Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar III CFR da Mai Martaba Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Adamu

     

    Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar III CFR  da Mai Martaba Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Adamu
    "Kututturan da ba sanyi gasu sun yi toho,
    Sun É—au Salati sun É—au Azumi da Kono da Zakka" 

    Inji MakaÉ—a Abdun Inka Yarkofoji, Bakura a  faifansa na Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar III mai amshi 'Ya tsare gaskiya Bajinin gidan Hassan, Jikan Bello Sarkin Musulmi'. Irin wannan aiki ne Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar III CFR ke ci gaba da gudanarwa a halin yanzu. 

    A wannan hoton, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar III CFR ne a gefen dama, a lokacin da Mai Martaba Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Adamu ke yi masa marhabin da sauka Masarautar Bauchi domin baiwa wasu Bayin Allah su fiye da 60 Kalmar Shahada a yankin Ganjuwa mai hedikwata a Kafin Madaki ta Jihar Bauchi a kwanan nan. Allah ya jiƙan magabatanmu, ya ƙara wa Masu Martaba Sarakunanmu Lafiya da nisan kwana mai albarka, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin. Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara. 08149388452, Jumu'a, 29/12/2023. 4:42 Na Yamma.

    Daga Taskar:
    Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
    ÆŠanmadamin Birnin Magaji
    Imel: birninbagaji4040@gmail.com
    Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.