Ticker

6/recent/ticker-posts

Ko Akwai Maganin Zina, Lesbian, Luwadi?

TAMBAYA (55)

Please ina da tambaya

Akwai Ayoyin da ake karantawa jarirai daga AL-QUR'AN daze tsaresu daga sharin fiyade,luwadi,da lesbian?

AMSA

A haqiqanin gaskiya babu wata sahihiyar addua da ta zo a sunnah akan wannan matsalan

Kwana kwanannan an samu case din wani mara imani da yayiwa wata yarinya wadda bata fi shekaru 5 ba fyade silar garzayawa da ita asibiti akayi mata aiki. Wannan wacce irin lalacewa ce ? Amsar saidai muce hakan yana da alaqa da alamomin tashin alqiyama domin kuwa muna ganin alamun akan idanunmu

Yin zina tsakanin saurayi da budurwa babban laifi ne a shari'ar musulunci, kuma alamu ne na cewar akwai karancin ilimi da kuma yalwataccen jahilci da son zuciya ga mazinatan, wanda kuma yayiwa karamar yarinya fyade wannan kam ba shi da tausayi kuma da za'a tambayeshi zai so ayi hakan ga yar sa zai ce a'a. Anan shaidan da biyewa sha'awarsa sun yi tasiri akansa har ya manta da gargadin Allah Azzawajallah;

( وَلَا تَقْرَبُوا الزِّنَا ۖ إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَسَاءَ سَبِيلًا )

الإسراء (32) Al-Israa

Kuma kada ku kusanci zina. Lalle ne ita ta kasance alfãsha ce kuma tã mũnãna ga zama hanya

A kokarin neman maganin faruwar hakanne wata mata ta je wajen wani malami wanda ya bata ayar dake cikin Suratu Maryam, wai ta dinga karantawa a al'aurar yar wai ta  hakan zai sa ta samu tsari daga sharrin fyade da sauransu

Dukkan wannan bai zo daga sunnah ba

Amman abinda ya tabbata shine; an rawaito cewar Annabi SAW yana yiwa jikokinsa wato Hassan da Hussaini bin Ali (Allah ya kara musu yarda baki daya) wadda ta tabbata a cikin sahihan hadisai, kamar yanda Shaikh Sa'id Alqataani (Rahimahullah) ya kawo a cikin littafinsa na Hisnul Muslim (Asaka mawallafin littafin a addu'a domin kuwa a watanni baya ya koma ga MahaliccinSa)

Inda yace: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance yana nema wa Hassan da Husain tsari da wannan addu'ar (Harma yace babanku {Annabi Ibrahim AS} yana yiwa yayansa {Annabi Ismail da Ishaq} ga addu'ar kamar haka

أُعِيذُكُمَا بِكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّة، مِنْ كُلِّ شَيْطَانٍ وَهَامَّةٍ، وَمِنْ كُلِّ عَيْنٍ لاَمَّةٍ.

"O'eezukuma bikalimatil-lahit-tammah, min kulli shaytanin wahammah, wamin kulli 'aynin lammah"

Bi ma'ana: "Ina neman muku tsari da kalmomin Allah cikakku daga dukkan shaidan da wata dabba mai dafi, da kuma dukkan wani mai kambun baka, mai cutarwa"

(Duba Sahihul Bukhari hadisi mai lambata 3371)

Sannan kuma tun ran gini tun ran zance, akan yi tuya a manta da albasa ma'ana mutane sukan manta da addu'ar da Annabi SAW ya koyar kafin tarawa da iyali, wadda rashin yinta kan iya kawo yiwuwar a haifi yaro kangararre ya zo ya dameku ya dami al'umma da shaidanci domin kuwa sakacin rashin neman tsarin Allah ne daman yasa shaidan kan shafi abinda Allah ya azurta ma'aurata tunma kafin a haifi yaron, addu'ar itace kamar haka

بِسْمِ اللهِ اللّهُمَّ جَنِّبْنَا الشَّيْطَانَ، وَجَنِّبِ الشَّيْطَانَ مَا رَزَقْتَنَا.

"Bismil-lah, allahumma jannibnash-shaytan, wajannibish-shaytana ma razaqtana"

Ma'anarta: "Da sunan Allah. Ya Allah! Ka nisantar da shaidan daga garemu, kuma ka nisantar da shaidan daga abin da Ka azurta mu da shi"

Addu'ar tana cikin Sahihul Bukhari tareda Fathul Bari 4/181, harma Shaykh Pantami yace ba abin mamaki bane idan kaga shaidanin yaro a wannan zamanin, kana bin salsala zakagano iyayensa basuyi waccan addu'ar bane

Don haka wadannan sune wasu daga cikin sahihan addu'u'o'in da suka inganta daga Ma'aiki SAW

Saidai kuma abu ne mai kyau kuma ya halatta iyaye su dinga yiwa yayansu addu'a ta musamman domin neman kariyar Allah Azzawajallah musamman ma a wannan zamani da muka tsinci kanmu a ciki. Akwai wata addu'a ta musamman da Shaikh Aminu Daurawa ya shawarci iyaye su dinga tashi kamar karfe 3 na dare suna roqawa yayansu, munsan cewar Allah SWT yana sakkowa sama'ud dunya a kowanne karshen dare, kuma addu'ar iyaye karbabbiyace, a cikin addu'ar ne yace;

"...Allahumma hassin furujahum, minazzina, walliwadi, wassihaqi, wa kullal jara'im..."

Ma'ana: Ya Allah ka tsare min gaban yaya na, ka kare su daga zina, da liwadi, da madigo da dukkan laifuffuka

Muna roqon Allah ya bamu ikon fahimtar addini dakuma aiwatar dashi, ya Allah ka tabbatardamu bisa tafarkin magabata na qwarai (Salafus salih)

Wallahu ta'ala aalam

Subhanakallahumma, wabi hamdika, ash-hadu anla'ilaha illa anta, astaghfiruka, wa'atubi ilayk

Amsawa;

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/G5NSbo2TyHMD6bcoEfds5E

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments