Ga yadda abun ya faru. Wani lokaci ne a cikin 1970s, En'a ta Sakkwato (Sakkwato Native Authority, NA) ta buga Tanda(Tender) ta wasu ayyukan kwangiloli, yan kwangila da dama suka yanki wannan Tanda ciki kuwa har da wannan bawan Allah da muke magana akai.
Bayan an fitar da sunayen yan kwangilar da suka samu nasara
sai wannan bawan Allah ya tafi ya duba ko sunansa ya fito. Aka yi sa'a kuwa ya
ga suna "Salihu Gummi" a cikin tsarin sunayen yan kwangilar da Allah
SWT ya baiwa nasara.
Sai kuma aka yi rashin sa'a su biyu ne masu wannan suna na
Salihu Gummi suka zo daga Gummi domin duba sunayensu su kuma karɓi takardar kama aiki.
Tandan Tandan Tandan!!! Idan aka kira Salihu Gummi sai duka
su biyun su karɓa. A
cikin hikimarsa da ya saba sakawa cikin lamurran mulki sai Mai Alfarma Sarkin
Musulmi Abubakar III, Allah ya kyauta makwanci, amin ya ce wa wancan Salihu
Gummi (wanda ya fi wannan Salihu Gummin
da muke magana akai yawan shekaru a duniya) "Kai mi as sana'ak ka, ka kau
cika wagga Tanda? Ya amsa masa cewa " Allah shi baka nasara sana'ag goro
nikai, kuma tabbas na yanki Tanda ".
Ya juya akan wannan Salihu Gummi da muke magana akai ya ce
" Kai Samari wace sana'a ka kayi, ka kau yanki Tandag ga? Ya ce masa
" Saye da sayar da hatci ni kayi, kuma na yanki Tandaw wanga aiki, Allah
ya taimake ka".
Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar III ya dube su, ya ce
tau zan kashe wagga gardama. Kai Salihu da ad da shekaru da yawa an baka wanga
aiki, daga yau kuma sunan ka Salihu Mai Goro Gummi. Ya juya wajen Salihu Gummin
da muke magana akai ya ce "Kai kuma in Allah yaso zan samo maka naka aikin
kuma daga yau sunan ka Salihu Mai Buhu Gummi".
Haka kuwa aka yi, domin ya samo masa aikin ginin Makarantar
Furamare ta garin Illelar Awwal dake cikin gundumar Gummi. Daga lokacin ne kuma
ya ci gaba da ansa wannan alkunya/laƙabi na "Mai Buhu" a cikin
sunansa.
Wannan shi ne Alhaji Salihu Mai Buhu Sarkin Yaƙin
Gummi, Ajiyan Zamfara, Ɗan Kasuwa, Ɗan Kwangila kuma Ɗan Siyasa. Allah ya ƙara
lafiya da nisan kwana mai albarka, amin.
Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara,
Nijeriya.
08149388452, 08027484815.
birninbagaji4040@gmail.com
Talata, 30/01/2024.
12:54 Na Rana.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.