San Kano ya tarbi Nasara"
Inji Makaɗa Salihu Alasan Jankiɗi Rawayya a faifansa na Marigayi Mai Girma Sardaunan Sakkwato, Sir Ahmadu Bello, GCON, KBE, Firimiyan Jihar Arewa mai amshi 'Ga Darajja Amadu Bello da arziki na mazan jiya kay yi'. Marigayi Mai Martaba Sarkin Kano Aliyu/Alu ɗan Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi ɗan Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo ke nan zaune a inda Turawan Mulkin Mallaka na Birtaniya suka tsare sa a garin Lokoja bayan arangamar da suka yi dashi a Ƙoramar Zorori dake kusa da Kwatarkwashin Jihar Zamfara ta yau bayan sun afkawa Kano a daidai lokacin da ya ke kan wata ziyara a Cibiyar Daular Usmaniya, Sakkwato a cikin shekarar 1903.
Yunƙurinsa na komawa Kano daga Sakkwato domin fuskantar Rundunarsu bai samu nasara ba domin sun haɗu dashi da Jama'arsa a wannan Ƙoramar suka gwabza. Gwabzawar ce Makaɗa Salihu Alasan Jankiɗi Rawayya ya taskace a cikin wannan ɗan Waƙar. Allah ya kyauta makwanci, amin. Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara.
Daga Taskar:
Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.