Marigayiya Hajiya Rakiya Bagobira, Jakadiyar Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji (Dr.) Shehu Idris

    Marigayiya Hajiya Rakiya Bagobira
    Marigayiya Hajiya Rakiya Bagobira, Jakadiyar Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji (Dr.) Shehu Idris, Allah ya kyauta makwanci, amin. Ita ce wacce/wadda MakaÉ—a Sa'idu Ango Maidaji Sabon Birni ke ambata a cikin WaÆ™oÆ™in da yi yiwa Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji (Dr.) Shehu Idris. Kasancewar ta Bagobira /Daga Tsatson Gobir/Gobirawa a Fadar Masarautar Zazzau kuma a lokacin mulkin Sarakunan Fulani ana iya cewa Tarihi ne ya maimaita kan sa domin ko a lokacin mulkin Amirul Muminina Muhammadu Bello É—an Mujaddadi Shehu Usman ÆŠanfodio tagammadahullah birahamatihi ya yi Jakadiya Bagobira da ake kira Yar Gurma Fatima wadda/wacce ta zauna a Fadar Gobir a matsayin Jakadiya a lokacin mulkin Mai Martaba Sarkin Gobir Yunfa. Mai arziki ce matuÆ™a saboda ko a lokacin da take Jakadiyar Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ance ta mallaki Bayi 40. Allah ya jiÆ™an magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin. 

    Daga Taskar:
    Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
    ÆŠanmadamin Birnin Magaji
    Imel: birninbagaji4040@gmail.com
    Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.