Abubuwan Da Ke Ciki
A wannan shafi, an kawo bayanai game da yaddda ake sarrafa Kunun Nono da Kunun Dankali da Kunun Aya da Kunun Kwakwa da Kunun 'Ya'yan Itace da Kunun Kuskus da Kwastad da Yogot da Ayis Kirim.
Kunun Nono
i. Gero
ii. Kayan ƙamshi
iii.
Madara
iv. Nono
v. Ruwa
vi. Suga
vii. Zuma
Za a samo nono adadin yawan kunun da za a yi, sai a raba shi
kashi biyu. Za a burkake kashi guda a sanya masa kayan ƙamshi a ciki. Kashi gudan
kuwa za a haɗe shi
tare da gumbar gero. Za a dama kashin da aka haɗe
da gumbar gero tare da ruwan zafi. Sannan sai a sanya sauran nonon da aka ajiye
a matsayin gasara. A wannan gaɓa
ne kuma za a iya ƙara madara ta ruwa ko ta gari tare da zuma.
Kunun Dankali
i. Dankalin Hausa
ii. Gero ko Dawa
iii. Kayan Ƙamshi
iv. Ruwa
Akan jiƙa gero ko dawa amma ba mai yawa ba. A gefe guda kuma sai a
fere dankalin Hausa a yayyanka cikin wannan gero ko dawa. Za a ƙara
kayan ƙamshi
ciki sannan a kai markaɗe.
Bayan an dawo da shi, za a tace a cire gasara sannan a dama kunu tamkar yadda
ake dama kunun koko. Daga baya ne kuma za a sanya wannan gasara da aka tanada.
Kunun Aya
i. Aya
ii. Dabino
iii. Kayan ƙamshi
iv. Kwakwa
v. Madara
vi. Ruwa
vii. Suga
Za a fece aya, sai a wanke, sannan kuma a jiƙa ta. An fi so a yi amfani da ayar Hausa. Yayin da za a kai markaɗe, za a sanya kwakwa da dabino (bayan an cire ƙwallon dabinon) tare kuma da kayan ƙamshi. Bayan an markaɗo za a tace sannan a zuba madarar ruwa ko ta gari.
Kunun Kwakwa
i. Kayan ƙamshi
ii. Kwakwa
iii. Ruwa
iv. Suga
v. Ɗanyar Shinkafa Ta Tuwo
Wannan nau’in kunu ne da ɗanyar
shinkafa ta fi yawa a ciki. Da farko, za a jiƙa ɗanyar
shinkafa ta jiƙu. Bayan ta jiƙu, za a sanya kwakwa adadi mai yawa tare
da kayan ƙamshi,
sannan sai a kai markaɗe.
Bayan an dawo da ita, za a tace, sannan sai a dama ta da ruwan sanyi. Ana iya
sha haka nan, ana kuma iya sanya suga.
Kunun ’Ya’yan Itace
i. Abarba
ii. Ayaba
iii. Kankana
iv. Kayan ƙamshi
v. Kwakwa
vi. Ruwa
vii. Shinkafa
viii. Tuffa
Wannnan nau’in kunu ne da ya ƙunshi ’ya’yan
itatuwa iri daban-daban. Da farko, za a jiƙa shinkafa, a gefe guda kuwa, za a tanadi
nau’o’in kayan marmari kamar
yadda aka bayyana a sama. Abu na gaba, sai a haɗe
su da wannan jiƙaƙƙiyar shinkafar, sannan sai a ƙara kayan ƙamshi a kai wurin markaɗe. Bayan an dawo da shi
daga markaɗe, za a
tace a fitar da gasara gefe (ba dole ba ne a yi gasara) daga nan sai a dama
kunu. Bayan ya damu, sai a kawo gasarar da aka tanada a sanya a ciki tare da ci
gaba da damawa. Ga mai son ya yi ɗanɗanon zaƙi
sosai (shazumami), sai ya ƙara suga kafin ya fara sha.
Kunun Kuskus (Couscous)
i. Kuskkus
ii. Madara
iii. Ruwa
iv. Suga
v. Tuffa
Za a tanadi madarar gari a kwaɓa
ta tare da suga a sanya a cikin tukunyar da aka ɗora
bisan wuta. Idan ta dafu, sai a ɗauko
kuskus a riƙa
barbaɗawa ana
juyawa/gaurayawa a hankali. Da zarar an zube kuskus ɗin tsaf, za a gauraya sosai domin ko’ina ya haɗe. Daga nan sai batun
saukewa.
Kunun Yara
i. Alkama
ii. Dawa ja
iii. Gyaɗa
iv.
Masara
v. Ruwa
vi. Waken suya
vii. Zuma
Za a jiƙa alkama da masara da waken suya su kwana. Washe gari sai a
soya gyaɗa a cire ɓawon a haɗa a markaɗo su gaba ɗaya. Bayan an dawo daga
markaɗen, sai a tace
sannan a cire gasara. Ana dama shi kamar kunun koko, sannan sai a sanya gasara
daga baya. Zai ƙara armashi idan aka sanya zuma cikin irin wannan nau’in kunu.
Kwastad (Custard)
i. Dawa
ii. Gyaɗa
iii. Masara
iv. Ƙwai
v. Ruwa
vi. Suga
vii.
Waken suya
Idan za a yi kunun kwastad, gyaɗa za a soya sai ta koma ja, sannan ɓawonta ya fita. Daga nan
sai a murje ta a fece a aje gefe guda. Bayan wannan, sai a soya gero da dawa da
kuma masara daban-daban sai a haɗe
su waje ɗaya da gyaɗar. Za a kawo waken suya a
zuba a kai wajen niƙa. Bayan an dawo daga niƙa, sai a tankaɗe shi. A gefe guda kuma, za a tanadi ruwa a
saman wuta. Da zarar ruwan ya tafasa, sai a riƙa ɗiban
wannan gari ana barbaɗawa
a hankali ana damawa. Kenan dai shi kwastad a kan wuta ake dama shi saɓanin sauran nau’o’in kunu
da ake zuba ruwan zafin kansu. Bayan an kammala damawa za a fasa ƙwai a
kwaɓa sannan a zuba
cikin kwastad ɗin da
ke saman wuta.
Bayan an zuba ƙwai, za a sake jujjuya shi domin ya haɗe gaba ɗaya. Daga nan sai a sauke
shi. Bayan an sauke, ana iya sanya madara ta ruwa (akan ma iya sanya ta gari)
da kuma suga. An fi ba wa yara irin wannan nau’in kwastad.
Yogot (Yoghurt)
i. Madarar gari
ii. Nono
iii. Ruwa
Za a ɗora
ruwa bisa wuta a tukunya mai kyau domin ya tafasa. Bayan ya tafasa, sai a sauke
a bar shi ya ɗan huce
kaɗan. Daga nan sai a
kawo madarar gari a riƙa barbaɗawa
a hankali ana damawa, har sai ya yi kauri. Za a lura da shi sosai domin kada ya
yi gudaji. Bayan wannan ya kamala, sai a kawo nono mai kyau mai kauri kuma
wanda ba shi da tsami. Za a riƙa zuba wannan nonon a hankali ana
gaurayawa. Bayan an kammala wannan, sai a rufe a ajiye a wuri mai ɗan ɗumi na kimanin awa huɗu. Bayan nan za a ɗauko a sanya filebo da suga. Ana buƙatar a
sanya shi cikin firijin a wannan gaɓa.
Yayin da aka zo cire shi, za a tarar da ya yi kauri sosai ya zama yogot.
Ayis Kirim (Ice-Cream)
i. Ayaba
ii. Filebo
iii. Madarar ruwa
iv. Ruwa
v. Suga
Za a sami ayaba mai kyau gwargwadon adadin ayis kirim ɗin da ake son haɗawa. Sai a yayyanka wannan
ayaba ƙanana-ƙanana,
a zuba a bilanda a markaɗe.
Ba a buƙatar
sanya ruwa yayin wannan markaɗe.
Daga nan sai a juye ayabar a cikin roba ko kwano mai kyau. Sai kuma a fasa
madarar ruwa a sanya a ciki. Za kuma a ƙara filebo amma ta ayaba (filebon ayaba).
A kula, filebon da za a sanya kaɗan
ne. Sannan za a sanya suga shi ma ba mai yawa ba. Idan ana buƙata,
za a ƙara
sanya ɗanyen inibi a
ciki. Da zarar an yi wannan, sai a juye cikin robobi sannan a sanya cikin
firijin. A lokacin da ya yi ƙanƙara, shi ke nan ya zama ayis kirim.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.