TAMBAYA (71)❓
Aslm Usmannoor ya
kake, mene ne matsayin murmushi ko fa'idarshi, alkhairi ne, ko ihsani, ko
sadaka?? Sako daga Zhrdn Zeemo.
AMSA❗
Allah SWT yace;
( وَأَنَّهُ
هُوَ أَضْحَكَ وَأَبْكَىٰ )
النجم (43) An-Najm
Kuma lalle, Shĩ,
Shĩ ne Ya sanya dariya, kuma Ya sanya kuka
Kamar yanda muka
sani cewar da dariya ko murmushi da kuka ko yaqe dukkansu halittu ne da Allah
SWT ya sakawa dan Adam da manufar isar da saqo. Dariya idan ta wuce iyaka tana
zama matsala haka ma kukan
An karbo hadisi
daga Abu Hurairah (RA) yace, Annabi SAW yace: Yin murmushi ga dan uwanka
musulmi sadaka ne, umarni da kyakkyawa da hani da aikata mummuna sadaka ne, yin
mu'amalar auratayya shima sadaka ne"
(Hadisin yana
cikin Kutubus Sittah wato Bukhari, Muslim, Abu Dawud, Tirmidhi, Nasa'i da Ibn
Majah)
Dangane da dariya
kuma ya tabbata a cikin Hadisil Qudsi (Divine Narrative) cewar Allah SWT yana
dariya. Kamar yanda Annabi SAW ya fada a cikin hadisi cewar yasan dan Aljannah
na karshe (Wanda shi ne karshen fita daga Wuta) wanda bayan Allah SWT ya sa a
fito dashi daga wuta zai ji dadi shi a tunaninsa ma nan wajen shi ne Aljannah
Sai a suranta
masa wata bishiya mai kyau, yace ya Ubangiji ka bani ikon zuwa karkashin
bishiyarcan na ci na sha daga itaciyarta na ji inuwarta, sai Allah SWT yace
masa, ai iya alfarmar da ka roqa shi ne fitowa daga wuta
Sai yace ya
Ubangiji don rahamarKa ba don ni ba. Allah SWT zai bashi ikon zuwa wannan
bishiyar. Daganan zai qara hango wata bishiyar wadda ta ninninka ta farko a
komai na daga ni'ima, ya qara roqon Allah SWT, hirar farko ta kara maimaituwa
har dai zuwa bishiya ta uku wadda ta ninninka ta farko da ta biyu. Anan ne zai
fara jiyo sautin mutanen gidan Aljannah (Allah ya sa muna cikinsu), idan yaji
haka sai yace; ya Allah a dan kara matsar dani zuwa koda gate din Aljannah ne
Allah SWT yace;
bamuyi haka dakai ba ya bani Adam, yace don RahamarKa ba don ni ba. Bayan an
bashi ikon karasawa gate din ne zai ce, ya Ubangiji kada dai a gaji da ni, a
dan saka ni daga cikin Aljannar
Har zuwa inda
hadisin yace; zai ga wani wanda bai taba ganinsa ba, nan take zai zube yayi
sujjada shi a tunaninsa Allah SWT ya bayyana, sai ace masa tashi wannan ai
mala'ika ne mai gadin gidanka. Allah SWT zai ce masa roqi dukkan abinda kake
so, zai kure burinsa amman a karshe za'a ce masa an baka dukkan abinda ka roqa,
an kara maka da abinda ke cikin duniya sau 10, zai ce ya isheni haka ya Rab,
Allah SWT zai yi masa dariya
Sai yace ya
Ubangiji, kaine fa Ubangijin sammai bakwai da kassai bakwai kuma kake dariya,
ko dan na kasance nine na karshe (talakan) Aljannah ?
Sai Allah SWT
yace; "ba don haka nake maka dariya ba, nayi ne saboda ina da iko akan
aiwatar da dukkan abinda na ga dama"
(Duba cikin
littafin Albidaya wan Nihaya na Ibn Khathir)
A Tirmidhi an
tabbatar da cewar Annabi SAW yana dariya saidai dariyarsa ba irin ta sauran
mutane bace ba, kuma yawanci yafi yin murmushi kuma yana cewa ina yin barkwanci
amman duk abinda zan fada gaskiya ne
_*(Tirmidhi
hadisi mai lambata 1990, da Musnad Ahmad bin Hambal
hadisi mai
lambata 8481)*_
Haka kuma
Tirmidhi ya fitar a riwayar Abdullahi Ibn Abbas cewar haramunne yin dariya.
Imam an-Nawawi yace yawan yin dariya yana qeqashe zuciyar mutum ga barin
yawaita ambaton Allah SWT kuma yana rage darajar mutum, idan kuma an yi ne don
asaka wani dariya to zai zama mustahab (recommended)
(Muhammad
AbdulRahman, al-Mubarak furi, Tuhfatul ahwazi bi sarhi Jami'al Tirmidhi a cikin
"babu majaa fi al-muzahi)
Misali shi ne
hadisin wannan tsohuwar da tace: ya rasulullah shin tsohuwa kamar ni zata shiga
Aljannah ?
Sai Annabi SAW
yace: Ya Ummu fulan, ai tsofaffi basa shiga Aljannah
Tsohuwa sai ta
fara kuka saboda tasan gaskiya ya fada
Sai ya karanta
mata ayar Qur'ani inda Allah SWT yake magana akan matan Aljannah, yace;
( إِنَّا
أَنشَأْنَاهُنَّ إِنشَاءً )
الواقعة (35) Al-Waaqia
Lalle Mu, Mun ƙaga
halittarsu ƙagawa
( فَجَعَلْنَاهُنَّ
أَبْكَارًا )
الواقعة (36) Al-Waaqia
Sa'an nan Muka
sanya su budurwai
Aikam da jin
haka, nan da nan, yar tsohuwa ta ji dadi saboda taji ance za'a maida tsohuwa
zata koma budurwa a Aljannah
Da kuma hadisin
Ummu Ayman (RA) da tazo wajen Annabi SAW tace: Ya rasulullah, miji na yana
gayyatar ka gidanmu. Sai yace: wanene mijinki, ko shi ne wannan wanda da akwai
fari a cikin idonsa ?
Sai tace: ya
rasulullah wallahi miji na babu fari a idonsa
Sai Annabi SAW
yace mata: kowanne dan Adam ai yanada fari a cikin idonsa
Anan Annabi SAW
yana nufin wannan farin da yake a kusa da baki da yake a idanun kowanne mutum
Haka kuma akwai
hadisin Anas Bin Malik (RA) da yace: Annabi SAW yana yawan kira na da "Ya
dhal udunayn" ma'ana: "Yakai ma'abocin kunnuwa biyu"
Da dai sauran
masu yawa da suka tabbatar da barkwancin Annabi SAW
(Duba littafin
"Joke of Prophet Muhammad in the Hadith" wato "Barkwancin Annabi
SAW a cikin hadisi")
A kimiyyance kuma
malaman Human Anatomy sun gano cewar Dimple naqasu ne ga fuskar mutum a
kimiyyance amman a zahiri tsarin halittane mai saka kyau ga fuskar da take
dauke dashi. Ana kiran cutar da suna Genetic Disorder kokuma Anatomical Defect
wanda akewa taken Blessing in Disguise. Ana samun Dimple ne sanadin tsokar
Zygomaticus major idan ta ribanyu (Double kokuma Bifid akan fuskar mutum). A
duk lokacinda mai dimple tayi murmushi sai wannan tsokar ta Zygomaticus ta bude
ta hanyar tattare fatar kumatu ta fitarda wani qaramin rami a karshe hakan ya
wanzarda murmushi mai taushi
To mene ne yake
kawo murmushin kokuma dariya ? Mutane da yawa basa iya bada amsar wannan
sauqaqaqqiyar tambayar, wani zai iya cewa abinda ya sa ake murmushi ko dariya shi
ne farin ciki, alhalin ba haka baneba, kuka wani zaice baqin ciki ke kawoshi
kuma shima ba haka baneba, abinda ke kawosu shi ne isarda saqo zuwaga wanda
akai niyyar isarwa da taimakon Allah dakuma tallafawar ita waccan jijiyar mai
suna Zygomaticus (wadda sun rabu kashi 2, akwai zygomaticus major akwai kuma
zygomaticus minor)
Duk suna yiwuwane
da izinin Allah ta sunayensa guda 2 cikin 99, Alqabid wal Basid. Shi ne
Al-qabid (The Contractor) mai quntace abu sannan kuma shi ne Al-basid (The
Expander) mai bude abu. Quntacewar da kuma budewar da jijiyar take a samu
murmushin yana yiwuwane silar sunayenSa SWT. Dukkan godiya ta tabbata ga Allah
mai bada ikon saka kuka ko dariya, da ba dan Zygomaticus ba, da bazamu iya kuka
ko dariya ba
Kamar yanda ya
fada a cikin Suratul Najm ayata 43 "Wa'innahu huwa adhaka wa'abka"
ma'ana "Kuma lalle, Shi, Shi ne Ya sanya dariya, kuma Ya sanya kuka".
Wannan ayar bai kamata kawai mu dauketa a matsayin ayar dake nuni akan Dariyar
mutum kokuma Kukansaba saidai anan Allah SWT yanason bayinSa suyi Tadabburi ga
littafin Qur'ani ne domin gano wasu boyayyun hikimomi da yake son su gano ta
hanyar fadada bincike a kimiyyance da fasahance ta yanda hakan zai tabbatarwa
da masu binciken akwai Mahalicci (The Grand Designer), sannan kuma wannan ayar
hujja ce akan masu ilimin Human Anatomy wadanda basu yarda da WanzuwarSa ba.
Sannan kuma wannan ayar kadai ta isa ta tabbatar maka da cewar Shi Mai Iko Ne
akan komai
Ba iya kuka ko
dariya bane suke damfare da sirrin dake cikin Alqabid wal Basid ba, hatta
sassan jikin mutum (irinsu zuciya, hunhu, harshe, ido, hanci, hannu, kafa, baki
da sauransu) idan mun samu lokaci zamu fadada bayanin akansu, insha Allahu
Ina fatan wannan
amsar za ta sa mutane su kara Imani da kuma godewa Allah SWT akan ni'imomin da
yayi mana wadanda bazasu qirgu ba. Alhamdulillah bini'matihi ta'atimus salihat
Wallahu ta'ala
a'alam
Subhanakallahumma
wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta, astaghfiruka wa'atubi ilayk
Amsawa;
Usman Danliti
Mato (Usmannoor_As-salafy)
Zauren Fatawoyi
Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.