𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Malam wasu Arna ne suka mana tambaya a makaranta cewa: Yaya
aka yi addinin Musulunci ya halattawa namiji Musulmi auren kirista mace, amma
ya hana a baiwa kirista namiji auren Musulma? Malam mun rasa amsar da za mu ba
su, shine muke so ka taimaka mana, don kar su samu hanyar da za su aibanta
addininmu.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
To, 'yar'uwa Sheikh Aɗiyya
Muh'd Salim ya yi ƙoƙari wajen warware wannan mushkilar a ƙarashen tafsirin
Adhwa'ulbayan da ya yi, inda ya ambaci dalilai guda biyu, wadanda suka hukunta
hakan
1. Kasancewar Musulunci shine yake yin sama, amma ba'a yin
sama da shi, idan kirista ya auri Musulma, zai zama yana sama da ita, tunda
namiji shine yake bawa mace umarni idan ya aure ta, saɓanin idan namiji Musulmi ne ya auri mace
kirista, tunda shi zai zama a samanta.
2. Musulmi ya yi imani da Annabi Isah (A.S.) da kuma Injila,
wannan zai sa idan ya auri kirista zai girmama ta, shi kuwa kirista bai yi
imani da Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi Wasallam) ba, don haka zai iya
wulakanta Musulma idan ya aure ta, tunda bai san darajar addininta ba, wadda
hakan zai sa su kasa fahimtar juna, zaman auren ya ta'azzara.
Duba Adhwa'ulbayan
8/164
Allah ne mafi sani.
Amsa daga Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.