𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum
Warahmatallahi Wabarkatahu. Mallam HAMISU Muna godiya sosai da irin kokarin da
kake yi, Allah ya saka maka da mafificin alkairi da kuma addu'ar cikawa da
imani su tabbata agareka tare da iyalanka, iyaye, malumanka da kuma daliban
wannan group mai albarka.
Tambayata ita ce mene
ne hukunci wandanda suke Kirkirar labarin karya don su bama mutane dariya?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus
salam Warahmatallahi Wabarkatahu
Manzon Allah
Sallallahu alaihi Wasallam Yace : ( AZABA TA TABBATA GA WANDA ZAI BADA WANI
LABARI SAI YAYI KARYA DOMIN YADARIYANTAR DA JAMA'A DASHI, AZABA TA TABBATA
AGARESHI, SANNAN AZABA TA TABBATA AGARESHI).
Tirmizi
yaruwaitoshi acikin كتاب الزهد (kitabus zuhudi) babi na 10.
Masu rubutawa da
masu karantawa da masu yi da baki duk sun shiga cikin wannan hadisin.
Manzon Allah
Sallallahu alaihi Wasallam Yace: Da kunsan abinda nasani, da kunyi dariya kaɗan, kuma kuyi kuka mai yawa.
Yana yin yanda mu
keyin dariya ya sha ban-ban daga wani zuwa wani. Inda yawan dariyar wani ba ta da
makama kuma ta wuce kima, sai kaga wani nata sharara dariya harda hawaye sai
kace an yafe masa dukkanin laifukkansa na duniya.
Wani har
fina-finnan barkwanci yake kallo dan kawai nishadin da zaisa ya sharara dariya
har sai ya ji cikinsa ya yimar ciwo. Ba tare da lura da ainihin illar da yawan
dariyar nan take haifarwa ba.
Ba laifi bane dan
an yi dariya sai dai yawan yinta akai-akai baya da fa'ida musamman kyakkyatawa.
Manzon Allah
(Sallallahu alaihi Wasallam) bai taɓa yin dariya ba saidai yakan yi murmushi.
Abu huraira ya
rawaito hadisi inda yace Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) "yana
cewa karkayi dariya da yawa, tabbas yawan dariya na busarda zuciya"
Al-tirmidhi,2305;Ibn
Maajah,4193.
Idan muka dubi
wannan hadisin to zamu ga cewa duk abinda ke busarda zuciya to a hakika yakan
gusarda imani, domin zuciya ita ce tsoka mafi kyau da ake son ta gyaru wanda da
zaran ta gyaru to a hakika dukkanin sauran ganganr jiki ya gyaru.(Hadisi)
Amma ayi fara'a,
ayi annashuwa da raha, da murmushi da kalamai masu daɗi a tsakanin juna duka ba
illa bane.
Wasu sun ɗauki yin dariya ta hanyar
nishadi da kallon fina finnai na gusarda damuwa da yawan tinani wanda wannan ba
haka bane, ba abinda ke saurin gusarda hushi da ɓacin rai a duniya tamkar sadaka da karatun Qur'ani. ko miye damuwarka to
ka tsare hakan ka gani wallahi zaka samu waraka.
Don haka akwai
bukatar mu kula da yanda muke yin dariya ganin wannan zamanin samuwar hanyoyin
sadarwa na kara ta'azzara labaran barkwancin da ake ta yaɗawa daga shafukan sada
zumunta na ' facebook da whatsapp' inda zaka ga labaran kirkire masu matukar
barkwanci, gaya kuma Allah ya tsinewa duk mutumen dake zama ya kirkiro da
labari dan ayi dariya.
Abinda yazo
gameda Wanda zai furta wata kalma domin ya sa mutane dariya dubi: Hadisi na
2315.
A dubi: Abu
dawud:4990.
A dubi: Sahihul
jam'i:7136.
Daga: Bahazu bin
Hakim daga Babansa daga kakansa (رضي الله عنهما)
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi
Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.