13 Tambaya: Ƙato tsakar gida ba wando

    Amsa: Turmi

    14 Tambaya: Kaɗata feffeffes amma babu mai iya taɓa ta

    Amsa: Taurari

    15 Tambaya: Ɗakin samari ba ƙofa

    Amsa: Ƙwai

    16 Tambaya: Gungume uku baya ɗauro wuri ɗaya

    Amsa: Ƙwai

    17 Tambaya: Kamar yadda ɗillin takan yi ɗillin haka ma ɗillin yakan yi ɗillin

    Amsa: Kamar yadda kaza takan yi ƙwannan haka ma ƙwan yakan yi kaza

    18 Tambaya: Da dodo da bado da badoduwa

    Amsa: Da rana da wata da tauraruwa

    19 Tambaya: Takalmin kitse maɗauki na wuta

    Amsa: Kunama

    20 Tambaya: ‘‘Yar burguma da fata goma

    Amsa: Albasa

    21 Tambaya: Abu ɗan ɗil ya sa mai gari sauka bisa doki

    Amsa: Fitsari

    22 Tambaya: Shanuna dubu dubu maɗaurarsu ɗaya

    Amsa: Tsintsiya

    23 Tambaya: Shanuna dubu dubu amma ‘yar ƙaramarsu ta fi su zaƙin nono

    Amsa: Rakke (takanɗa)

    24 Tambaya: Shanuna dubu dubu in suka wuce babu mai ganin ƙurarsu

    Amsa: Turwa

    25 Tambaya: Gari ɗaka yara kwana da yinwa

    Amsa: Toka

    26 Tambaya: Ga fili fallau amma babu mai damar yin ƙwallo

    Amsa: Sararin sama

    27 Tambaya: Tsohuwar gidanmu kullum wanka amma ƙara baƙi take

    Amsa: Guga

    28 Tambaya: Na gina taƙi ginuwa na rufe taƙi rufuwa

    Amsa: Inuwa

    29 Tambaya: Na wanke ‘yar ƙwaryata na je makka da madina na dawo ba ta bushe ba

    Amsa: Hancin kare

    30 Tambaya: Baƙar bakambara ratsa gidan sarki

    Amsa: Daidawa

    31 Tambaya: Iya ta zagaya baba ya zagaya amma basu haɗu ba

    Amsa: Kunnuwa

    32 Tambaya: ‘‘Yar tsohuwar gidanmu kullum wanka

    Amsa: Randa

    33 Tambaya: Abu siriri siriya abu da ginar ƙasa

    Amsa: Fitsari

    34 Tambaya: Taƙarna ba ƙashi ba

    Amsa: Kanwa

    35 Tambaya: Baba na ɗaka gemu na waje

    Amsa: Hayaƙi

    36 Tambaya: Shirin ba ci ba

    Amsa: Baba

    37 Tambaya: Icce gidana innuwa gidan wani

    Amsa: Budurwa

    38 Tambaya: Kai na laɓe ba ka shigowa?

    Amsa: Gambu

    39 Tambaya: Tsumunjiyar kan hanya fyaɗi yaro fyaɗi babba

    Amsa: Yinwa

    40 Tambaya: Na yi ‘yar sanwata kowazzo sai ya iza

    Amsa: Tuntuɓe

    41 Tambaya: Salame doguwa da duwatsu

    Amsa: Goruba

    42 Tambaya: Shimil ƙasa ba saye

    Amsa: Kashi

    43 Tambaya: Jan guru gagara sarki ɗauka

    Amsa: Garwashi

    44 Tambaya: Abu ɗan ɗil ya sa mai gari kuka

    Amsa: Barkono/yaji

    45 Tambaya: ‘‘Yar tsohuwar gidanmu kullum tanke da gaba

    Amsa: Darni

    46 Tambaya: Akushin baba gagara suɗi

    Amsa: Kududdufi

    47 Tambaya: Ɗan baka a bayan suri

    Amsa: Farce

    48 Tambaya: ‘‘Yar ƙaramar dabba da suna uku

    Amsa: Kyanwa

    49 Tambaya: Ga gaɓa ga gaɓa zomo ya bi ya wuce

    Amsa: Tusa

    50 Tambaya: Ɗan oga da ƙaton tumbi

    Amsa: Kwando

    4.0 SAKAMAKON BINCIKE

     

    Wannan bincike ya gano cewa akwai hasashen cewa nan da ‘yan shekaru masu zuwa,idan ba a yi hattara ba wannan fanni na azancin magana wato kacici-kacici yana iya yin ɓatan dabo; wato a nemesa arasa. Ganin wannan ne binciken yai ƙoƙarin zaƙulo wata hanya da za a bi domin a farfaɗo da wannan fage na azancin magana kacici-kacici.Hanyar kuwa ita ce ta kundace shi don gudun ɓacewarsa kwatakwata.

    5.0 KAMMALAWA

    Sakamakon wannan bincike ya yi daidai da hasashen binciken tun farko, na cewa akwai alamu da ke nuna cewa kacici-kacici na iya salwanta nan da ‘yan shekaru masu zuwa; matsawar ba a yi wani hoɓɓasa ba akai. Duba da babu wasu rubuce-rubuce masu yawa da na ci karo da su a kan kacici-kacici. Don haka, akwai buƙatar masu ruwa da tsaki wato masana da manazarta harshen Hausa da su zage dantse wajen ganin an haɓɓaka tare da kundace wannan fage na adabin baka don ganin haƙa ta cimma ruwa.

     MANAZARTA

    Muhammad, Y.M.(2015). Adabin Hausa, Ahamadu Bello University Press Samaru

     Zaria

    Yahayya, I. Y. da Ɗangambo A.(1986).Jagoran Nazarin Hausa, Northern Nigerian

     Publishing Company Limited.

    Ɗangambo, A. (2011). Rabe-raben Adabin Hausa(Sabon tsari) K. d. g. Publishers.

    Owomoyela, O. (1996). Yoruba riddles in Oral Literature. Research in African Literatures, 27 (3), 41-52.

    Zarruk et al (1990). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Ibadan: University Press.

    Dr. A. M Bunza da Malumfashi I.A (2000). Pivotal Teachers Training Programme

     National Teachers’ Institute, Kaduna.

    Umar, M.B. (1980), Adabin baka don makarantu: Zariya; Hausa Publishers Centre, p.o. Box 675.

    Gusau, S.M (2011), Adabin Hausa a taƙaice: Centre Research Publishing Limited, Kano- Nigeria

    2 comments:

    1. Wani abune fari kamar ruwa baki kamar tukunya namiji yana amfani dashi so uku a rana mace so daya tak a rayuwarta

      ReplyDelete
      Replies
      1. An ce ƙabari ne.
        1. Fari idan mutum ya yi aikin ƙwarai.
        2. Baƙi idan mutum ya yi aikin banza.
        3. Namiji na iya zuwa binne mamaci koyaushe, da safe ko da rana ko da dare.
        4. Mace takan je kabari ne kawai lokacin da Allah ya yi mata cikawa aka kai gawarta.

        Delete

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.